*LULLUƁIN BIRI*
*53*
*Azima Tahir Lukman.*
ashekarun baya masu yawa da suka shuɗe, Azima Tahir Lukman wata matashiyar budurwa ce, wacce ke matuƙar ji da kanta a ɓangaren kyau, ilimi da kuma dukiya ta mahaifiyarta wadda ta kasance ƴar siyasa.
kyau irin na Azima ke tasirantuwa a zuciyoyin maza da dama, daga masu kuɗin har talakawa, a inda ta ware manyan masu kuɗi da masu mulki waɗanda su ne take ganin su kaɗai ne suka isa su mallaketa.
kuma a kaf mazan da tayi mu'amala da su babu guda ɗaya aciki da zuciyarta ke jin tana so ko kuma zata iya aurensa, no; zata mu'amalanceka ne kawai domin kuɗin da suke aljihunka, da zarar ta gama da kai shikenan, saboda ta mallaki kuɗi a wurin irin alahazawan da ke zuwa wurinta ta kashe rai ba ɗaya ba, ba biyu ba.zuciyar Azima ta so mutum guda tallin tal ne a rayuwarta, wato Alƙali Habib Dikko, shi kaɗai zuciyarta ta so tsakani da Allah, wanda har take jin she can go to the extend akan taga ta mallake shi, alhalin kuma yana matsayin saurayi ne na aminiyarta da ta san cewa an saka musu rana.
Ramla Muhammad Turaki itace babbar aminiyarta da suka yi university tare anan london, duk wanda yasan Azima ya san Ramla, haka duk wanda ya san Ramla yasan Azima, su kwana tare su tashi tare, su ci abinci tare su yi yawo tare, haka zalika ba sa taɓa aiwatar da abu sai da shawarar juna.Azima ta samu Ramla ne tare da Dikko, tare ta gansu, wanda shi ma kuma ya aminta da ita sosai, musamman da yaga Ramla ta ɗauki duk wata yarda da amana ta bawa Azima.
sai dai daga lokacin da Dikko ya fara shirin kai lefen Ramla, a lokacin Azima ta fara kunno wutar gobarar da zata lalata lamarin auren, ta fara ɓata Ramla a wurinsa, abubuwa iri iri da zai sa yaji ya tsani Ramla babu wanda ba ta faɗa masa ba, tun baya yarda har ya zo ya fara yarda da ita, saboda sauyin da yake gani a tare da Ramla a lokacin da bata ba shi attension ɗinta, sakamakon final exams da za su fara.hatta vedion tsiraici na lesbian Azima ta ɗauka ta bayar anyi editing ɗinsa da fuskar Ramla ta bawa Dikko, daga wannan lokacin kuma yaji ya tsani Ramla kwatakwata, ita kuwa Ramla a lokacin bata kawo komai a ranta ba dangane da watsi da lamarinta da Dikko yay, ta ta'allaƙa hakan ne da space ya bata saboda ta samu tayi karatun exams sosai.
sai dai kuma a lokacin da Azima take tunanin tayi nasara, a lokacin Allah ya toni asirinta a ranar wata laraba, inda wanda yay ma ta editing vedion tsiraicin Ramla yaje ya sami Dikko ya faɗa masa gaskiyar komai, a lokacin soyayya ta riga tayi nisa tsakanin Dikko da Azima, dan saura ƙiris su shigar da iyaye cikin maganar, dan Azima ta gama tsara yacca zata shimfiɗar rayuwar aurenta da shi.
kuma duk wannan lamari da ke faruwa Ramla bata da labarin komai, yacca Azima ba ta bari ta fahimci wani abu ta ɓangarenta ba, haka shi ma Dikko bai taɓa tunkarar Ramla da irin abubuwan da Azima tayi akanta ba har kawo iyau da take matarsa, uwar gidansa, kuma uwar ƴaƴansa, wucewar shekaru sama da 20.lissafi ɗaya Azima tayi a bayan da Dikko ya juya ma ta bayansa, shi ne ba zata taɓa yin nisa daga gare shi ba, zata bi wata hanyar da zata kusance shi har ta wanke laifinta, kuma har ya yafe ma ta yace zai aureta kamar dai yanda taci burin hakan.
dalilin da yasa ta shiga rayuwar Mai Martaba Hashim Latif kenan, saboda ta lissafa cewa ta wannan hanyar kaɗai zata iya samun damar kusantar Dikko, ta hakan ne ba zasu yi nisa da junansu ba, ta hakanne zata samu damar wanke laifinta gare shi, in ya so a sanda yace ya yafe mata sai tayi duk iyakar ƙoƙarin da zata yi ta raba aurenta da Mai Martaba domin ta mallaki Dikko, amma sai dai me!, lissafin da hasashenta duk sai ya tarwatse ya bi iskar da ta kaɗa tun a ranar da ta sanya ƙafafunta acikin gidan mai martaba.kuma daga lokacin da ta fahimci cewa ba zata taɓa samun Dikko ba, daga lokacin ta ɗauki alwashin ƙuntata rayuwar duk macen da ke rayuwa tare da Dikko hatta kuwa da ƴaƴan da zai haifa ba tare da ita ba.
shigowarta cikin rayuwar Mai Martaba ta gane asalin menene mulki da kuma daɗin da yake cikinsa, wannan yasa ta dasa cin burika da yawa a rayuwarta, lokacin shaiɗan ya fara buga ma ta sabuwar ganga acikin kanta, akan aikata mugwayen abubuwan da ba zasu ɓulle ma ta ba, ya dinƙa rinjayar zuciyarta da cewa tayi duk fafutukar da zata yi wajen ganin ta mallaki kaso 70 cikin tarin dukiyar Mai Martaba kafin ta barshi.