Page 3️⃣4️⃣
________________________📖 Hasken da ya ratso ta tsakankanin asabarin ɗakin ya haske masa fuska yasa ya fara motsa idanun sa a hankali har ya buɗe su gaba ɗaya, kallon ɗakin ya shiga yi kafin ya zabura cikin son miƙewa sedai tuni ya koma saboda zugin da ya ratsa hannun sa ya kai tsakiyar kansa.
Seda ya ɗan yi mintuna a kwance kafin ya yunƙura ya zauna a dabarance, hasken da ya shigo ta duk wata kafa ta jikin asabarin ya tabbatar masa da gari ya daɗe da waye wa har rana ta fito gashi ko sallah be yi ba, takaici ne ya kama shi dan baze iya tuna yaushe ya makara sallar asuba ba, haushin sa ya fi ta'alkaƙa ne kan rashin baccin sa da wuri ne ya ja masa makarar wadda duk sanadin tunanin mafitar wannan ƙaddararren auren da aka ɗaura masa jiya ne.
Duban gefen da yasan take kwance yayi ya ga bata nan, kenan ta tashi ita tayi sallah amma shine ko ta tashe shi, ƙwafa yayi yana me jin zafin hakan a ransa.
Daga zaunen da yake yayi gyaran murya cikin babban sauti dan haka yake yi se arɗo ya shigo ya taimaka masa zuwa matsuguni kafin ya dawo dashi yayi alwala.
Nenne da ke zaune tare da Kisnah tana taya ta mulmula furar da take curawa wadda sana'ar tace ta juyo gyaran muryar Saraki hakan yasa ta dubi Kisnah da ta maida hankalin ta kan furar gaba ɗaya
"Tashi yalo mijin ka na kila".
Tsayawa da abinda take Kisnah tayi ta shiga kallon ta dan bata fahimci me take cewa ba, sake maimaita wa Nenne tayi amma ita bata gane komai ba se miji kawai, seda ta nuna bukkar su tana sake maimaita mata daidai lokacin kuma da Saraki ya sake yin wata gyaran muryar kafin ta gane me take nufi.
Miƙewa tayi da sauri ta ƙarasa bukkar tare da shigewa dan tun ɗazu take cikin jimiamin rashin farkawar tasa kasancewar tun da suka zo ƙauyen ya farfaɗo bata taɓa ganin yayi nauyin bacci irin wannan ba.
Bata lura da kallon da yake mata ba ta ƙarasa gaban gadon karar da yake kwance ta kai zaune
"Yaa lafiya kuwa yau irin wannan bacci haka, Allah har kasa hankali na ya tashi".
Ko kallon ta be yi ba ya sake yin gyaran murya shi a dole yana neman arɗo
"Yaa arɗo fa baya nan, yau tun sassafe ya fita gona, ya shigo baka tashi ba so se ya tafi".
Se a lokacin ya kalle ta, arɗo baya nan to wa ze taimaka masa yau gashi yana son zagayawa dan fitsari yake ji saboda magungunan da baffa arɗo ya bashi ya sha a can da kuma wanda ya taho dasu yasha kafin ya kwanta.
"Bari in kawo maka ruwa kayi alwala se kayi sallah".
Ta faɗa tana miƙewa zata fita, da sauri ya tsayar da ita dan ji yake kamar marar sa zata yi bombing
"Zan yi fitsari tukunna". Tsayawa tayi tare da juyowa ta kalle shi, ze yi fitsari tabɗin, to ita yaya zata yi mishi ga baffa baya nan.
"Bari in faɗa wa Nenne in ji ko za'a sami wani da zai taimaka maka to".
Wani banzan kallo ya watsa mata jin wani wai se ya tsaya an samo wanda ze taimaka masa, kawai tace so take ya saki fitsarin a nan mana
"Malama in zaki zo ki taimaka min na je bayi ki zo in Kuma ba so kike na sake shi a jiki na ba, salon gulma kawai".
Dariya ce ta ciyo ta ba kaɗan ba ganin yadda yake magana yana ɓaɓɓata fuska at the same time yana mutsu mustu da alamu dai da gaske fitsarin ya matse shin.
Gaban gadon ta matsa tare da miƙa masa hannun ta, se ya gama hararar hannun kafin ya kama da nashi ya fara ƙoƙarin miƙewa ita kuma ta saka ɗayan hannun ta tallafe nasa me ciwon, da ƙyar ya samu ya iya miƙewa dan ba wani ƙwari gare ta ba har kusan faɗo masa tayi.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.