*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*23*
ya ƙara maimaitawa,"help me pleaseeee". ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta. Fillo ta haɗiye yawun bakinta da ƙyar, ita bata taɓa jinta a jikin ɗa namiji ba ko da Yayanta Hamid. amma yau itace gaɓa ɗaya cikin jikin wani ƙaton ya ƙanƙameta, ƙanƙamar da tasa ta jin kasala, kuma tana ta ƙoƙarin ta fita a jikin nasa ta kasa.
sai tayi shiru kawai tana sauraren yanda zuciyarsa ke bugawa, beat ɗin na fita da ƙarfin gaske, sai taji tana jin tsoro.
muryarta a hankali tace,"taimakon me zanyi maka?". ta faɗa tana so ta raba jikin nata da nasa, lokaci ɗaya sai tsoronta ya ƙaru jin yacca jikinsa ya saki gaba ɗaya.ta fita daga jikin nasa a sanda ya tafi luu ya faɗi ƙasa, bata san lokacin da ta kurma uban ihu tana tallafo kansa da sauri. ta shiga girgiza shi tana cewa,"ka faɗa min taimakon me zan maka?, me kake so na maka?, Turaki ka tashi dan Allah".
kuka take sosai tana cewa ya tashi, da dai ta tabbatar cewa ya suma sai ta miƙe a ruɗe ta fice daga ɗakin, har ta kai step na ƙarshe zata sauka daga stairs sai kuma ta fara tunanin idan ta tafi ta barsa shi ɗaya cikin wannan halin me zai iya faruwa da shi?.
dan haka da sauri ta ƙara komawa har tana kusa zamewa, Allah ya taƙaita tsautsayi bata faɗo daga benen ba.yana nan a sumen har yanzu, tai kansa cikin kiɗima tana ƙara jijjigasa tana cewa,"ka tashi don Allah, ka tashi ka faɗa min duk abinda kake so zanyi, zan taimaka da ko menene ko da ace zan rasa raina ta sanadin hakan".
duk wata dabara nata da tunaninta ya gushe a brain ɗinta, tayi dirshen a wajen tana ta kuka abinta, tsoronta Allah tsoronta ace mutuwa yayi, wa ya kashe shi?. sai kawai ta ƙara fashewa da kuka tana tallafo kansa zuwa kan cinyarta, tasa hannu ta share hawayenta tana ta maganganu ita ɗaya.
"kar ka yi min haka dan Allah, kar ka mutu a sanda yake daga ni sai kai a wajen, za'a ce ni na kashe ka, wallahi haka zasu ce. kuma ni ban san komai ba, ban san me ya sameka ba, dan Allah dan Annabi ka farka karka mutu yanzu, ka farka ka faɗa min duk abinda kake so, ka faɗan duk kalan taimakon da zanyi maka, ni kuma nayi alƙawarin zan maka shi".
ta ƙarasa maganar tana kifa goshinta akan nasa, sam sam bata san me ya kamata tayi a yanzu ba, abu ɗaya ta sani, shine ba zata taɓa fita ta barsa shi ɗaya a cikin wannan halin ba. can kawai sai taji zuciyarta na faɗa mata cewar ta kira waya, ta kira Maama ta sanar mata komai, to amma da wacce wayar?.
ɗago da kanta tayi ta fara laluben aljihunsa dan ɗauko wayarsa, ta gama lalubenta bata ji komai ba sai wallet ɗinsa. tunaninta wayar ko tana cikin wallet ɗin ne, hakan yasa ta buɗe wallet ɗin da niyyar ɗaukowa, amma da mamakinta tana buɗewa taci karo da hoton mutum biyu, na Zaytuna da kuma Dattijuwar matar da ta gani a jikin wancan hoton.
kanta ya ƙara ƙullewa ta rasa wanne irin tunani za tai akan lamarin dake yawo cikin ranta, yanzu ba lokacin buƙatar lallai sai ta san komai ba ne, yanzu lokaci ne na kuɓutar da Turaki da take ganin kamar rayuwarsa tana jingine da ita ne, warwarewar abunda bata sani ba shi yafi komai sauƙi a wajenta, idan ya farka zata zauna ta zana komai dake ƙulle cikin kanta a tsakiyar tafin hannunta, tukunna ta karance shi da zurfin tunaninta, idan lissafin nata yayi dai-dai, to ta tabbata daga nan zata warware komai a cikin sauƙi.
cikin azama ta miƙe ta nufi hanyar fita sai Allah ya nufeta da ganin wayarsa akan locker, ta isa wajen ta ɗau wayar hannunta sai karkarwa yake.
ba security a wayar, dan haka tana buɗewa kai tsaye lambar Maama ta laluba, bata ma san ta yanda akai ta iya wayar ba tunda ba taɓa riƙe waya tayi ba a rayuwarta, ko wayar Yami ma tsakaninta da ita in Amir ya kira Maijidda ta kawo mata tasa mata a kunne, amma ko ɗaga waya bata taɓa yi da kanta ba.scrolling kawai take a ɓangaren miscalls amma ta rasa lambar da ta dace ta kira, bata san wani Bello Ƙaraye ba, haka bata san lambobin biyun da babu suna a jiki na waye ba, fita tai daga ɓangaren call ta shiga contact, take taci karo da sunan My world, cikin sauri ta danna kiran ya tafi. daga can ɓangaren Hajiya Madina da ke zaune akan kujerar dake cikin ɗakinta.