*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya**20*
bayan sati ɗaya jikin Fillo ya ƙara yin sauƙi sosai, yarinyar har wani fresh tayi hasken fatarta ya ƙara fitowa saboda kwanciyar da tayi a asibiti me kyau, da kuma irin cimar da take ci me rai da lafiya. na musamman Hajiya Madina ke yin lafiyayyan girki a kai mata, girkin da zai ji ganyayyaki masu ƙara lafiyar jiki da kuma hanta acikinsa, tunda aka kwantar da ita duk wani abinci da zata kai baki da hanta take yin lomarsa, fruite salad kam da bata taɓa shansa ba sai da ya ginsheta. kuma tunda suka dawo bata ci gaba da zuwa aiki ba sai Kaka ce ke yi, Hajiya Madina tace ta ƙara samun hutawa na sati ɗaya sannan sai taci gaba, har wannan lokacin kuma bata san Turaki ne ya kaɗeta ba, duk zuwan da yake yi akai akai zatonta halin karamci ne kawai irin nasu.sa fiya ce yanzu dan ko takwas da rabi bata yi ba, Kaka na daga falo tana sauraren Shaik Ibrahim Daurawa a radio, Fillo kuma na ɗaki tana shiryawa.
Kaka tace,"wai ba zaki fito ki wuce ba ne?, kullum sai kin ɓatawa bawan Allah lokaci Fillo, Allah raina yana ɓaci da wannan abin naki".
daga inda Fillo take ta ɗan gwame fuska tace,"Kaka fuskar hijab ɗin ce fa ta yage shine nake ɗinkewa". Kaka tace,"uhm haka dai kike kullum da uzurin da zaki bayar, to ki bar ganin saurayinki ne Allah sai nace ya fara yi miki bulalar makara, wataƙila ki fi maida hankali akan karatun".dariya kawai Fillo tai bata ce komai ba, amma har hangowa take wai Amir zai daketa, tana sonsa dan haka ba zata ƙi tsayawa ba amma shi ɗin tasan ba zai taɓa iyawa ba, ko wani me gangancin yaga zai gwada sai iyakar inda ƙarfinsa ya ƙare.
ta fito daga ɗakin sanye da hijab ruwan toka, hannunta kuma tana riƙe ne da qur'ani izu sittin ta rungume shi a ƙirjinta haɗe da dardumar sallah.
"na tafi Kaka". Kaka ta ɗago ta kalleta tace,"Allah ya bada sa'a, amma ku gama da wuri kinga Hajiya Madina tace ki koma aikinki yau, kya gaida Amir ɗin kice ina daɗa masa godiya Allah ya jiƙan mahaifa". tace,"tom Kaka". da haka ta fice.daga can bakin gate wurin da ya saba zama ta gansa, a durƙushe a ƙasa da alama ya gaji da tsayuwa ne. bakinsa na motsi yana latsa counter dake saƙale a yatsansa, baƙin yadi ne a jikinsa mai taushi mara tsada wanda ya karɓi jikinsa sosai. ya kuma fito da kyawunsa na usulin bafulatani, sumar nan tasa kwantacciya ta fulani tai luff sai ƙyalli takeyi, da takalminsa da agogonsa dai-dai na me rufin asirin ubangiji.
tunda ya ɗaga ido yaga Fillo na tahowa zuwa gare shi kyakkyawan murmushi ya ɓalle a saman fuskarsa, zuciyarsa na ƙara cika da tausayi da soyayyar Halimatunsa, ruhinsa na ƙara buƙatuwa da ƙwaɗaituwar ta zama mallakinsa.a lokacin da ta iso wurin ta sakar masa nata sanyayyan murmushi da yake motsa zuciyarsa. ta durƙusa a gabansa ta gaishesa.
Ya amsa yana kasa ɗauke ido daga dogayen yatsunta da ta rufe fuskarta da su, murmushinsa na ƙara faɗaɗuwa. sai da yay gajeriyar ajiyar zuciya sannan yace,"Barka da fitowa gimbiyar Amir, sarauniyar da ta kafa fadarta acikin zuciyar Amir, kazalika uwar ƴaƴan Amir".ta ƙara rufe fuskar da hijab ɗinta, wani daɗi na ratsata. Yay ƴar dariya yana jin tana ƙara burge shi saboda wannan kunyartata.
yace,"duk da an hanani ganin fuskar hakan ba zai hana ni faɗin kinyi kyau sosai, matsalar guda ɗaya ce dai da bana so".
ya ƙarasa maganar amon muryarsa na sauyawa, tai saurin buɗe fuskarta, so take ta kallesa amma ta kasa, ta sauke idanuwanta a ƙasa da rashin jin daɗi tana jan yatsunta tace,"wacce irin matsala ce?, mecece matsalar da baka so?, a shirye nake da gyara ko menene saboda kai?".ya murmusa kuncinsa sannan yace,"Kunya! itace matsalar kuma itace bana so, amma a iyaka tsakaninmu banda wani daban, sai dai na san ba zaki iya dainawa ba balle ki rage, tunda ba tun yau ba nake roƙon alfarmar a rageta ko ya ya ne saboda tana ƙwarata, amma kamar ma ba'a jin me nake cewa...ni kuma tsakani da Allah ina so ake a bani damar ganin cikin idanuwan gimbiya, ina sonsu, so me yawa ba kaɗan ba".