*LULLUƁIN BIRI*
*45*
Boɗejo ta ƙara ɗaure fuska a sanda take isowa kan Turaki ta tsaya.
"mara mutuncin banza da wofi, kai har nawa kake da zaka raina ni?, har ni ina maka magana ka yi banza da ni ka ƙaro gaba wato ga ƙatuwar shashasha na yi maka magana ko?, ko da yake babu komai, ba ni karaina ba ubanka ka raina".ta gyara zaman gyalenta tana saka hannu ta ɗago kansa sama,"wallahi bari kaji na faɗa maka kayi kaɗan kace zaka wulaƙanta min Ilham, sanin kanka ne kaf jikokina na fi ƙaunarta, ba'a haifeka ba ba'a haifi uwar da zata haifeka ba, ɗan iskan banza yaushe kaciyarka ta girma har da kake jin kafi ƙarfin kabi umarnina da na ubanka. kai ka sa ni dai Ilham tafi ƙarfin wulaƙancinka, domin kuwa ta fika gata, ita ɗaya a wajen uwarta bata taso ta san wata aba damuwa ba, saboda haka baka isa kace zaka haɗata da kishiya ba, kishiyar ma mara aji ƙasƙantacciya wadda tayi aiki a gidanku, haba dai cin mutunci haka har ina!, a wanne garin mahaukatan ma ka taɓa jin an yiwa mace kishiya alhalin ko shekara bata rufa ba, ka tambayi uwarka kaji shekarun da ta rufa bata taɓa ɓatan wata ba kafin ayi mata kishiya, duk da dai na san cewa ba kowa ke zugaka ba illa waɗannan munfukan marasa yafiya da haƙuri".
ta faɗa tana nuna Hajiya Ramla da Hajiya Madina da baki tana bin su da harara.
"kuskure uban waye ba ya yinsa, haka laifi uban waye ba ya yinsa, ku waye ya san adadin laifin da ku ka yiwa ubangiji kuma ku ka roƙe shi ya yafe muku. dan uwar yarinya tayi masa laifi ai ba yana nufin yarinyar ce da kanta tayi masa ba, ku wa yasan kalar mutanen ma da ku ka yiwa sharrin da yafi wanda tayi masa, kuma naga dai anyi shekara da shekaru da yin abun, kuma ke Madina bace kika yi kun yafe ba, amma saboda dai zuciyarki baƙa ce sai yanzu za ki wani fa-ke da abunda aka riga aka manta da shi, saboda dama kina baƙin ciki da gatan da Allah ya yiwa Ilham wanda ƴaƴanki basu samu ba, to kuwa sai dai ki haɗiyi zuciya ki mutu domin gata da mulki da jin daɗi da ilimi da tarbiyya Ilham ta yiwa ƴaƴanki zarra, har a naɗe duniya kuma ba zasu samu abunda ta samu ba".ta maida hankalinta kan Turaki,"mara imani wanda bai da tausayi, yarinya bata da lafiya amma ka iya tsallaketa kasa ƙafa ka bar gidan saboda ga ka baƙin mugu azzalumi, to idan ba ka sa ni ba ka sa ni, akan Ilham ina iya ɓatawa da uban kowa, in nace uban kowa har da nata uban kuwa, ka ga kenan naka uban ba komai ba ne a idona. saboda haka yanzu tun muna ta lafiya lafiya ban ja abinda zai hana kowa kwanciyar hankali ba to ka miƙe ka wuce muje ka kaita asibiti, shege ɗan banza ka samu ka ɗirkawa yarinya ciki shi ne za ka watsar da ita, to miƙe mu tafi, alhakin kulawa da ita ai akanka ya ke yanzu ba'a kan iyayenta ba".
shi dai kansa har lokacin na ƙasa yana ta kallon rubutun sakin da yay, ya rasa gaba ɗaya me ma yake ji a tare da shi, tsabar bala'in ciwon da kansa ke yi masa ji yake kamar zai bar jikinsa.
sai da Boɗejo ta kai bakin ƙofa tukunna ta waigo tana ƙara cewa,"wai kuwa ba zaka taso ba?, ka san Allah in har wani mummunan abu ya sami Ilham sai nasa an ɗaureka".tayi ƙwafa tana bin su Hajiya Madina da wani kallo na ban haushi tace,"algungumai duk ku biyun da ba ku da aiki sai saka yaro agaba kuna kimtsa masa yanda zai bijirewa umarnin ubansa, yau zan gani sai dai ko ni ko ku acikin gidan nan muddin ba'ai abunda nake so ba, dan ya zama dole yau a saki waccan yarinyar, domin a yanzu dai Ilham ba zata zauna da ita ba har sai ta haife abinda ke cikinta, zan nuna muku na isa zan kuma nuna muku kaf a ƙasana ku ke, munafukai biyu masu son raba zumuncin ƴan'uwa, abokan sheɗ...".
ba ta ƙarasa ba Turaki ya dakatar da ita a fusace,"ya ishe ki Boɗejo, zan lamunci duk kalar rashin mutunci amma banda cin zarafin iyayena a gaban idona. haba don Allah don Annabi, duk kin bi kin hana kowa kwanciyar hankali akan wata banza yarinya can, idan tafi ƙarfin a wulaƙantata me yasa kika na ce aka aurawa wanda ba ya sonta ba kuma zai taɓa sonta ba".
bai san lokacin da ɓacin rai ya kaisa ɗaga ɗan yatsa ya na nuna ta da shi ba. "kina cin darajar kin kawo mahaifina duniya ne shiyasa nake ɗaga miki ƙafa akan irin cin kashin da kike yiwa Maama da Mum, darajarsa kike ci nake yi miki duk kalar wata biyayya da girmamawa, banda haka wallahi da comon inuwarsu aka ce ki yiwa kallon banza ba za kiyi ba, da tun na farko da kika yi ba za ki so ki ƙara na biyu ba. saboda haka yau ta zama rana ta ƙarshe da za ki ƙara ɗaga muryarki akansu in ba haka ba zanyi abunda ban taɓa yi ba".