*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*12*
bayan ta gama jera komai a dining tazo ta tsuguna gaban Hajiya Madina. "Maama ko mai ya kammala". sunan da yaranta ke kiranta da shi itama da shi ta ke kiranta, Hajiya Madinar ta faɗa mata haka a watarana, sanda ta ke ce mata. "Fillo ban taɓa ƴar aikin da nake jinta tamkar ƴar cikina ba irinki, saboda haka daga yau Hajiya ya fita daga bakinki, ki dinga kirana da Maama kamar yanda kika ji ƴaƴana nace min kinji".Hajiya Madina ta shiga kallonta ta wutsiyar idonta ba tare da ta amsawa maganarta ba, Fillo kuma dai har yanzu tana nan durƙushe bata motsa ba, kuma tunaninta bai bata ko Hajiya Madinar bata ji ba ne, a'a tasan taji kawai dai a jininsu ne basa amsa maka nan ta ke sai sun ɗan ɗau lokaci.
"oak tom, kije ki zuba naki kici". abinda Hajiya Madina tace da ita kenan. Fillo ta miƙe ta wuce, sannan suma suka nufa dining, by the time Turaki har ya gama nasa, yana zaune wajen yana aikin danna waya.
suna cikin yin breakfast ɗin ne wayar Nihal tayi ƙara, ganin sunan dake yawo jikin screen ɗin wayar gabanta ya faɗi, jikinta na rawa ta kai hannu tana gyara zaman medical glass nata, ta cikinsa ta ke kallon Hajiya Madina wacce ta dakata da cin abincin tana yi mata wani duba ta ƙasan ido.duk ta dabarbarce, tsoronta Allah tsoronta kar tace ta miƙa mata wayar. saboda haka tayi saurin kai hannu tai mute na ringing ɗin, sai dai kamin ta ɗauke hannunta daga kan wayar sabon kira ya ƙara shigowa. babu shiri ta haɗiye wani dunƙulallan yawu tare da rufe ido.
sai dai kamin ta buɗe maganar Hajiya Madina ta shiga cikin kunnuwanta."give me the phone". kamar zata yi kuka ta ɗauki wayar hannu na rawa ta miƙa mata.
Hajiya Madina ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta miƙawa Khalil, ya karɓa ya saka a aljihunsa.
har suka kammala breakfast ɗin babu wani wanda yay motsi na hira ko kuma tsokanar juna kamar yanda suka saba da mahaifiyar tasu, saboda yanayin da ta tashi da shi yau sun kasa gane kanta, ga shi Nihal ta ƙara dagula musu ita.Samha ta ɗaga landline en dake gefensu ta kira wayar ɗakin ma'aikata. bugun da bai wuce 2 ba Fillo dake can ta ɗaga. "ke kizo mun kammala". abinda tace da Fillo kenan ta kashe wayar. wanda a ɓangarenta azamar tashin ta ke yi saboda tana lissafe ne da lokaci, su kan ɗauki 10-15minutes a dining, kuma buƙatarsu da zarar sun kammala da shi ai clearing wurin.
tana shigowa parlon Hajiya Madina na shirin hawa upstairs, ta kalleta tace mata.
"idan kin gama ki sameni a ɗaki". Fillo ta amsa da,"tou". sannan ta shiga gyara wajen.
komai nata cikin sanyin jiki ta ke yinsa amma kuma nan da nan ta ke gama abu, tana gama wanke-wanke bata tsaya ɗora lunch ba tunda tasan basa nan kuma bai wuce suyo takeaway na dinner ba idan sun tashi dawowa.zata wuce ɗakin Hajiya Madina Khalil dake parlon a zaune shi ɗaya ya tsayar da ita.
"sojan rana zo nan".
ta tsaya daga hawa saman ta juyo da murmushi fuskarta, abunda ke burge shi da ita fara'arta da tsabtarta, bata da wannan cunkus ɗin irin na sauran ƴan aikin da suka yi a baya.har ta ƙaraso ta tsuguna a gefen kujerar da yake zaune bai bar kallonta ba, kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace,"Hamma Khalil gani". ta faɗi sunan nasa kamar yanda taji ƙannensa na faɗa masa.
yace,"ai nai zaton ko kina ciwon baki ne". ya faɗa da salon zolaya.ta murmusa da cewan,"ciwon baki kuma?".
yace,"ehh mana, da na kiraki ai ba ki amsa ba tahowa kawai kika yi".
ta saki murmushi me faɗi da cewar,"Hamma Khalil to ai kaine kake faɗin sunan da ba nawa ba, shisa sai nayi zaton ko bada ni kake ba".shima murmusawar yay kafin yace,"yanzu ke tsakani da Allah duk wanda ya ganki ranar nan da kika yi ƙeƙam a tsakiyar rana me zai yi zato?, kinga kam dan na kiraki da sojan rana ai ba laifi ba ne".
murmushi kawai tayi bata ce komai ba."anyway, wanne class kike before ki taho aikatau?".
furucin da yay yasa ta ɗagowa ta kalle shi kaɗan sannan ta mayar da kanta ƙasa.
"bana zuwa makaranta ai".
da mamaki ya kalleta,"gaba ɗaya ba ki taɓa zuwa makarantar boko ba?".
ta ɗaga masa kai tabbacin hakan.