*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_not edited._
*28*
washegari da safe Fillo ta gama shiryawa kenan sai ga Yami ta faɗo ɗakin kamar an jefota. fuskarta a haɗe take kallon Fillo, ita kuma tana ganin hakan tasha jinin jikinta.
Yami ta miƙa mata wayar hannunta tana faɗin,"ungo nan, idan ta kama ki tafi da ita can, abu ɗaya kawai na sani shine ki tabbatar kin ɗaga kiran Amir kunyi magana da shi, ki kuma basa damar zuwa idan ya buƙaci hakan".idon Fillo suka ƙanƙance tana kallon Yami da ta ɓata rai, ƙirjinta taji yana bugawa da sauri sauri domin bata tunanin zata iya bin umarnin Yami.
Yami ta doka mata tsawa,"kin karɓa ko saina hamɓare ki". tuni jikinta ya hau kyarma tayi sauri ta karɓi wayar tana duƙawa a wurin ta fashe da kuka.Kaka tace,"to dama ni dai da naga ba kiyi magana ba yasa nayi shiru, zatona ko baki san komai ba".
Yami tace,"ai ina sane, na zuba mata ido ne naga iyakar gudun ruwanta. sai naga rashin hankalin nata da gaske ne, to banda ma dai ɗan Adam butulu ne dan ubanki ina ke ina juyawa Amir baya, duk abinda Amir zai yi miki a rayuwa ai ke me iya shanyewa ce ba wai kiyi zuciya da shi ba, wane irin alkhairi ne yaron nan bai yi miki ba, wane kalar halacci ne bai yi miki ba, ke inda baya sonki da gaskiya har yace yaji ya gani ya aminta zai aureki sanda ake hure masa kunne da cewar ke ƴar gaba da fatiha ce. amma saboda toshewar basira irin taki har ki iya ɗaukar fushi da shi na tsawon wata da watanni, gaskiya kin bani kunya da mamaki".
cike da takaici Yami ta ƙarasa maganar.Fillo dai kuka kawai take yi tana jin zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta, ita ake bawa laifi?. gaskiya ko Yami da Kaka zasu haɗu su kasheta bata jin zata iya yin abinda suke so akan Amir, in har dan ta ɗaga kiran Amir ne ko ta basa damar zuwa gwara ta mutu, dan ko kaɗan bata son jinsa balle ganinsa.
Kaka tace da ita,"ni dai ban taɓa tunanin a ɗan guntun ililimin da kika samu daga wurin Amir ba, ilimin da wanda ya haifeki ya kasa baki shi, zaki iya butulcewa Amir ba, ko da kuwa me zai yi miki, irin faɗi tashin da yaron nan ya dinƙa yi a game da rayuwarki ta inganta da kuma lafiyarki yafi ƙarfin wulaƙanwa daga gareki. amma babu komai iya abinda kika yi ma kin zubar min da mutuncina a idon iyayensa, na kuma gode, domin babu wanda zai yarda cewar bani na saka ki ba".Fillo na kuka sosai ta ɗago ta kalli Kaka tace,"shikenan ko mene ya faru sai a ɗora min laifin?, me yasa ba za'a tambaye ni abinda yayi min ba?".
Yami ta galla mata harara tace,"rufewa mutane baki, ba'a haƙuri ma'aikin Allah yay haƙuri?, ko kuma ba'a yafiya muke yiwa Allah laifi mu nemi yafiyarsa kuma ya yafe mana. to wallah tun muna shiri da juna ki sasanta tsakaninku a yau. nace masa yazo, dan haka ki tafi da wayar kwa haɗu da shi acan. mu ba mutanen banza bane da sai da aka tsayar da maganar aure tsakaninku sannan ki nuna mana ba haka ba, ƙarya kike yi kinyi kaɗan".Kaka tace,"ni dai kawai in har na isa dake to komai da ya faru tsakaninku ya wuce daga nan inda kike, in kuma ban isa dake ba zan gani. kuma insha'Allahu nima zan juya miki baya ata dalilin hakan, wallahi sai na nuna miki ban taɓa saninki ba, kallo wannan sai ya daina shiga tsakanina dake balle har ki samu ikon ci gaba da zama tare da ni".
jin furucin Kaka yasa Fillo ta dinƙa kallonta babu ko ƙifce, ji take ina ma ta haɗiyi zuciya ta mutu, anya ma Amir bai asirce mata Kaka ba?, ko da yake babban asirin da zakai wa mutane akan suƙi ganin bad side of you shine ka zama mutum na ƙwarai a idon duniya. ta tashi ba tare da tace komai ba tai fuuu ta fice daga ɗakin tana ƙara sakin kuka.
a ƙofar ɗakin taga Maijidda a tsaye tana hawaye, tai mata kallo ɗaya ta ɗauke kai tayi gaba abinta, Maijidda tabi bayanta tana kiranta, Fillo ta juyo a fusace tace da ita,"da kika iya zuwa kika faɗawa Yami na butulce masa why can't you ki faɗa mata shi irin wulaƙancin da yay min, why not ki faɗa mata ya kira ni da ƴar zina ko sa nuna masa kuskurensa, amma sai kika karesa kika bar laifin akaina ni ɗaya. babu komai, thank you for that, ko yanzu kin nuna min matsayina wurinki, kin nuna min ni ɗaya zan iya fighting akanki ba dai ke kiyi akaina ba".