PAGE 5️⃣1️⃣

434 13 0
                                    

                          Page 5️⃣1️⃣









__________________________📖 Suna sauka a tasha ya tare musu napep dan tuni ya daɗe da sawa an kama masa gida ƙarami me ɗan kyau dan baya so a san da shigowar su se ransa za'a shigar da ƙara.

Bedroom biyu da kitchen ke cikin parlon, kowane bedroom da na shi toilet hakan yasa tun da kowan su ya shige ɗaya be sake jin ɗuriyar ɗan uwan sa ba.

Bacci Saraki yayi bayan ya kira yaron Barrister sudais me suna Salihu ya sanar dashi ya zama ready anjima zasu fito suke tare da shi a shigar da ƙara, ita kam Kisnah ko baccin bata samu ba dan tunani yayi mata yawa a ranta, ko da tayi wankan ta kwanta kasa baccin ta yi se faman juye juye har zuwa lokaci da ya ƙwanƙwasa mata ƙafa, ya daɗe tsaye jikin ƙofar yana abu ɗaya amma sam bata ji ba saboda yadda tayi nisa cikin tunani, gajiya da knocking ɗin yayi ya murɗa handle ɗin ya shiga dan yana so ta shirya su shiga court yanzu.

Yadda ta ƙurawa waje ɗaya ido bata ko ƙiftawa ya tabbatar masa da tayi nisa, matuƙar nisa ma kuwa a duniyar tunani, tun daga ƙafafun ta har zuwa kan ta ya shiga ƙare mata kallo, ta rame masa a ido duk da ba kowa ze ga ramar ba Amma shi da yake tare da ita ya santa sosai yasan ta rame, wuyan ta ya kalla sedai ya ji rashin ganin alamun rama ta nan wato ƙashin wuya, maida kallan sa kan fuskar ta yayi wadda itace abu na farko da ya nuna ramar ta, idanun ta sun faɗa haka naman fuskar ta se hakan ya bawa hancin ta damar fitowa sosai kamar wadda zata yi rubutu dashi, ɗan ƙaramin bakin ta a tsuke yayinda lips ɗin ta suka sake yi masa pinkish a Ido.

Ajiyar zuciya ya sauke cikin tausayin ta dan yasan kwata kwata be kyauta mata ba haka shima baya jin daɗin sabuwar halayyar da suka tsiro a tsakanin su, he misses her so damn much, her warm hug, ya sight that makes him feels the man in him, her warm touch, her care, her affection, her laughter, her...her...her everything! sedai ya bar komai har zuwa a gama Shari'a, insha Allah ze yi ƙoƙarin ganin ya daidaita tsakanin su kafin su rabu.

Cin sanyin jiki ya shiga bubbuga gefen gadon da take kwance dan gidan irin me komai da akwai ne, masu gidan na saka komai na amfani kawai dai zaka biya kudi sosai, a firgice ta hantsilo daga kan gadon har tana buge kanta ga kuma neman faɗuwa da take yi, da hanzari ya ƙara sa ya tare ta ta faɗa kansa maimakon ƙasa, ajiyar zuciya ya sauke na jin ta a jikin sa after ranaku masu yawa, God! Yayi missing wannan ƙamshin na ta me ratsa jini da ƙwaƙwalwar sa fiye da zato, maimakon ya sake ga se ya sake ruƙunƙume ta a jikin nasa feeling her sosai cikin sauke ajiyar zuciya a kai a kai.

Lafewa Kisnah tayi a ƙirjin sa cikin maɗaukakin shauƙi, Allah ne kaɗai yasan adadin son da take wa Saraki, bata san yaushe ta fara ba, bata san taya ta fara ba haka kuma bata san ne ya jata ba, ta wayi gari ne ta tsinci kanta dumu dumu cikin kogin son sa, son da take jin bata taɓa yiwa wani mahaluƙi irin shi ba, son da take jin a wannan stage ɗin da yayi shunning ɗin ta ze iya zama silar mutuwar ta.

A kwanakin da suka wuce tana rayuwa ne kawai ba dan jin daɗi ba se dan Allah ya barta da rai da lafiyar ta so she have to show some appreciation, so da yawa in tana girki bata sanin ta ƙone se wajen ya tashi ko yayi shaida, so take ta tabbatar wa kanta zata iya rayuwa ko bashi shi yasa ta janye jikin ta ta kama kanta waje ɗaya sedai tabbas tana rayuwa amma rayuwar da babu ɗigon farin ciki a cikin ta, a iya mintuna biyun da tayi yanzu akan ƙirjin ta se taji bata da sauran damuwa, bata da sauran matsala in har zata dawwama kan wannan elegant and broad chest ɗin nasa.

Da sauri ta fisge jikin ta a nasa lokacin da kalaman sa suka dinga biya kan su a kanta, wani irin sarawa kanta yayi da yasa ta maza ta dafe shi bayan ta zauna sosai kan gadon da ta koma tana runtse idon ta, sighing Saraki yayi jin ta ƙwace jikin ta ya buɗe idon sa da ya rufe ɗazu saboda wani shauƙi da farin cikin dake ratsa shi jin ta a jikin sa, ɗan gyaran murya yayi cikin son basarwa

SARAKI (The Accused Prince) ✅Where stories live. Discover now