40

199 14 6
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*40*
Zaytuna tayi matuƙar furgita da yanayin Turaki, hakan yasa ta riƙe Fillo da kyau ta jata su kai baya da shi saboda yacca yake faman uban huci kamar mayunwacin zaki.

ta shiga kaɗa masa kai tana kallonsa tace,"Hammah dan Allah kawai ka kawo ƙarshen komai a yau ko zuciyarka ma ta huta, ita mene laifinta?, ita me ta sani?, bafa ta san komai ba".

ta faɗa ita kanta tana jin tsoronsa saboda yanda taga jijiyoyin kansa duk sun fito raɗau.
idonsa akan Fillo da ke ta kuka yana bin ta da wani irin mugun kallo na tsantsar jin haushi yace da Zaytuna,"saketa, ki saketa ko na haɗa har da ke". ya faɗa yana raising voice ɗinsa sama, har sai da Zaytuna tayi masa alama da yay ƙasa da murya kar cikin gida su jiyo, dan ita bata so a san lamarin ɓoyayyan auren nan acikin tashin hankalin da zai sa aƙi fahimta. ya ƙara sakar mata tsawa yana zare mata ido yace,"nace ki saketa ko?".

taƙi sakin Fillon tace,"Hammah it is not her fault, me ta sani  agame da hakan balle ta kiyaye, you just go and inform Maam about everything shikenan kai da ita duk sai ku huta".

yace,"tana haukar zan kawo ƙarshen komai, a hakan tana sauraron kowanne banza ya kulata, ita mahaukaciyar ina ce da bata san dai-dai da rashinsa ba?".
kamar zata yi kuka ta ƙara cewa,"please Hammah...". da ya yayo kanta kamar tashin iska babu shiri ta saki Fillo tayi gefe ɗaya.

me gadi yayo wajen da sauri yana bawa Turaki haƙuri duk da bai san meke faruwa ba amma da dukkan alama dai ba lafiyar. Turaki yay masa wani kallo shima yaja gefe, ya fizgi Fillo da ke ta tirjewa tana faɗin,"ni ka sakeni babu inda zan bika, me nai maka da zaka tsaneni, kuma Allah sai na rama marin da kayi min ai ba abin da na maka, Allah ni ka sakeni sai na rama".
ganin yana ƙoƙarin duƙawa ya ɗauketa ba shiri ta saki jiki ta bisa suka fita.

suna fita bakin gate ta gartsa masa cizo a hannu babu shiri ya saketa, ta falla a guje zata juya cikin zafin nama ya damƙota ya sunkuceta bai direta ba sai bakin ƙofa, bai ma san ashe a buɗe ya bar motar ba, yana zuwa ya buɗe front seat ya tankaɗata ciki yasa key ya rufe, dan yasan tsab zata iya guduwa before ya zagaya side ɗinsa.
Fillo ta saki wata razananniyar ƙara tana ƙwala kiran Umminaaaa, ƙarar da ta fito tun daga cikin motar har waje, hakan ya ƙara ƙular da shi, yaji kamar ya buɗe ya fito da ita ya rufeta da duka, yay saurin zagayawa side ɗinsa ya buɗe ya shiga gudun karta cire lock ɗin, ya doka mata tsawa sosai da cewa.

"za ki rufe min baki ko saina farfasa miki shi?".

ta ɗago kanta daga jikin glass ɗin da ta kifa, ta waigo tana kallonsa da ƙwayar idonta da tayi jajir, numfarfashi kawai take saukewa kamar wacce tai tseren gudu, magana take so tayi masa but ta rasa ta yanda zata furta saboda neman shiɗewa da take yi, ta kasa cewa komai sai yarfar da ɗayan hannunta da take yi.
ya ɗauke idonsa daga kanta yana kallon wurin da suka tsaya kwanaki ita da Amir, sannan ya mayar inda suka tsaya yanzu ita da Dr Yusuf, tukunna muryasa ta fito da wani irin amon sauti da ke shaida bala'in kishin da ke cinsa da kuma ɗacin ƙasan zuciyarsa yace,"ke akuyar ina ce da kowanne jaki zai dinƙa zuwa wurinki?, mutuncinki kika siyar ko me da ba za ki iya kame shi ba?, abinda ya faru da ke last bai isa kiyi hankali ba shine har kike ƙara sauraron wani namijin saboda baki da hankali, ke kinfi gane kiyita tallan kanki a titi ko?, ko ce miki akayi ƙofar gidan Alƙali matattarar ƴan iska ne da za ki dinƙa tara mana banzaye?".

Fillo ta kasa jurewa azabar da take ji yana shigarta, ta miƙa hannu ta damƙo kafaɗarsa, wannan yasa maganarsa ta katse ya juyo yana kallonta, sai yaga tana ta kallonsa tana hawaye kamar an kunna famfo, yaga jikinta ya saki gaba ɗaya hannunta na barin jikinsa ya faɗi, yaga ta kwantar da kanta a jikin kujerar idanuwanta sun lumshe numfashinta na fita da ƙyar.

sai yaji kamar tsoro ya kamasa, yay sauri kai hannunsa saman fuskarta, jin kamar bata motsi sai ya ruɗe ya shiga kiran sunanta yana girgiza fuskarta.  shiru bata amsa ba kuma kamar bata numfashi balle ta motsa, lokaci ɗaya hankalinsa ya tashi ya tattaro ƙafafunsa ya haye kan kujerar gaba ɗaya yana ƙoƙarin janyota jikinsa, can ƙasa yaji muryarta ta fita a wahalce da cewa,"hannuna". ta faɗa tana kama gaban rigarsa ta riƙe.
yace,"what?". ta ƙara cewa,"hannuna". ta faɗa tana fizgar numfashi.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now