24

94 10 1
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

_Please avoid any mistake._

*24*
"nima da nake mahaifiyarta na manta da ita, na manta na taɓa haihuwar ƴa me kamarta ko sunanta, na jima da cireta a sahun ƴaƴana. saboda haka kaima ka manta cewar ita mahaifiyarka ce tunda har ta iya manta da cewar tana da ƴaƴa, ka riƙe wadda ubangiji ya dubeku ya tausaya muku ya baku ita ta maye gurbinta...Allah ne kaɗai yasan hikimarsa akan hakan, wataƙila ba zaku sami tarbiyya da soyayya daga wurin Ramla ba shiyasa ya ƙaddara faruwar wannan lamarin".

jin maganan Granny ɗin yasa Turaki buɗe idanuwansa, ya buɗe su a daidai lokacin da Hajiya Madina ke shigowa ɗakin. kallo ɗaya yayi mata yaji tsananin tausayinta ya kamasa, ya ƙara jin ƙaunar matar a ransa, haka ne, basu sami soyayyar mahaifiyarsu ba, kuma basu samu tarbiyya daga wurinta ba, amma Allah ya basu wacce tayi musu dukkan waɗannan gatan, wanda iyakacin abinda wadda ta haifesu zata musu kenan.

hijab ɗin dake jikinta fuskarsa ma a karkace ta saka, ya bita da kallo har sanda ya sauke ƙwayar idonsa kan bayan hannunta. tabon ƙonuwar da tayi tsawon shekaru 25 har yanzu yanan bai ɓace gaba ɗaya ba, sai kawai yasa hannu ya goge hawayen da ya sakko masa a lokacin da bai sani ba, idan bai so Maama ba wa zai so?, idan bai ƙauna ce ta ba wa zai nunawa ƙauna?, idan bai kula da ita wa zai bawa kulawarsa?, wataran har yana jin yafi sonta fiye da wadda ta kawosa duniya, har yana jin tausayinta fiye da yanda yake tausayin Mum ɗinsa.

Hajiya Madina ta ƙaraso bakin gadon, Granny na amsa sallamarta, jikinta duk a sanyaye taja kujera ta zauna, ta dubi Turaki da muryanta da yay ƙasa tace,"sannu me Babban suna". ya amsa da,"yauwa Maama, thank you so much for your care".

ganin yanda ta ƙura masa ido sai ya sauke idonsa ƙasa, yana jin nauyinta na shigarsa, ya sani yayi mata laifi. laifi har guda biyu a rana ɗaya, ya saɓa umarninta na cewa duk inda zai ke tafiya yanzu suke tafiya tare da Khalil, sannan yazo yasa kansa a situation ɗin da ya shiga, saboda wannan condition ɗin da yake shiga ne a duk sanda ya shiga ɗakin mahaifiyarsa shi yasa ba'a so ya shige shi, yasa ma aka rufe ɗakin gaba ɗaya Baffa ya ɓoye key ɗin, ya gargaɗe shi da ko da wasa kar ya ƙara tunkarar ɗakin, tunda duk sanda ya shiga yana tunawa da komai da ya faru a ranar da Mum ta tafi ta barsu, sai ya dinƙa jin komai tamkar a lokacin yake faruwa, sai ya dinƙa ganin yacca wuta ta ke tashi da yanda ya dinga kuka Zaytuna ma tana yi, sai yake jin kukan a cikin kansa.

hakan sai yasa yake jin wani irin raɗaɗi, ya dinƙa jin wani irin abu a tare da shi da ba zai iya kwatantasa ba a yayin da yaga hotonta. idan yana ganin hotonta sai yaji kamar ya cirota daga cikin hoton ta zama a zahirance, yay mata kallo na zahiri sai ya rungumeta ta yanda ɗumin jikinta zai ratsa shi, taci gaba da rayuwa tare da su ko da ace ba zata so su ba, shi dai kawai ya dinga ganinta yana jin daɗi, yake yi mata duk wata kalar biyayya, ya kuma nuna mata zallar soyayyarsa, irin wannan soyayyar da ta ke only between child and his mother.

alƙawarinsa ne daga zarar da ya sami job ba zai dinga barinta tana zuwa office ba, ta gama yiwa gwamnati aiki, shi zai dinƙa biyanta da kuɗin da yafi wanda take samu ba tare da tayi aikin ko da rubutu a takarda ba, alƙawarinsa ne zai nema mata wacce zata dinga kasancewa tare da ita idan baya kusa da ita, zai nema mata yarinya kamilalliya kuma kimtsatstsiya, irin yarinyar da ta san darajar uwa, irin wacce tasan kalar soyayya da kulawar da ya dace a nunawa uwa, irin wacca yasan ko da a bayan idonsa ba shi da haufin ba zata bari ko da ƙuda ya taɓa mahaifiyarsa ba.

ya ƙara ɗago kai yana kallon Hajiya Madina, wacca a yanzu tayi ƙasa da kanta tana goge hawaye. sai ya rumtse ido sosai yana jin wani ɗaci a zuciyarsa. a hankali yace,"dan Allah Maama ki daina kuka a gabana, bana so, yana ɗaga min hankali...kiyi haƙuri ji nayi kamar idan na shiga room ɗin Mum zan ganta, naji ne kamar tana kirana a lokacin, dalilin da yasa na buɗe kenan...kuma dana shiga sai ban ganta ba, ban ganta ba ko da inuwarta sai hotonta".

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now