*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Please avoid any mistakes._
*25*
"barka da shigowa ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya magajin me gida". adu'ar da ma'aikatan ke tayi masa kenan tunda ya shigo ɓangaren su.
yasa hannu a aljihu ya ɗauko bandir na kuɗi ya bawa shugabar ma'aikatan wato Yami, ta duƙa har can ƙasa tasa hannu biyu ta karɓa suna ƙara yi masa adu'oi na fatan alkhairi.tun da ya nufi ɗakin Kaka aka je aka sanar mata, kamin ya ƙaraso tuni ta daɗa kimtsa wurin ta kunna turaren ƙamshi. Turaki yayi sallama a ƙofar ɗakin idonsa na mannewa akan yagalgalallan labulen ɗakin, Kaka ta taso da sauri tazo ta buɗe labulen tana faɗin,"Barka da zuwa ranka ya daɗe".
ta yaye masa labulen shi kuma ya shiga, sai bayan ya zauna sun gaisa da Kaka sannan ya fara tunanin acutual abinda ya kawosa.
tun bayan gaisawar su da Kaka ya kafe ƙofar ɗakinta da ido, ta yanda ba zaka taɓa fahimtar ga inda yake kallo ba, sama da mintina goma shiru bai ga alamar Fillo ko inuwar Fillo zata fito daga cikin ɗakin ba, kuma motsi kaɗan zai ji daga waje sai ya juyar da ƙwayar idonsa zuwa bakin ƙofa yaga ko ita ce, but sai yaga babu kowa.ya sauke numfashi a daidai sanda zuciyarsa ke ayyana masa tasirantuwar wani abu, kuma lokacin ne Maijidda ta shigo ɗakin tana ta mita. ganinsa yasa tai saurin zube gwiwoyinta a ƙasa tana gaida shi. bai amsa mata da baki illa kansa kawai da ya ɗaga mata.
ya miƙe ya yiwa Kaka sallama ya tafi, Kaka ta bawa Maijidda furar da ta dama ta bisa da ita.daga can ɗakin Hajiya Madina Fillo ce zaune a gabanta, kanta a ƙasa, idanuwanta sun cika da ruwan hawaye, tana jin kanta na mugun sara mata kamar zai faɗo ƙasa, maganganun Hajiya Madina nema suke su juyar mata da dukkan wani tunani nata, a yanda dukkan zancen Hajiya Madina suka ratsa jikinta bata jin zata iya ko da ɗaga ɗan yatsa guda a yanzu dai.
Hajiya Madina da idanuwanta ke manne akan Fillo itama nata idanun na zubar da ruwan hawaye tace,"wannan shine dalilin da yasa nace miki ina so ki nutsu kiyi karatu, kuma wannan aikin shine wanda nake faɗa miki zaki yi min Fillo, tun a kallon farko da nayi miki zuciyata ta faɗa min zaki iya, hakan yasa na zaɓe ki, ina fatan kuma zaki warware komai cikin sauƙi ba tare da abunda nake gudu ya faru ba".
a wannan karon da Hajiya Madina tayi magana, sai Fillo taji kamar tana neman ta tarwatse gaba ɗayanta ne. manyan idanuwanta suka maƙale a kan ƙafar Hajiya Madina dake cikin wani tsadaddan takalmi, so take ta haɗe dukkan maganganun Hajiya Madina wuri guda sannan ta watsar da su a gefe ɗaya, domin bata tunanin akwai ta yanda zata yarda cewar wannan jarumar matar dake gabanta ba itace mahaifiyar Turaki ba. amma dolenta a yau kuma a yanzu ta yarda da hakan, ta yarda da wannan macen ba ita bace asalin mahaifiya wacce ake kira uwa a wajen su Turaki ba.
"ban san me zance miki ba Maama, abu ɗaya kawai da na san ya zama dole shine jinjinawa, dole zan jinjina miki, kamar yanda na jinjinawa masu farautar rayuwar Turaki".
ta faɗi hakan tana me ɗagowa ta sanya idanuwanta cikin ƙwayar idon Hajiya Madina, sannan ta iya miƙewa jiki a saɓule tana jin kamar ba zata iya tafiya ba, ta bar ɗakin tana barin Hajiya Madina a cikin tsananin tashin hankalin da ba zai misaltu ba.a parlo ta tarar da Samha zata hau stairs wurin Maama, tana jinta tana yi mata magana tayi mata banza bata ko kalleta ba. ta baro side ɗin cike da mamaki da tunani kala-kala acikin ranta, kuma cike da tsoron ɗan'adam, ko waye shi kuma ko ya kuke da shi.
a coumpound ta tarar da Ɗausiyya acan wajen bakin famfo tana wanki, ta ƙarasa wurinta tana ce mata. "idan teacher yazo ki faɗa masa bani da lafiya, ba zan iya karatu ba yau. please ki basa assignment ɗina kar yay zaton ko saboda shi naƙi zuwa".Ɗausiyya na kallonta tace,"tun jiya kike kuka Fillo, kuma na tambaye ki kince ciwon kai ne kawai, ni dai wallahi ban yarda dake ba. dan Allah ki faɗa min ko da wata damuwar, mun riga fa mun zama ɗaya".