54

145 8 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*54*
akan kujera ya zaunar da ita, idanuwan Fillo suka manne akan hannun Turaki da suke cikin plate ɗin abincin da yayo takeaway, abincin da ta san ya siya ne saboda ita, ba don shi yaci ba.

ya ɗebo ya kai bakinta, har yanzu ɓacin ran da ke saman fuskarsa bai gushe ba, idanuwansu ya sarƙe ana juna, ta kaudar da hannun nasa da ke nufar bakinta.

"ban ji daɗin yanda ka yiwa Boɗejo ba".
ya rufe idonsa bai ce komai ba.
"don Allah kar ka ƙara, ko babu komai ita ce fa ta haifi Baffa, tana da girman da bai kamaci ai faɗa ma ta kowacce irin magana ba saboda ɓacin rai".

still idonsa na rufe ya ce,"ba don hukuncin ubangiji ba, sannan ba don ke da taimakonki ba, da yanzu bana raye, ko kuma da ban kawo yanzu da lafiyar da zan yi tafiya ba, da yanzu wataƙila ina kwance marabata da matacce numfashi kawai, kuma wataƙila da har yanzu ban ga mahaifiyata ba. saboda haka girmanki da nake gani yafi gaban tunani, kina da girman da ba zan iya ganin an ci mutunciki na ƙyale ba".

ta buɗe baki zata yi magana ya ɗora yatsansa a leɓenta,"shhhh bana son magana, ki ci abinci".
ta kalli abincin ta ce,"bana ci".
"saboda me?".
"saboda kaima ba zaka ci ba, me yasa zaka tsaya siyan abinci bayan na iya dafawa, and beside da ka siyo bafa ci zaka yi ba, so kake ka kwana da yunwa?, ban iya rashin adalci ba kuma ba zan fara ba daga yau, Ummi ta jaddada min sau babu adadi cewar kar na taɓa barinka da yunwa".
kafin yay magana ta miƙe, ta kamo nasa hannun shi ma ya miƙe.

"muje kitchen na dafa mana abin da zamu ci".
ya dakatar da ita,"kin gaji ba za ki iya girki ba, kuma kinga akwai ciwo a ƙafarki".
"ni ban gaji ba". ta faɗa tana saƙalo hannunta guda a wuyansa sannan ta ƙara cewa,"idan ƙafan na ciwo ai sai ka ɗauke ni".

murmushi yay tare da ɗaukarta su ka fita a ɗakin,  su na saukowa downstairs kitchen ya nufa, sai da suka shiga ya ajiyeta, ya kama ƙugu yana cewa,"zan ga yanda ake aiki da gurguwar ƙafa".
tayi murmushi me sauti tare da jan gemunsa ta ce,"to ai da ka ɗauko ni na warke".

ya buɗe ido yana kallonta,"ƙatoto da ni kika yiwa wayo?".
ita ma ta kama nata ƙugun ta ɗaga kai sama ta juya idanu, sannan ta ce,"me zamu ci?".
"duk abin da aka girka da waɗannan siraran hannun zan ci".
ta dafa kafaɗarsa ta ce,"ummm Maama ta taɓa cewa kana son soyayyan indomie, so yau zan ci abin da kake so ni kuma bana sonsa, but na san daga yau zan fara so, in dafa ko?".

ya ɗaga ma ta gira yana jin wani daɗi a zuciyarsa, ta wuce ta ɗora tukunya a gas, ya bi ta yana faɗin zai tayata, ta dakatar da shi,"no ba yanzu ba, zaka fara girki but not today not now, but one day. for now just sit and watch".

kujeran dining ɗin dake kitchen ya ɗauko ya zauna gefe daga in da cooker gas yake, kafin ta gama yankan albasa idonsa duk ya cika da ruwan hawaye saboda yajin albasar, tuni kuma suka zubo, sai ƙyafta idanu yake, Fillo duk na kallonsa tana ƴar dariya, tace,"me aka maka kake kuka?".
ta tambaya tana dariya ƙasa-ƙasa.

"ni kike yiwa dariya?".
ya miƙe zai bar kitchen ɗin ta maido shi ya zauna tana faɗin,"sorry, idan ka fita ina jin tsoro".

ya ƙanƙace idanu yana kallonta cikin tarin ruwan da ya cika idonsa,"Fulani Nah idona yaji".
"ni dai ka zauna haka, ina gama yankawa zai daina ai". ta faɗa tana narkar da murya, haka ya zauna babu yacca ya so, har sai da ta gama yankan albasa tukunna ta wanke masa fuska a sink.

wayarsa tayi ringing yana dubawa yaga Sameer ne, yay picking Sameer na faɗa masa ga shi ya kawo masa ticket ɗin.
ya kalli Fillo ya ce,"Fulani Nah zan amso saƙo wajen Sameer".
tayi shiru kamar bata ji shi ba har sai da ya ƙara kiran sunanta.
ta ɗan ɓata rai ta ce masa,"to ya shigo parlo ya jiraka mana, idan mun kammala sai mu same shi, ni ba zan iya jira idan ka fita ba, kafin ka dawo dodon kitchen ɗin ya cinye ni".

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now