*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya**5*
Fitarta da minti biyar akai knocking ɗin door, ba tare da ya ɗago kansa daga kan system ba yace,"yes come in".
Muryar nasa ya fito a hankali yayin da hannunsa guda ke dunƙule a gefen bakinsa.Bello ƙaraye ya shigo cikin office ɗin ya zauna akan kujera, ya fuskanci Turaki da har yanzu bai ɗago ido ya kalle shi ba yace da shi.
"sai yanzu ka ga damar fitowan?".
Turaki na typing a Laptop yace,"kai ma dai kasan ba mata gare ni ba balle na sami me tashina da wuri".
Bello Ƙaraye yay masa wani duba yace,"tun yaushe ake cewa kayi auren kaƙi. ni na rasa ruwan idon uban me ka tsaya yi da har yanzu ka rasa macen da tayi maka".
Turaki yace,"Lokacina ne bai yi ba, ko kaga nayi girman da za'a dinga tarata da maganar aure ne?".
Bello ya harare shi yace,"sannu motsin gado".
Turaki yace,"Yauwa, don haka sai a barni na sarara".Bello ya ƙara cewa,"yanzu Asma'u ɗin ma bata yi maka ba?".
"yes, she is not beautifull enough, and you know me well bana son abu mara kyau...idan kana sonta ka ƙara ata biyu na bar maka".Bello dake masa wani kallo yace,"Ba ka da hankali...let close the charpter kamin ka ɓata min rai. kuma bari na faɗa maka, ka daina discouraging mutum akan abunda kai bai yi maka ba alhalin shi yayi masa, Ishaq told me you were telling him to get rid of that girl after all kasan yayi magana da iyayen yarinyar nan...tsaya ma! just because you think the girl was too local shikenan sai akace ba za'a aureta ba?".
Turaki yay guntun tsaki yace,"ka zo muyi magana akan aiki ne ko kuma zamu tsaya kan shirmen zancenka ne, da baku da aiki sai zancen soyayya, mace, aure".
Har yay shiru sai kuma ya ƙara cewa,"to for what reason ma yana da degree har biyu zai je ya ɗauko yarinyar da she didn't even finish secondary school".
"to kai ina ruwanka?, shi ai yasan da hakan yaje ya ɗauko ta ko".
Turaki yay tsaki, Bello bai ce da shi komai ba ya fiddo laptop ɗinsa daga cikin jaka. Yay danne danne ya juyar da fuskar laptop ɗin yana nunawa Turaki.
"Na sami number'n contractor ɗin, zanyi waya da shi zuwa dare".
Turaki ya faɗa sanda ya gama karanta rubutun da ke jiki, sannan ya miƙe daga kujerarsa zuwa gaban wata drower da tarin takardu suke a cikinta.Bello Ƙaraye na binsa da kallo har ya taka steps, hannunsa ya kai cikin drower ɗin yana fito da wani file ƙunshe da takardu fal a ciki. Ya dawo kan kujerarsa yana duba takardun cikin file ɗin. Bayan yay musu ɗai-ɗai ya kwashi wanda zai amfani da su ya wuce cikin madaidaicn parlon cikin office ɗin, daga bisani Bello ya mara masa baya.
Tsaye ya tarar da shi yana fuskantar gilashin windo, ya harɗe hannunsa guda ɗaya ta baya. Idanunsa na kafe ne akan glass ɗin kamar mai son ɗakko wani abu ajiki. Bello ya zauna kan kujera yana ƙarewa tsayuwar Turaki kallo, tsayuwar nan tasa mai cike da ƙasaita da taƙama, kana kallo zaka san an gaji sarauta cikin jini da asali.
Sanyin Ac yasa idanuwan Turaki lumshewa, muryarsa a kausashe yace, "tunda naji ana talking of billions tunanina ya bani da akwai wata a ƙasa".
Ya faɗa sannan ya juyo ya zauna kan kujerar da ke fuskartar Bello, ya shafo fuskarsa da duka tafukan hannunsa biyu kamin yace,"dole ne ma ba zamu yi aiki da wannan company ɗin ba".
Bello ya dube shi da mamaki yace,"saboda me?".
"yanzu Accounter suka fita shi da mutanen nan".
"ta ina kai ka gansu?".
"a bakin gate suka tsaya, shi kuma ya fita da mota ya ɗebe su".