*LULLUƁIN BIRI*
*47*
kirayen sallar asuba ya farkar da Fillo da ga bacci, ta buɗe idanuwanta a hankali, tana miƙewa zaune aka ɗauke wuta, babu shiri ta koma ta ƙara dunƙelewa, har sai da taji masallaci na sallamewa da ga sallah tukunna ta ƙara buɗe fuskarta tana leƙowa, farko duhu ta gani sai kuma ta ga haske ya gauraye ɗakin.da ƙyar ta iya sakkowa kamar me tsoron taka tiles ɗin, alwalar ma kanta ɗaiɗai ta yi saboda tsoron toilet ɗin, ta fito ta isa kan dardumar da ta bari a shimfiɗe tun sallar daren da tayi.
zata tayar da sallah taji kamar an buɗe gate, jikin windo ɗin ta isa ta ɗa ga labulen tana hangen bakin gate da mai gadi ke mayar da ƙofa ya rufe, kafin idonta ya manne akan Turaki da yake tafiya zuwa in da taga ya nufa jiya wanda ta tabbatar nan ne part ɗin Ilham, dubai jallabiya ce a jikinsa dark blue, sai carbi da yake hannunsa yana ja, a yanzu ma da ya zuge glass door sai taji kamar ya datse da zuciyarta, idonta ya ciko da ruwan hawaye sai dai ba ta basu damar zubowa ba, a hankali ta din ga bin tazarar da ke tsakanin part ɗin na su, cikin kanta tana jin kamar ƙwaƙwalwarta na couting ma ta nisan interval ɗin da ke tsakanin part ɗin na su, tazara ce sosai amma sai take ganin kamar tazarar daidai take da tazarar yatsun hannunta.jikinta taji gaba ɗaya ya saɓule, ta koma kan sallayar ta tayar da sallah, ta jima tana jero adu'oi a san da ta idar, haka kawai taji zuciyarta na raya ma ta kamar Turaki zai mayar da aurensu, ta yi saurin girgiza kanta, it can never be possible ta san da hakan, yanda ya ke da muguwar zuciya ta sani ko da wuri ɗaya zasu ke kwana su na tashi ba zai taɓa mai da auren ba, kuma itama ba ta jin ko da ya mayar da auren za ta yar da ta zauna da shi, ai yanzun ma zama kawai take yi da zarar ta gama iddah zata bar masa gidansa, bari kuwa na har gaban abada.
ka sa ta shi ta yi ta koma kan gadon, kawai sai ta kwanta nan kan darduma jikinta tana jin duk yana yi ma ta ciwo, hawayen da take ta danne zubarsu taji sun gangaro, muryar Ummi kawai take son ji, ita kawai take son gani.
cikin kanta taji na karanta ma ta yanzu ita ɗaya zata yi ta zama haka kamar mayya?, to ai ko wannan bedroom ɗin ya yi ma ta girma da zama ita ɗaya balle wawakeken part ɗin na ta da taji ana ta faɗarsa tun a jiya da su Arɗo su ka dawo daga jere, anya kuwa zata iya ci gaba da wannan zaman da zuciyarta ta tsara ma ta?, ba zata falllasa komai ba kuwa?, kamar fa hauka ne take yi hakan!, ita abin da ba ta so shi ne ƴar ƙaramarta da ita ace wai tana zaman iddah a gidansu, to wanne irin kallo za'a koma yi ma ta?, wanne kalar tunani za su koma yiwa silar rabuwar auren?.sai kawai taji kuka ya taho ma ta sosai, tasa hannu ta toshe bakin kamar akwai wanda ya ke kusa da ita ba ta so ya ji, ita dai ba zata iya wannan zaman ba, gwara ta yi tafiyarta kawai, ko kuma ta kira Ummi ta faɗa ma ta a kawo Sumayya ta tayata zama, Sumayya ƙanwarta ƴar matar Hayyo da har ya mutu da ita ɗaya ce ba su rabu ba, ko kuma ta cewa Maijidda ta dawo nan ɗin?, to ai in har ta faɗawa Maijidda kamar ta kai takardar sakinta ne gaban Dada.
da waɗannan lissafin tunanin bacci ya ɗauketa, ƙarfe takwas yunwa ta farkar da ita, hasken ranar da ya ratso ta windon ɗakin yasa hankalinta kwanciya, tsoron ya bar jikinta.
tana ta shi ta gyara kan gado, sannan ta shiga toilet tayi wanka, ta daɗe a toilet ɗin kafin ta fito, ɗaya da ga cikin lotions da aka jere ma ta akan dressing mirror ta ɗauka ta shafa, ta shafa farar powder tasa lip balm, sannan ta saka abaya baƙa, ramar da ta yi sai ta ƙara yin kyau sosai acikin kayan.tana sakkowa downstairs sai ta shiga laluben ƙofar kitchen, ƙofofi uku duk sai da ta buɗe, kuma dukansu bedroom ne sai 1 parlo wanda yake shi ne a middle, cikin sanyin jiki ta rufo ƙofar, kenan ita babu kitchen a part ɗin ta?, haɗe musu yay kenan su yi shairing guda ɗaya?, kenan duk wannan uban kayan kitchen ɗin da taga an siya su na can an haɗe su tare da na Ilham?, abun da ake nufi har in zata ci abinci sai taje part ɗin Ilham sannan zata dafa?, ashe kuwa an so yunwa ta kasheta, dan wallahi in har dan sai taje part ɗin Ilham ne zata dafa abin da zata ci, to gwara tayi ta zama a haka har yunwar ta gaji da damƙarta ta kasheta.