6

128 7 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

*6*

Yau ya kasance juma'a. Ƙofar gidan na Judge Dikko Habib cike yake da ɗumbin mutane masu zuwa karɓan sadaqa, yara da manya musamman ma magidanta marasa ƙarfi, haka gidan yake kasancewa a duk wata juma'a, zaka ga mutane babu masaka tsinke tun an idar da sallar asubahi sun bi layi suna jiran fitowar Mai gidan.

Judge Dikko Habib babban alƙali ne wanda ake damawa da shi a manyan shari'ar da ta shafi cikin ƙasa da wajenta, kuma alƙalin da gwamnatin tarayya keji da shi. Dattijon ƙwarai mai halin dattako da nagarta, Yawancin zamansa a america yay, karatunsa ma tun daga secondry har matakin phd duka acan yayi.

Matansa Biyu Hajiya Ramla da Hajiya Madina amma ainihin sunanta Aina'u, Ƴaƴansa 6, uku maza uku mata. Kuma kaf cikinsu babu wanda ke karatu a nigeria duka waje yake fitar da su. Turaki ne ma kawai yayi secondry a nigeria kamin ya fita US yay degree da masters ɗinsa acan.

Idan yazo zai bawa kowa sadaqa zai bashi kuɗi dubu uku, sai ma'aikatan gidan maza su bika da kwanon shinkafa, taliya guda biyu da kwalaban farin mai da manja. Judge Dikko baya taɓa barin wajen har sai ya tabbatar da kowa ya samu, duk kuwa da uban yawan da mutanen ke da, baya gajiyawa kuma baya ƙosawa, hakana duk nisan tafiyar da yayi duk irin muhimmancinta zai katse kome yake yi ya dawo alhamis dan kawai waɗannan mutanen da Allah ya ba shi ikon taimaka musu.

Ya faɗa saveral times gani yake idan har ba shine da kansa ba to ba za'a riƙe amana kamar yanda ya bayar ba, saudiya kawai yake tafiya ya iya haƙura, shima kuma sai ya kira Muhammad Turaki a duk inda yake ya dawo ya tsaya akan ragamar abun, dan shi kaɗai yake ganin zai iya kwatankwacin abinda shi zai yi da kansa.

Kuma a wannan juma'ar ne ma'aikatan gidan basa samun hutu ko kaɗan, dan tun daga safe har dare suna rabon abincin sadaqa.

Ƙarfe goma da rabi Baffa ya dawo cikin gidan daga rabon sadaqar daya fita, Khalil dake ƙoƙarin shiga motarsa zai fita ya hange shi, hakan yasa ya rufe motar ya taho da sauri.
Ya rissina a gaban mahaifin nasa cike da girmamawa yana faɗin,"Barka da dawowa Baffa". tare da miƙa hannu don karɓar jakar hannunsa, wadda yake zuba kuɗin sadaqa ya fita da ita.

Baffan ya dube shi yace,"ba fita zaka yi ba?".

"fitar ba wata mai muhimmanci bace". Ya faɗa yana ƙara miƙa hannu don amsar jakar. Baffan ya miƙa masa, shi kuma yana masa sannu tare da adu'ar Allah ya bada lada a irin ayyukan alkhairan da yake yi.

Tare suka jera suna tafiya, suna entrance na shiga parlo Baffa yace da Khalil.
"Muhammadu ya dawo ne?".
"a'a bai dawo ba".
"amma ɗazu sai naga motarsa".
"ai dama ba da ita ya tafi ba, da GLK ya tafi".

Baffa bai ce komai ba ya shiga katafaren parlonsa bayan Khalil ya buɗe masa ƙofa. Hajiya Madina coming down from stairs take welcoming nasa. Khalil ya miƙa mata jakar hannunsa tace ya wuce ya kai bedroom ɗin Baffa.

Tana gyara dining area ta ke cewa Baffa, "yau ka dawo da wuri, hala ba'a taru ba yanda aka saba".
"ba haka bane, jikina nake jinsa babu daɗi".
"subhanallahi". Ta faɗa a sanda tayi saurin barin abinda ta ke yi ta dawo kusa da shi ta zauna.

Tana taɓa jikinsa looking worried tace,"i hope ba ciwonka ne zai tashi ba". Tai maganar tana ɓalle maɓallin gaban rigarsa. Sannan ta miƙe tana cewa,"let me reduce the AC".

Kayan breakfast ta ɗauko ta dawo da shi gabansa ta aje saman wani medium glass table. His favorite dish kunun gyaɗa da awaran ƙwai, da kanta ta ke feeding nasa tana jera masa sannu, bayan ya gama ta bashi drugs sannan ta buƙaci daya tashi ya koma bedroom yace a'a ta barshi nan.

Ƙasa ya sauko ya zauna kan tattausan carpet ɗin dake malale, haɗuwar parlon da tsaruwarsa kace turakar sarki, ya kishingiɗa da tum tum ɗin dake gefensa, in a state of misery yace.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now