*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*13*
Hakimi wato Alhaji Babba zaune akan royal chair ɗin da ke tamfatsetsen parlon da ya gaji da tsaruwa da kayan alatu, duk wani kayan jin daɗi na mo re rayuwa an zuba a wannan parlon, haka idan har kai farin shiga ne a zuwa gidan, to tabbas zaka iya rantsewa ba'a ƙasar nigeria kake ba. farin rawani ne akansa, kana masa kallo ɗaya zaka san jinin sarauta ya gama ratsa shi.kamar yanda tarihi ya gabatar, an kafa Masarautar Gombe a shekarar 1804 a lokacin jihadin Fulani wanda Buba Yero mabiyin Usman ɗan Fodio ne. Buba Yero ya mai da Gombe (Abba) hedikwatarsa domin yaƙin da ake yi da matsugunan Jukun na Pindiga da Kalam, daga nan kuma yayi ta kai hare-hare har zuwa Adamawa da ke gefen kogin Benue.
a lokacin sarki Alhaji Bukar Dukku shi ke riƙe da sarautar garin gombe, bayan rasuwarsa ne kuma babban ɗansa Hashim Bukar Dukko ya karɓi sauratar, wanda ya riƙe sarautar tsawon shekaru masu yawa.
Sarki Hashim Bukar ya ajiye ƴaƴa a ƙalla guda takwas kuma dukansu maza, kuma duk su takwas ɗin sun fito ne daga tsatson mace guda ɗaya Sarauniya Falmata, wacca a lokacinsu ne aka kafa tarihin sarkin daya zauna da mace ɗaya tal a karagar mulkinsa har rayuwarsa ta ƙare ba tare daya mallaki ko da ƙwarƙwara ba.cikin ƴaƴa takwas daya bari sune Adam, Ishaq, Lateef, Harun, Ibrahim, Yusuf, Isma'il, Shu'aib. akaf cikin yaran babu wanda ya samu kulawa me girma da gata daga wurin mahaifinsa irin babban ɗansa Adam, kasancewar tunda Sarauniya Falmata ta haife shi sai da ta shafe shekaru shida kafin ta ƙara samun wani cikin, lokacin har sun yanke tsammani da samun wani rabon, kuma daga haihuwar Yarima Ishaq shikenan ta shiga jero haihuwar ƴaƴa har sai da ta jera 8 gaba ɗaya.
duk da ƙarancin shekaru da Yarima Adam ke da shi a wancan lokacin, hakan bai gaza fahimtar cewar shi wanene ba, ya san daga tsatson daya fito, domin a ko da yaushe mahaifinsa na faɗa masa cewar gaba da bayansa shi ɗan sarauta ne dan ko mahaifiyarsa ma ƴar sarki ce.
bayan tarin ƙauna, soyayya, gata da kulawa wadda Yarima Adam ya samu a wurin mahaifinsa da mahaifiyarsa, sai kuma na ɓangaren al'umma. waɗanda suke ƙasƙan da kansu a gare shi matsayinsa na ɗa ɗaya tilo a wurin Mai Martaba da suke jin basu da tamkarsa.
hakan kuma ya haifar da aƙida ta girman kai da gadara a wurin Yarima Adam, har ta kai ga yana nuna ƙasƙanci ga na ƙasansa, hatta ga hadiman dake kewaye da Sarki kuwa.tun kamin ayi masa ƙanne ya haddace wani furuci dake fitowa daga bakin al'umma na kirarin da suke yi masa da Yarima Sarkin Gobe, kai ɗaya ne Yariman da akai babu irinsa, bayanka sarauta gabanka sarauta.
amma tun daga lokacin da mahaifiyarsa ta ƙara haihuwa sai yaji salon wannan kirarin ya sauya, kuma bai gyaru ba har zuwa lokacin da ta tsaya da haihuwa, kirakiran ya tashi daga kansa shi ɗaya ya koma har ga sauran ƴan'uwansa.dalilin da yasa zuciyarsa tayi baƙi kenan akan ƴan'uwansa, dan yana ganin silarsu zai iya rasa wasu tarin nasarori daya rubuce su a tafin hannunsa. da tafiya tayi tafiya sai ya zamana sam Yarima Adam baya ko da raɓar inda ƴan'uwansa suke, tsakaninsa da su nisantar juna, basa samun fuska a wurinsa matsayinsa na babbansu.
tun zuciyarsa na raya masa wani abu wai shi ƙiyayya har hakan ta tabbata akan ɗan'uwansa Yarima Lateef, wanda ya ƙwace duk wata fada da yake da ita a wurin mahaifinsu, wannan soyayyar da gata da dukkan komai da ya samu lokacin da yake shi ɗaya daga wurin mahaifinsa gaba ɗaya sai ta koma kan Yarima Lateef, hatta da soyayya da girmamawar da al'umma suke ba shi.kuma hakan ya samo wuri ne dalilin banbancin halayya, cikin kaf su takwas ɗin da Mai Martaba ya mallaka babu wanda ya ɗauko kyawun halayyarsa da ɗabi'unsa sai Yarima Lateef, shine yasan darajar mutane, saɓanin sauran da suke nuna ƙasƙsanci ga mutane, haka shine kaɗai mai sauƙin kai amma kaf sauran suna da mummunar ɗabi'a ta girman kai, kuma shi ɗaya ne mai son mutane da yi musu fara'a, gaba ɗaya Yarima Lateef kan manta da cewar shi ɗin jinin sarauta ne kasancewar ba'a gabansa take ba, amma ƴan'uwansa sarautar itace abar alfaharinsu da tunƙahonsu, a karan kansu sukan ji tamkar su mutstsuke juna saboda girman izza, kowannensu mulki da muƙami kawai yake wa hari a rayuwarsa amma banda Yarima Lateef.