Page 4️⃣4️⃣
_________________________📖 Litattafai ya ɗebo guda biyar ya bata wanda dasu zata dinga karatu, Alqur'ani izifi sittin, usulul salasa, Hadith, Muɗali'a, se drusu luggatul Arabiyya, wata Malama mace ya kira ta tafi da Kisnah aka nuna mata ajin da zata zauna.
Fitowa tayi daga ajin ta tsaya a compound na school ɗin tana jiran ya fito, sefa ya ɗan ɗau lokaci dan se a suka ƙara tattaunawa sosai da shugaban makarantar sannan ya fito, da sauri ta ƙarasa tana kiran sunan sa hakan yasa ya ankare da ita, kwaɓe fuska tayi cikin son yin kuka dan har idanun ta sun kawo ruwa, she's feeling awkward, kamar yau zata fara shiga aji, kamar za'a mata dariya, kamar kowa kallon ta yake, kamar...kamar.....!.
Ruƙo hannun ta na dama yayi ya shiga murzawa yana yi mata magana a hankali cikin son lallashin ta
"Is okay kinji, komai ze zama daidai, infact gaba ɗaya ƴan ajin ba wadda ta sanki balle tayi mocking ɗin ki kuma su ma duk manya ne, just relax and concentrate okay?".
Gyaɗa Masa kai tayi a hankali tana ƙoƙarin maida ƙwallar ta, hannu ya saka cikin aljihun sa ya fiddo ɗari biyar ya miƙa mata
"Take this and make sure you cook something as delicious as yesterday's, uhm?".
Nan ma Kai ta gyaɗa Masa tana murmushi ganin yadda yayi emphasizing kalmar delicious ɗin, ɗan kallon gefen su yayi yaga ba me tahowa so ya sake matsowa kusan ta tare da yin ƙasa da murya sosai
"Pray for me zamu fita karɓar shagon yanzu".
"Allah ya bada Sa'a yasa a fara da Nasara".
"Ameen, what about a goodbye and Goodluck kiss?".
Zaro ido tayi ta saka hannu ta rufe baki kafin ta Harare shi ta matsa baya tare da juyawa da sauri ta nufi ajin su, yana tsaye har ta shige kafin ya juya ya tafi yana sakin murmushin zaro eyes ɗin da tayi, dama saboda ta saki ranta yayi dan shima baya fatan faruwar wani abu makamancin wannan a tsakanin su.
Seat ɗin can tsakiya ta zauna tana bin littattafan da ta ajiye kan desk ɗin ta da kallo, gaba ɗaya she's not comfortable dan tana jin idanuwa a kanta ba kuma idon mutum ɗaya ko biyu ba, a'a da yawa.
Mutum kusan Ashirin ne a ajin kuma duk mata ne manya, uku ne kawai za su yi sa'anni da Kisnah ragowar kuwa sun girme mata sosai, tun da ta shigo abin suka bita da kallo, ba wai dan suna ganin bata iya komai ko dan wani abu ba se dan kyanta da hasken fatar ta da ya kuma bayyana sanadin maroon ɗin hijab ɗin jikin ta.
A hankali suke ɗan ƙusƙus tsakanin su a kanta, gani suke anya ma wannan tana jin Hausa, anya ba baturiya ce ba ta musulunta shine dalilin shigar ta makarantar, haka dai suke ta gulmar ta tsakanin su d ayawa na faɗin sam ba bahaushiya bace, cikin haka wata matashiya ta shigo sanye da nata hijab ɗin sedai Ash color ne, sallama tayi musu gaba ɗaya sannan ta ƙarasa seat ɗin da Kisnah take ta zauna, sam bata so hakan ba dan so tayi har a tashi kar wanda yazo kusa da ita balle magana ta haɗa su, sallama yarinyar ta sake yi mata daban bayan ta zauna ta amsa ta can ƙasa da bata ma tunanin ta ji ta.
Suna zaune malamin farko ya shigo, lokacin ne kowa ya maida hankali kan sa ya shiga biya musu Alkur'ani inda suka fara da Ummul Qur'an wato suratul fatiha wadda dole se da ita sallah zata tabbata, sosai suka maida hankali suka shiga maimaitawa yana faɗa suna biyawa, kusan awa ɗaya ya share a ajin kafin yayi musu sallama ya fita dan lokacin sa ya ƙare haka kuma alhamdulillah kusan da yawan su sun iya, yana fita wata Malama ta shigo inda ta shiga koya musu alwala bit by bit, nan suka kuma kuma ɓata awa ɗaya me kyau dan ɗaya bayan ɗaya ta dinga sa suna yi a gaban ta tana gani bayan ta maimaita musu kusan so biyar, lokacin da tayi pointing Kisnah kuwa diriricewa tayi gaban ta ya shiga faɗuwa, kallon malamar ta shiga yi kamar zata saki kuka idon ta na cika da hawaye, sake maimaita kiran ta malamar tayi amma taƙi fita se hawayen da ta fara yi hakan yasa malamar ƙyale fa bayan ƴan ajin sun ɗan yi dariya tare da sanar da ita ai bata jin Hausa so ba lallai ta ma ji bayanan da tayi musu ba dan da harshen Hausa ake musu dan su fahimta sosai.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.