Page 5️⃣0️⃣
__________________________📖 Da ƙyar Yarima Jamal da yayi mutuwar tsaye ya iya ɗaga ƙafar sa yayi baya tare da juyawa ya bar cikin falon, wata irin kuwa da hajijiya yake ji dake neman kai shi ƙasa, gaba ɗaya tunanin sa ya tsaya cak a lokacin, ba abinda ke masa yawo a ka se muryoyin da yaji suna faɗin abinda ze iya kira baƙin labari a kunnen sa.
Be taɓa zato ba haka be taɓa tsammanin jin abin da kunnen sa ya jiye masa a inda ya jin ba, je thought yadda fuskar me wajen take haka zuciyar ma sedai a yau yasan he's mistaken and has been mistaken for long, maybe since from his childhood or even his birth.
Da ƙyar ya iya jan ƙafar sa da tayi masa nauyi sosai ya ƙara sa part ɗin sa, kan royal seats ɗin da suka ƙawata falon ya faɗa har lokacin zuciyar sa bata gama da abinda ya ji ba, sedai ba fa faɗa masa akayi ba haka ba tura shi akayi ba balle yace set up ne, da kansa ya ji komai kuma da kan sa ya kai kan nasa.
Fadila ce ta fito daga kitchen da ɗan cikin ta a gaba da ya tasan ma wata na bakwai, plate ɗin da ta fito dashi daga kitchen tayi kan dining tare da ƙarasawa wajen mijin ta da gani kwance kan kujera bayan be daɗe da fita ba bayan haka kuma ga yanayin da ta ganshi a ciki, zama tayi gefen sa tana ɗaukar kan sa ta ɗora kan laps ɗin ta ta shiga shafa lallausan kwantaccen sumar kansa tsawon lokaci batare da ta ce masa komai ba haka shima dan ta daɗe da karantar mijin nata, in har yana cikin irin wannan yanayin baya son magana har se in shi ya buɗe baki yayi da kansa.
Seda ya ji yanayin sa ya ɗan daidaita kafin ya miƙe ya zauna sosai ya kalle ta tare da sake mata murmushi dan ya kwantar mata da hankali,
"Bari in je wajen Mami, daga can zan wuce aiki, se na dawo, ki kula da kanki da Saraki na kinji".
Ɗaga masa kai tayi tana mayar masa da martanin murmushin da yake mata, bata damu da rashin sanar da ita abinda ke damun sa da be yi ba dan tasan ko ba yanzu ba ze sanar da ita ɗin
"Adawo lafiya, agaida Mami dan yau ban sami shiga ba se zuwa gobe, ni da yayan mu kuwa zaka dawo ka same mu lafiya insha Allah".
Kiss yayi mata a kumatun, goshi da lips sannan ya juya ya fita, gurin Mami za shi ya sanar da ita abinda yaji dan ya zama dole ta san meke faruwa da kuma abinda ya riga ya farun tuntuni, baze iya barin a cikin sa iya shi kaɗai ba dole ya fitar.
Sedai yana zuwa kilisar Mamin kuyangin ta suka sanar da shi tana bacci dole haka ya haƙura ya fita zuwa wajen aiki dan baze so a tashe ta a baccin da ba ko yaushe take samun damar yin isasshe ba.
Ko da ya taso daga wajen aiki a part ɗin baban su ya fara tsayawa ya kai gaisuwa wajen Maimartaba sedai se da yaji ina ma be zo ba dan takardar gayyata Maimartaba ɗin ya bashi na wani banki da ke ƙasar sarbila in da yayi karatu suka gayyace shi aiki na tsawon wata biyu tare dasu gashi a yau ɗin suke buƙatar sa bayan shi kuma yana da abinda yake son aiwatar wa a masarauta.
Sun daɗe dama suna neman shi yana zille wa shine wato suka biyo masa ta hannun Maimartaba ta yarda baze iya kubcewa ba, in ko ze tafi yau to ya zama dole su gana da Mami dan baze iya tafiya da wannan nauyin ba a kansa.
Daga wajen Maimartaba kilisar Mamin ya wuce, be tsaya jiran wani iso ba dan he's in hurry, ita kanta Mamin tana ganin yanayin sa ta ja hannun sa suka shige bedroom ɗin ta.
Kallon fuskar Jamal kawai Mami ke yi cikin tsananin ruɗu da mamakin abinda ya gama sanar da ita a yanzu, bata taɓa zaton haka ba kuma bata taɓa kawo hakan ba ko a makuwar tunani to amma kuma se yanzu wani haske yazo kanta dangane da hakan, in har be zama haka ba ma to ya take son ya zama, dolen dole hakan ne.
Sedai tabbas an shammace ta, yadda take zaune da kowa da zuciya ɗaya yasa bata taɓa zargin kowa dake tare da ita ba, ta sani suna da maƙiya amma bata kawo su a kusa da ita hasalima in da ta kai hasashen ta daban in da kuma ƙiyayyar take daban,
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.