41

124 9 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*41*
with confusion Baffa ke kallon Turaki, kuma tashin hankali da damuwar da ke tattare da Mum da Maama sai suka juye zuwa tsantsar mamaki. Maama ta dinƙa kallonsa babu ko ƙifta ido, so take ta tabbatar da idan a hayyacinsa yay wannan maganar, kamar dai ba ɗanta ba an sauya mata wani, kuma kamar dai yasha wani abu da ya juyar da tunaninsa.

Mum ta jefar da kwalbar hannunta, ta mayar da ƙwayar idonta kan Bello wanda ganin zata kallesa ɗin yay saurin sauke idonsa ƙasa.
Baffa yay ajiyar zuciya wadda babu wanda bai jita ba, muryarsa ta fito da amon da babu wanda bai sha jinin jikinsa ba acikinsu, ya juya zai bar ɗakin yace,"ku sameni a parlo".

wannan sautin muryar tasa da kuma yacca ya juya ya fice ɗin Turaki ya tabbatar da ya gama shiga uku, Bello ma ya ɗora hannu aka ya furzar da wata iska daga bakinsa, ya san Baffa ya san ya faɗansa idan ransa ya kai ƙololuwar ɓaci, yana da masifar son ƴaƴa shisa ma ba ya iya musu faɗa, but baya tolerating shits, ya san ba zai taɓa ɗaukar wannan kwaɓar da Turaki yajawa kansa ba, bayan wannan ɗan guntun jawabin da yay bai kuma san ta inda zai fara yin wani ba in aka tsaresu.

Mum tazo ta wuce ta kusa da shi fuuu kamar zata tashi sama, kallo ɗaya zaka mata ka san a fusace take. Turaki yabi bayanta da ido kafin ya maida kallonsa kan Maama ya buɗe baki zai yi magana, tayi saurin ɗaga masa hannu,"dakata, kar ɗan ƙwaya ya sake yace zai min bayanin da kaina ba zai ɗauke shi ba".

sai kuma ta miƙe tai bakin ƙofa tana ƙara faɗa masa,"kar in jini a cikin lamarinka". ta fice tana jin ita bama tasan actual tunanin da zatai akan maganar tasa ba, dan magana ce yay ba irin ta waɗanda ke cikin hankalinsu ba.

kowa ya fita a ɗakin aka bar Turaki da Fillo kawai, ya miƙe yana jin kansa na sara masa, Bello ya dawo yay tsaya jikin ƙofar yana kallon abokin nasa da tausayi yace,"ka taso muje tun wutar da sanyi sanyinta before ta balbala ta ƙona mu".

Turaki ya kallesa ya ɗauke ido, ya mayar da kallonsa kan Fillo da har yanzu take a wajen a duƙe kowa ma ya manta da ita, kukanta take tayi bata daina ba, ya tafi yana jin jikinsa kamar mara lafiya ya isa inda take, ya ɗagota tsaye yana faɗin,"please stop this crying its hurts me alot, from today ba zan ƙara saka ki hawaye ba, i promise".

ya faɗa yana ƙoƙarin ɗora kanta a ƙirjinsa, sai ta hana hakan tana ɗago da kanta ta kallesa tace,"me kace musu?".

Ya rufe ido ya buɗe yace,"ce musu nayi ke matata ce".

ta kasa ɗauke idonta akansa saboda itama a shock take, and gani take kamar ya sha ƙwaya ne shisa yake wannan maganar da hankali ba zai ɗauka ba.

"shi auren film ne dama?".
yana kallonta yace,"ba film ba ne, namu ɗin ne dai ya zama kamar a film".

ya faɗa yana matso da ita ta ƙwace daga riƙon da yay mata ta tankaɗa shi baya, cikin sheƙar sabon kuka tace,"leave me alone, Allah i hate you, ji a matsalar da ka jefa ni alhalin ni babu wanda ya taɓa riƙe hannuna ma, shikenan yanzu zaka ja Ummina ta yanka ni".

tai maganar tana wani kukan sosai.
da damuwa sosai yace da ita,"muje". taƙi tafiya, ransa a ɓace ya doka mata tsawa,"nace muje ko".

jikinta ya fara kyarma ya kama hannunta suka fito, tafiya suke kamar marasa lafiya, ji yake kamar babu komai acikin kansa, kamar babu yawun da zai yi musu bayani, taƙaimaimai ma bai san ta ina zai fara ba.

Bello dake daga gefensu yace da Fillo,"ki ɗaga ƙafa dan Allah, acikin matsala fa muke".

suka haɗa ido da Turaki yace masa,"kaita innalillahi ni inata yin hasbunallahu".

sai da Bello yay adu'a sosai tukunna ya iya saka ƙafarsa cikin parlon, ƙafafun Fillo suka fara shiga sannan na Turaki, idon Maama ya sauka akan hannunsa dake riƙe da nata wanda da alama forcing nata yay ta ƙasa ƙwacewa, lallai me babban suna ya riƙa da yawa.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now