52

142 7 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*52*
samun ta yay a ɗaki ta kifa kai akan gado, da murmushi ya ƙarasa ya ɗagota, murmushinsa ya ƙaru a san da suka haɗa ido, ko ba komai ya ɗanɗana ma ta, kuma yacca ƙwayar idanunta suka sauya ya shaida masa zata buƙaci zumar nan ba da jimawa ba.
ya ɗora hannunsa a chest ɗinta yana cewa,"me ya janyo wannan nishin?".

"ni bana son abin da ka min". ta faɗa tana turo laɓɓa gaba.

"me yasa ba kya so?, ko bakin nawa babu daɗi?". ya faɗa yana ɗan cizonta a kunne.

sai ta ƙara jin kunya, ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa, karatun da Nuratu tayi mata na yawo a cikin kanta, duk sai yanzu take jin maganganun su na yi mata nauyi.

haɓarsa ya ɗora a saman kafaɗarta, ya kai hannunsa saman cikinta yana faɗin,"how many days wancan abun yake yi ya tafi?".

ta ɗago kai tana kallon inda idonsa ke tsaye a wajen, ba ta ga komai ba hakan yasa ta dawo da kallonta gare shi ta ce,"wanne abu?".

yasa bakinsa a kunnenta ya hura iska, hakan ya haifar mata da sake jin kasala, ta lumshe idanuwanta tana jin abun da bata san ko menene ba na tsikararta, a hankali ya ce,"your menstrual blood".

ba ta ce komai ba tayi ƙasa da kanta, ya ɗago fuskarta aiko ta kulle ido, sai ya mintsineta a ciki da sauri kuwa ta buɗe idon tana kallonsa.

"stop ignoring, answer me".
"7days". ta faɗa tana kama gaban rigarsa.

sai ya sauke numfashi ya kamata suka miƙe suka koma kan kujera.
"ga abincin ki". ya faɗa yana ɗebowa da cokali ya kai bakinta.

sai ta tura hannun da yake riƙe da kofin gefe ɗaya, tasa hannu a gefen bakinsa tana faɗin,"na gani".

ya ɗan buɗe bakin sannan ya zaro harshen nasa waje, tasa yatsanta akai kafin ta fara hura iska akansa, ɗumin iskar bakin nata na ratsa shi.
"ya daina zafin?".

gira kawai ya ɗaga ma ta ba tare da yay magana ba, ta shiga tsakanin cinyarsa tana cewa,"ai sai da na faɗi maka da zafi".

"but ai daɗin wannan yasa zafin ya gudu".
ya faɗa yana nuna ɗan ƙaramin bakinta da ta tsuke.

kunun ya shiga bata da kansa, wayarsa dake aljihu tayi ringing ya ɗauko, ya ɗaga kiran Khaleel yana amsa sallamar da yay masa.

Khaleel yace masa,"Hammah naga har yanzu baka shigo office, by 11 fa visitors ɗin nan za su zo".

Turaki ya sosa girarsa ya shafo fuskar Fillo yace,"Fulani nah kina so na fita?".

ta buɗe ido tare da girgiza masa kai.
ya ce da Khaleel,"tunda Bello yana nan ba sai na fito ba".

Khaleel yace,"but Hammah there are some issues fa da ya kamata a tattauna da kai".

"in dai Bello yana nan ka san kamar ina nan ne ko".

Bello da ke jinsa ya karɓi wayar hannun Khaleel yana cewa da shi,"MT wanne irin iskanci ne wannan wai, duk ka tattara komai ka bar min kai ga me aure, to ni ɗan iska na zama kake nufi?, kasan irin baƙar wuyar da nake sha kuwa?, kullum sai nayi ciwon jiki, but Allah ya kai mu next month idan na bari wata ya ƙare banyi aure ba shege nake, sai in ga da wanda zaka yi".

Turaki yay wata dariyar ƙeta yace,"kayi a this month shi ne zan san kai zuciya".

Bello yay tsaki,"don Allah ka fito Malami, ka san dai kai ɗaya zaka iya duba wannan algorithsm ɗin ko?".

jin yay masa shiru ya ƙara cewa,"zan kira Baffa na faɗa masa ba ka zuwa office kwatakwata".

"idan ka fasa".

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now