*LULLUƁIN BIRI*
*35*
Fillo na rungume da matar har bayan wucewar wasu daƙiƙu sannan ta zare jikinta anata, ta ƙara saka idonta akan fuskar matar don tabbatar da abinda ta gani ɗin kar taje ko idonta ke mata gizo.
ai ko da ace bata taɓa ganin hotonta ba, tsananin kamannin da take da yaranta kaɗai ya shaida mata wannan itace matar da suka ɗauki shekaru ashirin da biyar basu ganta ba.ita ayanzu ma sai ta iya rantsewa hoton fuskar Turaki kawai ta-ke gani a fuskarta, ta kamo hannayenta tana daɗa kallo da suke sak da na Zaytuna tun daga kan tsayin yatsun har farcen, haka ma a sautin muryarta sai ka rantse kace Zaytuna ce tai magana, daga nan sai kuma ta sauke idonta akan sarƙar dake ɗaure da hannuwan nata.
taji hawaye ya kusa sakko mata tsaboda tsananin tausayi, tayi attempting kunce sarƙar sai taga ba zata iya ba.ji tayi matar ta ƙara ce mata,"dan Allah karki cutar da ni kema".
Fillo tai murmushin ƙarfin hali, taji tausayin kanta na bin iska yana tafiya, yayinda na matar ke biyo iska na lulluɓeta.
tace,"ba zan cutar da ke ba Mum, adu'a nake so kiyi mu fita daga wurin nan lafiya".Hajiya Ramla ta dinƙa kallon Fillo tana jin kamar wani ya taɓa kiranta da wannan sunan Mum.
Fillo tasa hannu a rigarta ta ɗauko wayar ɗazu, ta kunna sannan ta kalli Hajiya Ramla tace,"Mum za ki iya faɗin lambar Baffa ko ta Maama? sai mu kira su azo a tafi damu".
Mum tace,"su waye hakan?".
Fillo ta ɗago ido ta kalleta sannan tace,"lambar mijinki Alƙali Dikko ko ta abokiyar zamanki Hajiya Madina".Mum ta girgiza kanta tace,"ni ban san su ba ai, ban taɓa jin sunansu ba". sai kuma ta haɗe hannayenta tace,"idan kin san sune mutanen da suka saka ni a ɗakin duhu don Allah karki kira su, sun ce zasu yi tsafi da ni ne, kuma babu abinda nayi musu".
Fillo tasa hannu ta goge hawayenta, babu makawa ƙwaƙwalwarta tayi formating abubuwa da yawa, kuma ba lallai ta tuna komai ba ayanzu ƙila sai ta gani da idonta.
a lokacin suka ƙara jin harbin bindiga, cikin azama Fillo ta miƙe ta kamo hannunta a rikice tana cewa,"Mum zo mu gudu kar su kama mu".Hajiya Ramla ta miƙe da ƙyar suka nausa inda basu san ina zasu ɓulle ba suna ta zabga gudu, da sun gaji sai su tsaya su huta, sannan suci gaba da gudun, gaba ɗayansu a galabaice suke.
*A dai-dai wannan lokacin.*
Fulani Azima zaune a gaban boka dunƙus, idanuwanta na manne acikin ruwan ƙwaryar dake gabansa yana mata bayani, tana jin zuciyarta na tafarfasa saboda baƙin ciki."to ban san dai abinda hakan ke nufi ba, amma kwata-kwata ko aljani ɗaya ya kasa nuna mana fuskar yarinyar, amma tabbas dai aljanu sun shaida ita ke lalata miki aiki".
maganar ta ƙara ƙona ran Fulani Azima, ta ɗaga murya tana saka hannu ta toshe kunnenta tace,"wacece wannan?, wacece ita da har aljanu suka kasa gano min fuskarta?".
sai kuma tayi ƙasa da murya tana kallon Boka tace,"ni dai na roƙe ka da Aljani Jambus ka nuna min fuskar yarinyar nan ko kuma sunanta, nayi maka alƙawarin ko menene zan bayar ko da kuwa kaina ne".Boka yay dariya yace,"haba Azima, yanda muke da ke ai kin fi ƙarfin haka a wajena. abinda nake so ki fahimta shine yarinyar nan tafi ƙarfinmu saboda tana tare da tsari a jikinta".
sai yasa wani mifici ya rufe ƙwaryar sannan ya buɗe yace,"leƙo ki gani". ta leƙa kanta ta hango wata mace a tsaye doguwa siririya, amma baka ganin komai nata sai ɗan banzan duhu.yace,"to kinga ni babu ta yanda zamu ga fuskarta haka kuma sunanta ɓacewa yake akan aljanunmu".
fuskar Fulani Azima na shaida mamaki matuƙa tace,"to saboda me boka?".
sai yasa hannunsa acikin ruwan ya zuƙo hoton, daidai inda hannun Fillo yake yace,"ba lallai ke ki gani ba amma ni ina iya gani, wannan azurfar ta yatsanta azurfa ce ta tsari wadda ba zata taɓa barin wani aljani ya ganta ba balle har ya sami damar shigarta, bayan haka kuma ɗan autan aljanu ya faɗa min cewa yarinyar na kasancewa kullum cikin yin adu'oin tsari, bata minti ɗaya bata ambaci sunan Allah ba haka kuma bata min ɗaya bata ambaci adu'ar neman tsari ba. saboda haka babu yanda zamu yi da ita gaskiya, kuma shugaban Aljanu ya shaida mana muddin yarinyar na tare da Turaki babu abinda asirinmu ya isa yayi masa, domin ita ɗin kamar sila ce ta kariya a tare da shi".