*LULLUƁIN BIRI*
'''DAGA MARUBUCIYAR'''
1-Sirrin Ɓoye
2-Al'amari
3-Hidaya Noor
4-Alhussain
5-Sanadin Talauci
6-Ƙaddarar So
7-Prince Khaleed
Da sauran su.....*2*
"Maijidda na kasa gane wajen".
Fullo ta faɗa a sanda ta ke ƙarewa babban filin wurin kallo. Dukkan tunaninta da hasashenta ta ɗora shi a wurin na fiye da daƙiƙa biyar amma sam ta kasa ta fahimci inda akai haƙan ramin.Maijidda na tsaye itama ta ƙarasa bakin kujerun wajen(resting chairs) ta zauna. Ta ajiye digar da ke hannunta sannan itama tabi wajen da kallo cike da nazari da kuma son tunanowa.
"wallah Fillo nima na kasa tunawa kin san an kwan biyu...amma wai ajiyar me ki kayi ne a wurin nan?".
Fullo bata ce da ita komai ba, sai baki da ta zumɓura mata ta harareta kaɗan. ta zauna bakin tudun da ke wajen tare da naɗe ƙafafunta, kamar wadda ta shiga ajin makarantar allo. Yatsanta manuniya akan leɓanta na ƙasa tana ƙarewa faɗin wajen kallo, da kuma tsirran ciyayin da suka firfito a ƙasar wajen.
Cikin zuciyarta tana ayyana ya za'ai ta manta wajen nan, bayan tasan tsawon watanni biyar da aka ɗauko bata ko zo wurin ba, hoton gun na haska mata acikin idonta a duk san da ta tuno, abu ne da bai shafeta ba bai shafi wani nata ba amma ta kasa mantawa da shi a cikin ranta.Ita dai ta san ta kuɗuri aniyar tarwatsa alƙadarin waɗanda su kai aikin dama wanda ya saka su. Abunda ta ke son sani a yanzu shi ne waima waye Muhammad Turaki?, mene alaƙarsa da waɗanda suke neman ganin bayansa?, wanene shi a cikin gidan nan?, me yasa tsawon shekaru takwas da ta ɗauka tana rayuwa a cikin gidan nan bata taɓa ganin ko da gimlawar inuwarsa ce ba sai yau?, me yasa bata taɓa jin zancensa ba a inda ya dace a dinga ambatonsa?, me ya yiwa masu son kassara rayuwarsa?.
Bata da dukkan amsar waɗannan tambayoyin, sai kawai ta lumshe ido tare da hura iska a bakinta kamin ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya. Bata manta da abunda ya faru ba a wajen, tsawon watanni biyar da suka wuce. Komai yana nan daki-daki a cikin kanta, fuskokin mutanen da su kai aikin ne kawai ba zata iya shaidawa ba, dan a lokacin bayansu da kayan jikinsu kawai ta gani kamar yanda taga Muhammad Turaki a yau, amma ko muryarsu taji a yanzu zata nuna su ta rantse da Allah cewar su ne.
MUHAMMAD TURAKI, harufan sunan da manyan baƙi suka ƙara haskawa cikin idonta, sunan da yake a jikin wannan farar takardar da babu zanen komai acikinta sai na sunansa da jan fenti. Sunan da ta kasa karantawa a randa tayi arangama da layar, kuma haka tayi ta ajiyar takardar har sanda Amir ya shigo cikin rayuwarta, ya fara koya mata karatu har tazo ta iya haɗa harufan a wata takarda ta daban ta maimaita rubutun sunan, sannan ta iya karantawa.
Ita dai bata san asiri ba, bata san ya ake yinsa ba, kuma bata san ya yake ba. amma zata iya rantsewa cewar aikin da waɗannan mutanen su kai asiri ne duk da bata ji sun ambaci wani abu da zai haska mata hakan ba, kuma babu tantanma asirin yana da alaƙa da sunan da ke rubuce ajikin wannan farar takardar da aka maida ita laya.
Abu guda kawai ta san da shi, shine idan har ta manta wurin da akai haƙan aka binne, to ba zata manta maganganun mutanen ba a lokacin da suke aikinsu. Aikin da suka gudanar a sanda ƙafafu suka ɗauke a cikin wannan babban gidan da ba ya rabo da shiga da fice ako da yaushe, ranar da akai naɗin Yarima Abbas zuwa wani matsayi da bata san wane matsayi bane, taji dai labarin irin rikicin da aka sha akan naɗin a wajen Kaka da Yami.
kuma zata iya cewa Allah ya nufeta da zuwa wajen ne saboda ta zama wata hanya ta tarwatsa mugun ƙudurin da ake shirinyi akan wani bawan Allah, tunda tsawon shekarun da ta ɗauka tana rayuwa cikin gidan bata taɓa zuwa wurin ba sai a ranar, lokacin kowa ya watse ana can masarauta ita kuma ta dawo dan ɗaukar ƙwaryar furar da ta dama zata bawa Amir.
A lokacin bata san ta ya ma akai ta kai kanta wajen ba. Ita dai kawai ta ganta ne ta ɓullo ta cikin lambu, ta durƙusa ta ƙasan bishiyan ayaban ta fito, kuma tana fitowa ne taci karo da wasu mutane su uku su na kalle kalle dan tabbatar da babu kowa a wurin da alama basu da gaskiya.