56

109 7 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*56*
agogon dake manne a bangon ɗakin, tsintsiyar jikinsa ta kaɗa cikin sautin dake ba da ƙarar ɗil, ɗil, ɗil. sakanni 1,2,3 su ka wuce kafin ya shiga bugawar daƙiƙu 1,2,3 har zuwa biyar.

sautin ƙarar ya shiga cikin kunnuwan Turaki kaɗai, kuma a wannan lokacin komai ya lafa, komai banda sautin kukan Fulani da ke tashi.

dogayen gashin idon Turaki su ka ɗaga, kafin murfin idanuwansa su ka buɗe, ya waiga ya kalli Fillo, ya rungumota tsam a ƙirjinsa, numfashi kawai yake saukewa tamkar wanda yay tseren gudu tun daga china, magana yake so yayi but sam ya kasa, ji yake tamkar yau ne rana ta farko, kamar today is the first day he knows the virginity of a woman in his life, sai ya lumshe idonsa, abu ɗaya ne yake da akwai, daɗin wannan ya fi wancan.

yana jin yanda hawayenta ke sauka a jikinsa, sautin kukanta na fita ɗauke da tsabar wahala, hawayen da suka wanzar da wani bala'in tausayinta a ransa, ya ɗago hannu da ƙyar zai goge mata hawayen sai yaji ta ture hannun a zuciye.

ya buɗe idonsa ya kalleta sai yaga idonta a rufe yake, sai uban hawaye dake silalowa ta gefen idonta kamar an kunna famfo, da ma ya lafiyar kura balle an taɓota, yay wani irin murmushi da zai iya cewa bai taɓa yin irinsa ba, ƙara tsamketa yay a jikinsa har sanda baccin wahala ya ɗauketa.

kissing lips dinta yay kafin ya zare ta daga jikinsa, ya sauka akan gadon yaje ya kunna fitila don ba ya jin lamp ɗin dake kusa da gadon iyaka haskenta zai wadatar da shi wajen kallonta.
ya kalli agogo yaga ƙarfe ɗaya da rabi, dawowa yay ya zauna, yay tagumi yana kallon fuskar Fillo da tayi jawur kamar jini zai fito, dogayen gashin idonsa suka ƙifta a hankali, ya kamo hannunta ya riƙe yana kallon fuskarta da tayi looking so innocent.

hawaye duk ya bushe a fuskar, wani irin azababben sonta da ƙaunarta yaji suna fuzgarsa, ya san yana sonta tun a lokacin da bai san ya kamu ba, but a yanzu sai yake jin tamkar wani sabon son nata aka dasa a zuciyarsa, gaba ɗaya ta gama mallake zuciyarsa a yau, he was in a state of indescribable joy.

ya san yayi farin ciki da yawa a rayuwarsa, iyaka adadin farin cikin da ba zai ƙirgu ba, but bai taɓa tunanin cewa akwai wani farin ciki a duniya na daban ba kamar wanda yake ji a yanzu, sai yanzu ya shaida farin cikin duniya daban, haka ma farin cikin aure tare da wadda kake so daban.

kallonta yake yi tamkar yau ya fara ganinta, sai ƙyalli take yi, she looks so gorgeous and affectionate.
ya ɗora yatsansa saman lips ɗinta da ta turo gaba ta taɓe su, yay murmushi, in ban da bacci take yi ya san dole ma sai tayi masa tsiwa.

ƙarfe uku da rabi hannun Fillo ya miƙe ya sauka akan cinyar Turaki, ta buɗe idanuwanta da suka yi mata mugun nauyi, ƙwayar idonta ta sauka akan fuskarsa. a san da su ka haɗa ido sai tayi saurin runtse ido ta juyar da kanta gefe.

sabon kuka ne yake so ya ƙwace mata, so take ta motsa ta miƙe amma bata jin zata iya, every part of her body feels as if it is not her own, she is feeling pain everywhere, she wished ace bata yarda ta amince masa ba, kawai sai ta sa ki wani marayan kuka tana jin yacca take zugi ke ziyartar ƙasanta.

sautin kukan nata ya tafi ya zarce har cikin ƙuryar zuciyar Turaki ya matse zuciyarsa, zuciyar tayi rawa, da sauri ya ɗagota ya rungumeta yana shafa bayanta, shi kansa ya san dole tayi kuka, ya san bai yi mata ta sauƙi ba, bai ma san ta inda zai soma lallashinta ba, jinsa yake kamar babu wasu kalamai akan harshensa.

jin yanda hawayenta ke sauka akan fatarsa yasa ya dagota daga kafaɗarsa, sai kawai yasa harshensa yana goge ma ta hawayen, muryarsa na karyewa yake faɗin,"i am sorry wifey, you must pass this stage kafin kika zama cikakkiyar mace".

yaji ta ɗora hannunta akan ƙirjinsa, kafin muryarta ta fito cikin rauni tana faɗin,"mutuwa zan yi".
da sauri ya shiga girgiza mata kai yana faɗin,"not now, you will not die Wifiey, please don't say it again".

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now