Page 7️⃣
___________________📖 Sak saurayin da ta faɗa kan sa yayi dan it's unexpected kafin ya ɗan zare ta daga jikin sa ya ja baya kaɗan, zare Ido yayi ganin ta kafin unbelievably ya nuna ta Yana faɗin sunan ta
"Queen, Kisnah".
Da ƴar dariyar dake fuskar ta ta furta sunan sa Shima
"Deeq".A sittin ya sake fisgota jikin sa ya ƙanƙame yana sakin dariyar farin ciki kamar yadda itama ta kasa rufe bakin ta, ƙara zare ta jikin sa yayi ya tsura mata Ido har se da ta hura Masa iska a bakin sa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya sake rungumar ta, wannan karon da kan ta tai breaking hug ɗin kana ta ja kujerar gefen sa ta zauna tana gyara zaman rigar ta da ta ɗan janye zuwa cikin ta.
Zama Shima yayi a kujerar sa ya sake kafe ta da Ido Yana kallo kamar irin Wanda ya Sami film ɗin da ya daɗe Yana jira, ɗan haɗe rai tayi tana dukan table ɗin gaban su
"Zaka Fara ko Deeq bayan kafi kowa sanin bana San wannan ƙure kallon ko".
"Uhm..hmmm...am..am sorry Kissy, kawai na kasa daina mamaki da jin daɗin ganin ki ne, we missed you so badlyyyy".
Ya ƙarashe faɗa Yana Jan ƙarshen kalmar badly ɗin, murmushin ta me cike da aji tayi kafin a ɗan shagwaɓe itama ta mayar Masa da amsa
"I missed you people so much also, it's a kinda feeling I gat at that time, I thought of nothing but home, my country, my land, my pride and my happiness, and as you can see am enjoying it here".
Gyaɗa kansa yayi cikin yarda da abinda tace "Sure I believe you're enjoying it, but what about we people, you don't have idea how we felt at the time, you leaving without even saying a goodbye is something we didn't expected".
"And am sorry for that, nasan in na faɗa muku ba zaku bar ni in tafi ba that's why I choose to just disappear without your consent".
"Allah ya shirya ki, so bani labari, how's life here in naija to you bayan nasan kin Saba da rayuwan Canada".
"The feeling of living in my home is as sweeter as honey, that's what I lack in Canada, but I missed all those partying, clubbing and dancing like hell though am trying to catch up here".
"I see, those girls?.
Ya faɗa pointing at su Meenah da suke cin abincin su hankali kwance dan sun Saba irin haka da Kisnah ɗin,
"Friends". Ta Bashi amsa a taƙaice, nodding yai Shima without saying anything dan daga yadda ta amsashi ya tuna Kisnah fa bata son yawan tambaya da bin ƙwaƙƙwafi akan personal life ɗin ta, miƙewa tayi tana duban designer and fashionable wristwatch ɗin dake tsintisyar hannun ta
"We see some other times Deeq, will be having some lectures now".
"No am not letting you off until you gave me ur digits, kaɗan daga aikin ki ki ɓace min a garin nan".
Ƴar dariya tayi a gayance da ya bayyana wushiryar ta dake ƙara Maya kyau kafin ta shiga karanta Masa number ta Yana shigarwa wayar sa, hannu ta ɗaga masa bayan ya gama sawa ta wuce wajen su Meenah da zuwa lokacin su ma sun gama ita suke jira, Surayya ce ta ɗauka mata nata abincin da akayi packaging cikin wrapping paper me kyau duk da a cikin wani ƙayataccen takeaway take dan bata Sami cin abincin ba tana ta magana da Deeq.
Makarantar suka koma dan suna da lectures biyu kafin su tashi, kamar yadda ya zame mata halayya da ɗabi'a wajen mai da hankali kan karatu yanzu ma haka tayi dan bata sake ko kallon su Hameedah ba se da suka fito daga theatre dan babu interval a jere ne lectures ɗin, wani na fita wani na shiga.
Ƙarfe shida biyar saura suka fito, kowa ka kalla fuskar sa gajiya zaka karanto kwance kanta wanda su Kisnah na ɗaya daga cikin su, na lokacin ba abinda take buƙata se wanka dan wani irin danƙo da ƙaiƙayi take jin jikin ta na mata, haka yasa hannu kawai ta ɗagawa su Hameedah da suka ƙarasa wajen motocin su kafin ta shige tata ta fige ta a ɗari ta fice a makarantar.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.