22

92 12 1
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

*22*
After 4months, cikin ƙaton office ɗin da sanyin Ac ke ta busawa yana haɗewa da daddaɗan ƙamshin turaren dake jikinsa yana bada wani irin sanyayyan ƙamshi me motsa zuciya. Turaki ne zaune akan kujera dake ɗan juyawa da shi gefe zuwa gefe, one of his fingers on his lips, cikin yanayi na nazari akan wani lissafi nasa.
numfashi ya sauke sannan ya shiga operating laptop ɗin dake kan table a gabansa, ya ɗau lokaci kafin ya ɗauƙi wayarsa a gefe yay calling numbern Khalil.
in the next 3minutes sai ga Khalil ya shigo office ɗin, tun shigowansa Turaki ke kallonsa har sanda ya ƙaraso ya zauna kan kujera.

"Director". Turaki ya faɗi sunan da yake kiran Khalil da shi a yanzu tun bayan mallakar wannan company ɗin da sukai. Khalil ɗin shima yana kallonsa ya amsa da nasa sunan da yake kiransa da shi na yanzu. "yes Manager".

anan ne kuma Turaki ya ɓullo da wata magana wadda ta shafi aikin company ɗin nasu, sun ɗau tsawon lokaci suna tattaunawa akan issue ɗin, Khalil nata ƙara kawo dabaru da zasu daɗa ɗaga company ɗin nasu zuwa sama, dan sam basa saka kamfanin nasu a matsayin ƙarami saboda yana sabon buɗewa, so suke cikin ƙaramin lokaci ya kai wani babban mataki da ba kowanne company ke samu ba at once.

a lokacin Turaki ya haɗa urgent meeting da staffs nasu, aka shiga aka ƙara tattaunawa kowa na bada POV nasa akan ganin kamfanin ya haɓɓaka. sai da suka ɗauki tsawon awa guda sannan suka gama.
suna kammalawa kuma Turaki ya bar office ɗin, ya tafi airport ɗauko Bello Ƙaraye wanda ya dawo daga sudan yaje wani course.

akan tinin barin Gombe international airport, cikin motar ƙirar Bugatti, motar da Mai Martaba ya bawa Turaki ita a ranar buɗe company ɗinsu, Bello ya kai hannu yay reducing volume na karatun qur'anin da suke saurare tun barowansu airport, can kuma sai ya kashe gaba ɗaya.

yace,"Kana ciwon baki ne?". Turaki yayi masa shiru bai tanka masa ba, idonsa na manne akan titi.
Bello yay tsaki,"duk inda ɗan rainin hankali yake daga kanka an rufe ƙofa. banda iskanci tun tahowarmu nake magana but you refuse to answer me, kuma tsabar miskilancinka ya kai intaha ina kallon bakinka yana motsi amma ba zaka faɗi abinda ke cikinka ba...i don't know what is exactly wrong with you, i saw some changes in you tun before na tafi, to ni ba ɗan iska bane da zan ta tambayarka kana min banza".

Turaki yace,"ka bani damar magana ne balle na faɗa maka abinda ke cikin nawa?, tun fa da na ɗaukoka ka isheni da Bima Restaurant, sai kace baka taɓa cin abinci ba a duniyarka. tun saukar ka you din't even ask about my health, abinci abinci kawai shi ka sani, kai idan kana jin yunwa you see nothing balle ma ka lura da ramewar da mutum yay".

yanda yay maganar a ƙufule Bello Ƙaraye ya bushe da dariyar ƙeta, shi dai tunda ya fito a jirgi ya kalla kamar idanun Turaki sun faɗa loko, to amma bai lura da muguwar ramewar da yay ba sai yanzu, yanwa yake ji sosai shi yasa idonsa ya rufe da ganin komai.

yace,"to ka bani damar ganin ramar da kayi ne balle nace Muhammad Turaki baka da lafiya ne?, tunda fa da ka ɗaukoni fuskarka take a ɗaure, sannu wannan bata haɗani da kai ba, to ta ina zanga wata rama?, motsin bakinka kawai na lura da shi...anyway what is wrong with you?, did you go to the hospital?".

Turaki yay masa wani kallo yace,"ciwon uban me nace maka ina yi da zanje asibiti?, ni lafiyata ƙalau". Bello yace,"ikon Allah, to naji lafiyarka lau. what is the problem?".

Turaki yay masa shiru yana kallon titin gabansa, cikin ransa yana tunanin ta inda zai fara yi masa maganar, sarai ya san rainin hankalin Bello, yanzu sai ya faɗa masa kuma ya ɗauki maganar a gantale. ba zai nutsu ya fahimci naganar ba balle ya basa damar fayyace masa komai.
Bello dai na gefe yana kallonsa, ganin baida niyyar cewa komai ya ɗaga kafaɗa ya maida hankalinsa kan wayarsa, ko mene idan tayi tsami zaiji, ba zai iya da wannan miskilancin ba, yunwar dake rarakar cikinsa ma ta ishe shi.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now