*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*14*
Fillo tasa hannu ta goge hawayen dake fuskarta, ta ɗaga kai tana bin wayar dake ringing da ido, tunani takeyi akan taje ta ɗaga ko karta ɗaga, ɗaya ɓari na zuciyarta ya rinjayeta akan taje ta ɗaga ɗin.
saboda haka ta yunƙura ta miƙe tsaye jikinta a mace, bata ma ko iya ɗaga ƙafa sai janta take yi har ta ƙarasa inda wayar take manne a bango.ta kai hannu ta ɗaga wayar, daga ɓangaren Hajiya Madina ta kaɓe abinda ke jikin zaninta sannan tace,"Fillo". jin muryarta acikin wayar yasa Fillo saurin saita natsuwarta, sai da ta gyara muryarta sosai sannan ta amsa kiran. "Na'am Maama".
Hajiya Madina tamkar tana kallonta ne a lokacin, don tana jin muryartata tunaninta ya bata kamar da wani abu, apple ne a hannunta a lokacin, amma cikin wani irin zullumi ta ajiye tana tambayar Fillo,"kuka kike yi?".
Fillo ta haɗiye wani abu sannan ta ƙara gyara muryarta tukunna tace,"a'a Maama".
Hajiya Madina tace,"but how comes naji muryarki some how?, wani abu ya faru ne?, ko ba kya jin daɗi?". ta jero tambayoyin ga Fillo muryarta na fita da sautin dake nuna damuwa da kulawa.kamar tana gabanta ta girgiza kanta tace,"a'a Maama lafiya lau". ta faɗa cike da mamakin yanda akai Hajiya Madinan ta gane kuka acikin sound ɗinta farat ɗaya, dan har sai da ta kai ga ta kalli wayar ko dai tana kallonta ne.
Hajiya Madina ta ƙara cewa,"tiles ɗin nan yana da tsantsi sosai i forgot to tell you that, Allah yasa ba faɗuwa kika yi ba wajen yin mopping?". duk da cewar bata fahimci ɗan guntun turancin ba amma ƙarashen maganar ya fahimyar da ita dukkan maganar.
tace,"a'a Maama nayi takatsantsan, har na gama ban zame ba". Hajiya Madina tace,"to yayi kyau, kin gama aikin?".
tace,"ehh yanzu nake shirin rufe ɗakin". Hajiya Madina tace,"me amsar saƙon da na baki yazo yana ta jiranki, kije ki kai masa sannan ki ƙarasa aikin...muma mun kusa dawowa muna jira Boɗejo ta shirya ne tare zamu taho". tace,"tom Maama Allah ya dawo daku lafiya".da haka wayar tasu ta katse, Fillo tabi wayar da kallo tana jin son Hajiya Madina har cikin ranta, a iya ɗan zaman da tai ta gama karantar matar, zata rantse duk wanda ya faɗi aibun Hajiya Madina to ɗan hassadarta ne.
macece da bata da ɗagawa ko kaɗan, bata tunƙaho da arziƙinsu, bata wulaƙanta talaka, bata da ƙasƙanci, kowa nata ne, kowa ganinsa ta ke ɗaya suke, kowa sonsa ta ke yi, mutumta duk wanda yake tare da ita takeyi babu tozarci.ƙasa ta duƙa ta tattara takardun ta mayar cikin file ɗin da suka faɗo, sannan ta mayar cikin wata drower daban da wadda suke ciki da.
ta fita daga ɗakin jiki a saɓule, da ƙyar ma take yin tafiyar tamkar me ƙarancin jini a jiki, tana saukowa daga upstairs ɗinne cikin tsautsayi ta gurɗe ƙafa.bakinta ya furta bismillah kafin ƴar ƙarar da ta saki ta biyo baya. cikin jin zafi da raɗaɗi na lokaci guda ta riƙe ƙafar tana cije fuska.
gurɗewar ba ƙarama bace, dalilin da yasa idanuwanta suka cika da tarin hawaye kenan, wani sabon kukan ya ƙaru akan wanda zuciyarta bata gama yinsa ba, sai da ta ɗauki kusan 4minutes sannan ta tashi ta sauko da ƙyar sai ɗingisa ƙafar takeyi, sai da ta kashe light na parlon tukunna ta bar side ɗin.a ƙofar ɗakin me gadi ta tarar da mutumin, baƙi ne kamar yanda Hajiya Madina ta sanar mata, yana da curar ƙasumba, fuskarsa kuma sam babu fara'a. me gadi dake jin radio ganinta yasa shi yin murmushi, ta rissina ta gaishe shi ya amsa mata yana tambayarta ya aiki, ta amsa masa da lafiya.
sannan ta tsuguna a gaban mutumin da ko inda take bai kalla ba tun zuwanta, bata sani ba ko haka yake ko kuma ita yakewa hakan dan ta ɓata masa lokaci oho. "ina yini".
ya kalleta ta wutsiyar ido, kamar ba zai amsa ba can kuma yace,"lafiya".ta fito da hannunta daga cikin hijab wanda ke ɗauke da file ta miƙa masa tace,"ga shi wannan tace a baka".
sai da yayi mata wani kallo kafin ya warta, dan ba zata kira hakan da karɓa ba sai dai warcewar, hakan kuma ya ɓata mata rai, ta miƙe cikin ɗaurewar fuska.