21

98 9 1
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

*21*
Maijidda ce ta wuce da ledar kayan, Fillo na faɗa mata karta soma ta ambaci sunanta idan Kaka ta nemi ba'asin karɓan kayan Dr Yusuf. ai tasan an hanasu shine yana miƙowa ta amshe.
Maijidda na ɗan jin tsoro tace,"to ni ai nai zaton da gaske alluran ne shiyasa na karɓa".

Fillo na dariya tace,"kinga ke dai kije kisha faɗanki ke ɗaya, ni na tafi aiki. da nasha faɗan Kaka gwara na sha na Hajiya Madina".
tana faɗa ta ƙara saurin tafiyarta tana taiwa Maijidda dariya, ita kuma nata jin shakkar shiga da kayan, ji take kamar ta koma taga idan Dr Yusuf bai tafi ba ta basa kayansa, to amma tasan zuwa yanzu ya tafi kam, dan ko ɓata lokacin da suka yi a wurin duba kayan tasan yaje inda zai je.

tun shigowarsu gate Fillo ta dage sai sun wuce inda ake zubar da bolar gidan sun zubar da maganun, wanda zatonsu abinda ya faɗa hakan yake. kuma sai da suka je zasu zubar ne suka tsaya suna kallon uban kayan da mamaki.
leda ɗaya tulin kayan ƙwalama ne kamar hauka, madara, snacks da choculates da lemukan kwali, tarkace dai iri-iri. sai ɗayan ledan kuma kayan makeup ne aciki, shower gel manyan roba guda biyu wanda mutum sai yafi wata yana wanka da roba, sai lotions da su powder, duka dai dangin kayan kwalliya, kuma da gani kuɗi ne ba na wasa ba aka kashe wajen sayayyar.

Fillo ta shiga parlon da sallama tana tafiya a hankali, kanta a ƙasa sai jan yatsun hannunta take yi, Hajiya Madina na zaune akan kujera, ƙafafunta duka biyu akan tum-tum, Sameer na zaune a gaban ƙafafun nata ya tankwashe ƙafa yana yanke mata farcen ƙafarta. sai Nihal dake ɗaya kujeran a zaune tana duba wata handout, daga dining area kuma Zaytuna ce a zaune tana danna waya.
Fillo ta ƙarasa ta durƙusa a gefen kujera tana gaida Hajiya Madina. Hajiya Madina ta ɗauke idonta daga karanta story book ɗin da take yi ta kalli Fillo tana amsa gaisuwar tata.

"Halimatu anji sauƙi kenan". tace,"ehh Maama na wartsake gaba ɗaya". "to masha'Allahu, Allah ƙara miki lafiya. kina da ƙwarin dai da zaki iya aiki ko?". Fillo tace,"ehh Maama".
Hajiya Madina ta gyaɗa kanta, tai shiru for some seconds sannan tace. "to jiya an kawo miki ƴar'uwa da zaku ke aikin tare, ta kammala komai tun ɗazu, yanzu sai ki tashi kije lesson teacher ɗin ku yazo, idan kuka kammala ke sai kiyi aikin rana".

wani daɗi ya mamaye Fillo, ko babu komai burinta na yin karatun boko zai cika, abunda mahaifinsu ya kasa yi musu yau wasu bayin Allah zasu mata shi. tunaninta ya tafi can wani lokaci baya, tana wannan tunanin taji Hajiya Madina na ƙara cewa,"dan Allah ku mayar da hankali kunji ko, abunda za'a muku a makaranta shi zai muku, kuɗi masu yawa aka biyasa, akwai percentage ɗin da za'a ke cirewa a cikin kuɗin aikinku, so idan kun mayar da hankali akan karatun kanku kuka taimaka, idan kuma kunƙi kunwa kanku asara babba".

Fillo tace,"insha'Allahu Mama zamu mayar da hankali, insha'Allah ba zan baku kunya ba zanyi abinda kuke so nayi". Hajiya Madina ta jinjina kanta. a lokacin sabuwar maid ɗin da aka kawo ta iso wurin ta tsuguna kusa da inda Fillo take. tace,"Hajiya gani".
Maama tace,"yauwa ga ƴar'uwar aikin naki nan. ki bata nata reading materials ɗin da Zaytuna ta baki ɗazu, sai kuyi maza ku wuce me karatun na can na jiranku, awa biyu zaku dinƙa yi, da zarar kun kammala ku yo cikin gida, a kama kai bana son shashashancin banza if not zan sallami yarinya".
duka su biyun suka amsa da,"to". sannan Fillo tace,"aina zamu sami Malamin?".

Nihal tace,"ku tashi muje let me escort you". ta faɗa tana gyara zaman glasses ɗinta, da gyara dogon wandon dake jikinta.
"je ki ɗauko littafan naku". ta faɗa tana nuna Ɗausiyya ɗaya ƴar aikin. da ganinta tana da hanzari akan yin abu, dan cikin sauri ta ɗauko ta dawo, kuma kallo ɗaya zaka mata zaka san she is typical ƴar ƙauye, balle kuma ka kai ka ga kallon the way take abubuwanta, maganarta duka hi da ha ne, jiya ana kawota Hajiya Madina tasa Baba Jummai dake kawo mata ƴan aiki ta kaita saloon aka wanko dattin kanta, kuma suna dawowa tasa tai wanka me kyau da dettol da turaren ƙamshi. haka Hajiya Madina take, bata nuna ƙyama ko ƙyanƙyami ga duk yaran da ake kawo mata, karɓarsu take ta nuna musu hanyar gyara kawai.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now