Page 4️⃣8️⃣
_________________________📖 Jan ta ya sake yi jikin sa ya ƙanƙame yana lallashin ta har tayi shiru kafin ya ɗan ja bawa ya sa hannu ya ɗago haɓar ta
"Is okay my Keenah, is okay kukan ya isa haka kinji?".
Gyaɗa masa kai tayi tana turo baki
"Zan samu mijin ta anjima, dole yayi wa matar sa warning if not zan ɗau mataki, insha Allah hakan ba zata kuma faruwa ba okay?".
Sake gyaɗa Masa kai tayi ta kwantar da kansa a ƙirjin sa tana sauke ajiyar zuciya, shima numfashi ya saki dan jin kan ta a ƙirjin sa yana neman sa shi cikin wani hali, sun jima a haka har se da ta janye dan kanta
"Muje kayi wanka yaa, nasan ka gaji ko?".
Hararar wasa yayi mata
"Se yanzu kika tuna da ya kamata nayi wanka bayan kin gama taɓarar ki, abin haushi ma ba ki rama marin ba se kika zauna kuka, raguwa kawai".
"Ni ba raguwa bace wallahi su kan su sun san haka dan su biyun ma basu iya da ni ba, dan dai na faɗi kan ƙafata tana min zafi lokacin ne, kuma kukan da nayi ai dan ban rama bane ba wai zafin marin ba". Ta gyara kalaman ta da sauri jin zata tonawa kanta asiri.
"Yayi miss ƙarfi, bari in dubo in toilet ɗin is clean".
Kamar tace masa bari taje da kanta se kuma ta ƙyaleshi yaje tunda tace ƙafarta na mata zafi kar ya gano ƙarya take, dawowa yayi ya juye ruwan zafin dake cikin flask ya fita ya sirka tare da kaiwa toilet, kwandon wanka ya koma ya ɗauka tare da komawa ya shiga wanka.
Yana fitowa aka kira sallar isha ya fita inda a can suka haɗu da Isa mijin maman junior, seda suka fito daga masallaci suka yo hanyar gida kafin yake sanar dashi abinda Kisnah ta faɗa masa tare da faɗin
"Na sanar da kai ne dan ka ja wa matar ka kunne ka gargaɗe ta dan bana haɗa iyalina da komai, Iyali na bame fitina bace nasan ta nasan abinda zata iya yi, wannan ma na haƙura ne dan ba'a taɓa ba se yanzu, kayi haƙuri amma wallahi in makamancin haka ya sake faruwa i won't take it lightly with her dan se na kai ta hukuma an mata hukunci daidai abin da ta aikata".
"Kayi haƙuri Ahmad insha Allah hakan baze kuma faruwa ba dan zan wa tufkar hanci, na maka alƙawari na kuma gode da mutunta ni da kayi".
"Nima Nagode da ka saurare ni ka kuma fahimce ni".
Da haka suka ƙarasa cikin gidan kowa kuma yayi hanyar ɗakin sa.
Zaune ya same ta tana downloading yadda ake tuwon shinkafa dan shi take son yi, gefen ta ya zauna tare da kwantar da kansa a kafaɗar ta yana kallon me take yi, vedion na gama sauka ta buɗe suka shiga kalla, yana ƙarewa zata sake replaying ya karɓe wayar,
"Me yasa baki tambaye ni na faɗa miki yadda ake yi ba, na fa iya sosai".
Ƙyalkyale wa tayi da dariya jin abinda yace, wai ya iya girki
"Allah da gaske nake na iya sosai".
"To shikenan goben se in yi mana miya in kadawo se kayi tuwon ko?".
Ta faɗa teasingly, hararar ta yayi dan ya fahimci tsokanar sa take
"Let's bet, Allah se na baki mamaki".
Ƙullawa suka yi tana ta dariyar imagining yadda ze yi tuwo shikuma a ransa yana faɗa wa kansa se ya bata kunya.
A can ɗakin maman junior kuwa ba ƙaramin tayar mata da hankali Isa yayi ba dan har iƙirarin ze iya sakin ta yayi akan zubar masa da mutunci da take son yi, ba ƙaramin mamaki ne ya kama su ba ita da sa'adah lokacin da ya faɗi abinda suka yi wa Kisnah, sun san ba haka bane sharri ta musu amma ba bakin kare kai dan baza su so maganar tayi zurfin da za'a gano ainahin dalilin faɗan ba dan ƙaramin aikin isa yace su tafi gidan su se ya neme ta, tass ya sille su kafin ya bawa sa'adah umarnin komawa hostel washegari dan dama ba ƙaramin takura yake yi da zuwan nata ba tunda ɗakin dai falle ɗaya ne.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.