PAGE 4️⃣5️⃣

402 21 3
                                    

Page 4️⃣5️⃣









__________________________📖 Washegari ma haka ya tashe ta tun 6, wanka suka yi suka karya da breakfast ɗin da ta haɗa musu, nine thirty suka fito daga ɗakin ta rufe suka nufi fita daga gidan, tsakar gida ta tsaya gaisawa da maman habu shi kuma ya fice daidai nan wata yarinyar mace da bazata wuce sa'ar ta ba ko ta girme mata da kaɗan ta fito daga ɗakin kusa da ita, kallon kallo suka yi kafin Kisnah ta ɗauke kanta tayi wa maman habu sallama zata fice ta dakatar da ita

"Amarya ga maman junior da na faɗa miki muna zaune tare da ita, maman junior ga amarya da suka tare shekaranjiya".

"Sannu fa". Kisnah ta cewa matar da aka kira da maman junior da ke bin ta da wani irin kallo ta kasa mata magana, maida hankali tayi wajen maman habu ta mata sallama ta fice da sauri sanin yana waje yana jiran ta, ƙofar gida ta same shi tsaye suka jera zuwa hanya har suka kai shagon sa kafin ya tsaya hakan yasa ita ma ta tsaya, shagon gefen sa ya nuna mata

"Ga shagon nan, ko zamu je ki gani?".

Girgiza kanta tayi

"No Yaa, saura kaɗan na makara ka bari in na dawo zan koma se in taho maka da abincin ka daga nan sai in gani ko".

Gyaɗa mata kai yayi alamar amsawa kafin tayi masa sallama ta wuce yana mata addu'ar dawo wa lafiya, yana tsaye har ta yi kwana kafin ya ƙarasa ya buɗe shagon.

Yau ma haka aka yi musu karatun da take fahimta sosai, ƙarfe ɗaya da mintuna ta dawo gida, kamar jiya yau muna wanka ta fara yi tare da gabatar da sallah sannan ta shiga ƙoƙarin ɗora girki a gefen ɗakin ta inda ta ajiye gas ɗin ta ba tare da kula kowacce cikin matan gidan ba, ita kam tun kallon farko taji maman junior bata yi mata ba ko kaɗan, matar ta fiya zubin munafukai haka kuma a yau kaɗai bata ga wani hali nata da ze nuna tana da mutunci ba dan ko da ta dawo tayi sallama tare da sannun kun da tace musu bata amsa ba se maman habu ce ta karɓa mata tare da mata ya makaranta.

Ita kanta maman habun yanzu tana da shakku a kanta, yadda ta shigo ta same su suna shewa da dariya ta gane suna good times sosai da maman junior ɗin, ance abokin ɓarawo ɓarawo ne dan haka yau ta fara ja baya da ita dan se hali yazo ɗaya ake abota so akwai halayen su da yake the same kenan shiyasa yau ko ɗan sakin fuskar da take bata yi ba ta haɗe sama da ƙasa tas ta koma Kisnahn ta ta ainahi.

Tana gama girkin ta zubawa Sultan da yayi mata cefane duk da yau take son yiwa Yaa maganar samo mata almajirin da ze dinga mata cefanen dan ta ji uwar Sultan ɗin na maganar zasu koma school next week Kuma ko ba haka so take ta zame daga duk wani abu da ze haɗa ta da maman habu se ko sallama da ta zama dole tsakanin su ɗan gaisuwa ma ba dole bace.

Habu ta kira ya ɗauki bowl ɗin da ta zubawa su maman habu abincin ya miƙa musu ita kuma ta hau jera warmer dasu plate ɗin da zata kaiwa Saraki abinci cikin madaidaicin basket, daga inda suke zaune maman habu ta ɗaga murya tana mata magana yadda zata ji ta

"Gaskiya amarya ba ƙarya kin iya girki, ji dai a mintuna kaɗan har kin gama abincin ki kuma yayi daɗi sosai wallahi, nace zan zo ki koya min ban ma ji kince komai ba".

Bata sake fuskar ta ba daga yadda take sedai ta ɗan yi faking smile

"Tun ranar da habu ya faɗa min ai nace masa ba matsala, sedai kin ga ina zuwa school sedai in da yamma dan girkin rana a gurguje nake yin sa so ba zan sami lokacin yi miki bayani ba".

"Ba matsala amarya, zan miki magana in na tanadi kuɗi sosai dan naga yadda kike kashe kuɗi kan cefane, ai gaskiya mijin ki na ƙoƙari".

Bata amsa ba dan bata san wata magana kan mijin ta a bakin su se kawai ta shige ɗaki ta canjo hijab dan ya siyo mata madaidaita iya gwiwa da take sawa in zata yi aiki a tsakar gida musamman da safe da dare saboda mazajen su, dari blue ɗin hijab ɗin da ta saka tun safe ta maida tare da fitowa ta zura takalmin ta, fuskar slipper gare shi amma wedge ne, tun farkon siyayyar kayan su ya haɗa mata da takalma huɗu kuma duk babu flat dan be taɓa ganin ta da shi ba iya zaman shi tare da ita a manya, baze siyo mata me shegen tsinin nan da take sakawa ba shiyasa ya siyo mata wedges.

SARAKI (The Accused Prince) ✅Where stories live. Discover now