*LULLUƁIN BIRI*
*48*
"Daughter nah". Hajiya Madina ta kirata da sabon sunan da ta raɗa ma ta tun a ranar da aka kawo musu ita."na'am Maama".
with much care Maama ta ce mata,"ya jikin naki?, da sauƙi ko kuwa?, kina shan magani?, yanzu ya kike ji?, mene yake ya damunki?".waɗannann tarin tambayoyin yasa ta kallon Turaki ta gefen ido, idonsa na kan ɗaya wayar da ke hannunsa, fuskarsa kamar baƙin hadarin da ya haɗo, ta rufe ido ta ce,"Maama lafiyata lau, shi ne kawai yace miki ban da lafiya". ta faɗa kamar zata sa kuka.
furucin nata yasa Hajiya Madina murmushi, ko ba komai ta san da gaske jikin nata da sauƙi kamar yan da yace, ta furta alhamdullahi sannan ta ƙara cewa,"kina cin abinci sosai ko?".
ta ce,"ina ci".
"to Allah ya ba ki lafiya Daughter, Allah ya sa kaffara, ki daure ki dinƙa shan magani kinji, becx bana so na ji wani abu yana taɓa min ke, zan zo anjima na duba ku, Allah ya yi muku albarka".a hankali Fillo ta ce,"Maama Ummina fa?". ta faɗa muryarta na ɓallewa da kuka.
zaton Hajiya Madina ko tana so ta ganta hakan yasa tace mata,"za ki je kiga Ummin ki very soon, ni da kaina ma zan kai ki".
kamar ta faɗawa Maama komai sai kuma tayi shiru, ita tambayar da tayi saboda Maama ta ce zata haɗa su a waya ne, in yaso sai tace da Ummi azo a ɗauketa dan ba ta fatan ta ƙara kwana acikin gidan da ba zaman aure take yi ba.
ta sauke wayar da ga kunnenta bayan Hajiya Madina ta kashe, ta waiga tana kallon Turaki ta ce,"ka ba ni lambar Kaka ko Ummi please".
maganar tata sai ya zama tamkar da dutse tayi, yay banza da ita ban da ma waya da ya kara a kunnensa yana amsa sallama, bata ɗauke idonta akansa ba taci gaba da kallonsa, hotunan kasadar da ta dinƙa yi wurin ceto rayuwarsa yana haska mata a ido, sai a yanzu ne ta yarda da cewa ɗan adam butulu ne, ita ba wai don ya saketa ba, a'a irin wulaƙanci ma da yake mata na nuna da ita da banza da wofi ɗaya, kuma ƙila duk yana mata haka ne saboda sanin mahaifinta da yay, da ma sai da ta faɗawa Ummi cewa wallahi bai aureta ba saboda abubuwan da ya faɗa sai don ya wulaƙantata, a lokacin Ummin ba ta yarda da ita ba hasalima faɗa suka haɗu suka dinƙa yi ma ta ita da Kaka, but yanzu ta san dole za su yarda da abin da ta ce, kuma ko ba komai ta san Turaki zai ga ishara akan aurenta da yay ba don komai ba sai domin ya tozartata.
maganar da yake yi a cikin wayar ta shiga kunnenta.
"no ba haka ba ne Faruq, bana fatan na ƙara maimaita kuskure, this time around ba zan yi gaban kaina ba, ba zan ƙara yiwa kaina aure ba sai da sanin iyayena, kai ba ma aure ba kawai, dukka wani abu na rayuwata, gaban kaina da nayi banji da daɗi ba, ni ɗaya na san halin da na shiga, but da na rabu da kowacce yanzu komai ya zamar min normal, ina cikin farin ciki da kwanciyar hankali"._na rabu da kowacce._ kalmar ta maimaitu a cikin kan Fillo, kenan har Ilham ma ya rabu da ita?, ita kuma me tayi masa?, wai wanne irin mutum ne shi ɗin?, kenan shi ma yana sahun mazan da basa mutunta aure, burinsu su aura su saka?.
ta yiwa kanta tambayar da zuciyarta ke ba ta amsa, tunaninta ya tsaya cak san da taji yana cewa,"sunanta Aisha ƴar sarkin kano ce, insha'Allahu gobe nake so naje na gana da iyayenta, zan fara neman izininsu before na kai maganar gaban su Baffa, ita ba ni da matsala da ita becx ita ta fara cewa tana so na, so pray for me kar na sami matsala da Baffa, dan nima ina son yarinyar sosai...".cak maganarsa ta katse dalilin ƙarar fashewar abu da yaji, yay saurin ɗago ido yana kallon wurin da Fillo ke tsaye tana ƙoƙarin saka hijab, sai kuma idonsa ya kai kan wayarsa da ta tawarwatse a ƙasa, ta yi ragaga tamkar tayar mota ce ta bi ta kanta.
bai san lokacin da ya miƙe ba yana bin ƙasan tiles ɗin da kallo, yana kallon kowanne pieces na glass ɗin wayar da ya barbaje.