*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*9*
Khalil ya kalli me gadi daya buɗe masa gate,"waccan fa?". ya tambaye shi yana Indicavit masa Fillo.Me gadin yace,"ehh tou Yallaɓai nima dai bayan fitowata daga banɗaki nan na ganta tsaye, ina ce ma cikin masu aiki".
Khalil ya maida kallonsa ga Fillo, ba fuskarta yake kallo ba, side view ɗinta kawai yake iya gani, tsinin hancin nan ya fita ta gefe kamar allura. to ai kaf cikin masu aikin babu fara kamar wannan, infact bama sa gari dukansu, banda tsohuwar da ya gani jiya su Samha suka ce masa ita ke aiki yanzu kamin a sami wasu.
to ko dai ba mutum bace?, banda haka ya za'ai bawa yazo cikin rana ya tsaya sama da minti biyar, kuma bai ganta da jakar kaya ba balle yace baƙuwa ce ta shigo, to wannan ƴar ƙauyen ma baƙuwar wa zai ce?, yana da tabbacin ba tasu bace, and cikin yaran gidan babu me yin ƙawance da wannan villager ɗin.
ba tare da ya dubi me gadin ba yace,"baka ga lokacin da ta shigo ba ne?".
"a'a ranka ya daɗe, bata nan ta shigo ba gaskiya, dan ko second ɗaya banyi da shiga ɗaki na ɗakko radio ba na fito, can kuma ina ɗaga kai na hangeta tsaye a wurin".
mamaki ya kama Khalil, ya bar motar a buɗe ya nufi inda ta ke, me gadin ya mara masa baya.
taji zuwan mutum wurin, taga kuma inuwarsu a ƙasa inda idonta yake kallo, amma sai tayi kamar bata san da zuwan kowa ba. ai yana kallonta ɗazu yazo ya wuceta yay shigewarsa ciki, ya ƙara fitowa ya wuceta ko sannu kamar bai san darajar ɗan adam ba.To yanzu da ya dawo ya tsaya gabanta me ya dawo da shi ko kuma me zai mata?, tukunna ma shirun da yay bai yi magana ba yana jiran cewarta ne?, ashe kuwa wannan ranar zata ƙare akansu.
Shi kam Khalil tsayawa yayi yana ƙare mata kallo da yanda ta ke wasa da yatsun hannunta, yatsunta sirara dogwaye gwanin sha'awa, farcenta fari ƙal da shi.abunda zuciyarsa ta raya masa shine yarinyar kurma ce ko kuma makauniya, tunda ga shi dai ko yanzu da ya tabbatar tasan da tsayuwarsu a gabanta ko motsi bata yi ba, tana nan kamar wadda aka sassaƙa. yanayinta ne kaɗai zai nuna maka ba'a waye ta ke ba, amma kyawun surarta ba zaka taɓa cewa hakan ba.
"lafiya dai?". Ya tambaya idonsa tarr akanta.
Ta ɗago kyawawan idanuwanta farare ƙal da babu ko kwalli ta ɗan kalle shi, tukunna ta mayar da idonta ƙasa tace,"aiki nazo yi?".
Da mamaki yace,"Wanne irin aiki?".
Har yanzu idonta na ƙasa ta ba shi amsa da cewa,"ni dai haka aka ce nazo nayi aiki, Kakata ce ke yi, ita kuma yau bata lafiya".
Khalil ya gyara tsayuwa tare da cewa,"kuma sai tace miki idan tazo aikin cikin rana ta ke nema ta tsaya?".
ta girgiza kai tace,"a'a, ban san inda zan shiga nayi aikin ba ne".yana daɗa ma ta duban tsanaki, a cikin ƴan ƙauyen ma wannan lamba ɗaya ce.
yay wani guntun tsaki yace,"shi kuma bakinki wari yake yi da ba za ki iya buɗe shi kiyi tambaya ba?".
muryarta tayi sanyi yayin faɗin,"ai banga mutane ba ne".
Yay mata wani kallon up and down na ban haushi sannan yace,"shi me gadin da kika gani dodo ne ko?".
Fillo na ƙifta idanuwa ta ɗago zata dube shi taga har ya bar wajen, tabi bayan nasa da kallo, saurin tafiya yake amma ba zaka gane hakan ba a lokaci ɗaya.Tana jan yatsunta hannunta tace da me gadin,"Baba ina zan shiga?, ginin ne na gansa da yawa".
"ko dan gaba in kika je wuri ki dinga tambaya, ai matambayi baya ɓata".
Me gadin ya faɗa yana yi mata nuni da part ɗin Hajiya Madina.
Cikin sanyin tafiyarta ta wuce, kawai tsayawa tayi a bakin ƙofar dan bata san ta yanda zata buɗe ba, bata taɓa ganin irin wannan ƙofar ba, inda ma ace handle ne irin wanda ta saba gani sai ta murɗa wataƙila ta buɗe, amma wannan ma ai ba ƙofa bace glass ne kawai.
Kusan 2minutes tana tunanin ta yanda zata shiga, sai gani tayi an turo ƙofar daga ciki ta buɗe. ta kalli Sameer wanda ya fito bai lura da ita ba, ya saki ƙofan ta ƙarasa rufe kanta sannan ya fara taka steps zai sauka.