Page 3️⃣5️⃣
_________________________📖 kallon kwanon yayi ya kuma kallon ta yana tunani me ye something atrocious ɗin da tace,
"In gani".
Matsar da kwanon tayi gaban sa yasa hannu ya buɗe, zubawa zogalen da yasha haɗi yaji ƙuli ƙuli yayi kyau ido yayi, so this is something atrocious a wajen ta kenan, ɗago wa yayi ya dube ta se kallon sa take tana ɓata fuska, miƙa mata kwanon yai ta karɓa tana neman rufewa ya tare ta
"Bani naci". Zaro ido tayi waje jin abinda yace, shin be ga meke cikin kwanon bane da zece ta bashi, ko kuwa dan yana jin yunwa ze ci, in kuwa hakane yanzu zata je ta maida wa Nenne su dai kawai a basu furar su sha.
"Yunwa kake ji ko yaa, bari na maida mata abin nan nace a bamu fura kaji, dama nasan kaima bazaka iya cin wannan trash ɗin ba".
Dakatar da ita yayi daga fitar da zata yi
"Wannan ɗin nake son ci, in ke a wajen ki trash ne to ni a wajena yafi ye min all that luxurious dishes, ko kin manta da background ɗina ne, being with you doesn't make me as you, you're rich and am not, you're from a high class family and am from from a middle class family, so you go and get the fura, as for me this is what I want but don't forget we have no any relation with these people, they're only helping and yet they are trying their best with all they have, if you won't appreciate it I think you shouldn't curse it".
Cak ta tsaya a inda take tana sauraren sa, sosai jikin ta yayi sanyi da kalaman sa, 2 mins back ba taga aibu a cikin maida zogalen ba amma yanzu kam da ya faɗa mata wannan words ɗin se taji sam bata kyauta ba, ta sani wannan shine cimar su and shine abinda suka basu, in ta koma tace a canja is like ta Raina musu, bata gode ba kuma ta raina wa ƙoƙarin su.
A hankali ta dawo ta zauna in da ta tashi ta saka hannun ta ta ɗebo zuwa bakin sa, buɗe wa yayi ta saka masa ya shiga taunawa knowing ba zata ci ba sedai ga mamakin sa she feed herself also kuma duk yadda taso ganin wani baƙon reaction akan abinda bata saba ci ba be gani ba dan bata nuna masa komai ba ta shiga taunawa har ta haɗiye though deeo down tana dannewa ne amma ji take kamar tayi amai.
Haka suka cinye zogalen tass kafin ta ɗebo masa ruwa yasha ya kuma yi alwala, kallon ta yayi lokacin da ta koma ta zauna, fasa tada sallar yayi ya dube ta
"Ke ba zaki yi sallar bane?".
"Zanyi da magrib".
Ba abin mamaki bane a wajen sa jin hakan daga gare ta sedai abin haushi ne dan be manta not more than 10 days back da suke tare a Company yana ƙoƙarin saka ta yin Sallah a kan lokaci duk in lokaci yayi amma shine har zata ce masa wai zata yi da magrib, a yanda ya ke ji kaman ya rufe ta da duka wallahi se dai Allah ya taimake ta hannun sa be da lafiya
"You get up go and pray ko se ranki ya ɓaci, mara hankali kawai".
Tun tsawan da ya daka mata tayi wuff ta fice daga ɗakin sedai jin last word ɗin da ya faɗa ya mata ciwo, itace mara hankali, mara hankali fa ya kirata, is he in his right sense kuwa ko ko dan bata nuna masa kalar ta bane, ko kuwa gaskiyar Hameedah ne ta sake masa da yawa, aikuwa in haka ne ze san da ita yake wallahi.
Cikin ɓacin rai tayi alwalar ta koma bukkar su ta yafa wani baƙin saƙi da Nenne ta bata wai mayafi tayi sallar, tana idarwa ta matsa can gefe ta zauna ya shiga tunani, tunanin data rayu cikin guje ma yin sa a koda yaushe, tunanin iyayen ta dama rayuwar ta gaba ɗaya!
*SAKEENA SAFWAN*
Sunan mahaifin ta Alh Safwan Yaƙoub, asalin su mutanen ƙasar Congo ne dake maƙwabtaka da tasu, cirani ya kawo shi ƙasar Hawarya inda ya bar ƙanin sa ɗaya tal da yake dashi a can gida Congo, mahaifin su Safwan wato Yaƙoub manomi ne me ƙaramin ƙarfi wanda yake da mata biyu, A'i da suke kira Inna se kuma Inna lami da ainahin sunan ta Sakeena ne.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.