*LULLUƁIN BIRI*
*46*
*Taraba.*acikin gidan babu abin da kake ji yana tashi sai hayaniyar mutane masu hadadar biki.
Inna Kareema ta fito daga sashin Kawu Abdullahi hannunta ɗauke da ƙatuwar cooler na abinci, tana nufar sashin Jagarɗo suka yi kiciɓis da baƙuwar da ke shigowa.
ta tsaya da tafiyar fuskarta na washewa da tsurar fara'a, ta ajiye kular a ƙasa tana faɗin,"maraba maraba da mutanen Abuja, wato ku sai yau ku ke tafe?".
ta faɗa tana ƙarasawa ta tarota tare da amsar ƙatuwar jakar hannunta.Dattijuwar baƙa me suna Yaya Sahura ta ce,"yo ke Kareema ai wannan biki da sai an gama za ku ganmu".
Inna Kareema ta ce,"kai haba dai, lafiya?".
Yaya Sahura tace,"ƙalau, ai mu zatonmu litinin ta sama aka ce za'a kawo lefe, taron biki kuma a fara shi ranar laraba, sai daren jiya da Lamiɗo ya kira waya yake cewa da Baban Yara ai bai ga gimlawarmu ba, shi ne yaufa babu shiri muka bugo sammako".
Inna Kareema ta ɗauki kular abinci suka ci gaba da tafiya tana faɗa ma ta,"to ai kin san auren a yanda yazo, shi Dottijo ma ce ya yi mene na cewa sai anyi wani taron biki tun da dai ɗaurin aure an jima da yinsa, akai yarinya ɗakinta kawai, to kuma kin san lamarin Dada. ita taron ma ce tayi sai anyi sati guda ta yanda Kakar mijin zata gane su ne ƴan iska, da ƙyar Dottijo ya shawo kanta yanzu dai za'a yi shi kwana biyu, to jiya anyi Kamu, yau zamu yi al'adarmu ta fulani da kika sa ni, sai gobe kuma a kaita gidanta".
Yaya Sahura tana dariya suka wuce suna ci gaba da tattaunawar su. "hmmm ai da yake Kakar mijin duk ita taso ta ɓata lamarin, karki ga irin tataɓarzar da aka sha kamin Dada ta yarda amma da tsaye tayi tace ko zai mutu sai ya sakar ma ta jika, da ƙyar su Dottijo dai suka shawo kanta ta haƙura".
a parlon Hajjah suka ya da zango in da babu kowa, Yaya Sahura ta zaro ido waje tana faɗin,"wannan uban akwatunan fa kamar za'a buɗe sabon kanti, kar dai kice min su ne lefen?".
Inna Kareema ta wuce ta ajiye kular hannunta tana faɗin,"hhh aiko dai abin da kowa ke faɗa kenan, Fillo dai ai abun nata sai son barka, ƴa tayi goshi dan kaf jikokin gidan nan albarka, banda haka da yanzu Dada taja ma ta tayi asarar wannan abun arziƙin".
"masha'Allahu, kiga akwatuna kamar ba'a rashin kuɗi a ƙasar nan, kalla fa yacca aka ɗaure su da ribom kyace lefen da ake kaiwa gidan sarki ko gidan shugaban ƙasa".
Yaya Sahura ta faɗa tana tattaɓa akwatunan da aka jere su waje ɗaya ɗaiɗai har guda ashirin da takwas.
Inna Kareema ta wuce ta rufe ƙofa, ta dawo tana cewa,"ai buɗe su duk ki gani, gwala-gwalai ne aciki har takwas. lefen nan dai in faɗa miki tun ranar farko ba'a ƙara buɗe su ba kin san ba zuciyar kowa ke da kyau ba, masu ɗan hali ba'a gane musu, zan rantse miki kaf kayan ciki babu na ƙasar nan. kin gansu nan kuma Dada ta ce ko kwalli ba za'a taɓa ba".su kai dariya tare, sannan su ka shiga buɗe akwatunan na gani na faɗa, Yaya Sahura sai saka albarka take tana yabawa.
daga can ɗakin Dada kuwa waya ce maƙale a kunnenta, magana take yi cikin faɗa tana cewa,"ka ga Arɗo ni bana son wannan magana, su kwashe kayansu kawai, duk wani kaya da suka zuba a kwashe su akai musu gidan su ba ma neman taimakon kowa don muna da shi, haka kawai salon yarinya ta tare azo ana goranta ma ta ana cewa ai kayan ɗakin nata ma iyayen miji ne suka yi ma ta, a'a sam ku kwashe musu kayansu ku jera na ku".da ga cikin wayar Arɗo yace,"to Dada wallahi duk mun rasa yanda zamu yi da su fa, ita mahaifiyar yaron ta ce gudunmawarta ne, Fillo ai ƴace a wurinta...".
tayi hanzarin katse shi a yayin da ta kulle ido tana girgiza kai,"Arɗo akwai ka da shegen taurin kai, ka faɗa musu gudunmawa bama so ta bawa ƴarta, ni jikata bata buƙata".
Arɗo yace,"tom shikenan Dada yanda kika ce".
ta sa ke cewa,"yanzu an kammala kawo kayan gaba ɗaya?".