*LULLUƁIN BIRI*
*57*
*ƙarfe tara na safe.*tun daga ƙofar gidan zaka shaida ana wani babban taro a gidan, taro irin na bikin aure.
motoci ne iri-iri daban danƙare daga wajen gidan, a yayin da gate ɗin gidan yake a wangale gaba ɗayansa, wasu mutanen na shiga ciki wasu kuma na fita.Khaleel ne tsaye a bakin gate, wanda yake ango a yanzu, waya ce kare a kunnensa yana faɗa akan abin da ban san menene ba.
Sameer ya iso wajen a lokacin yana cewa da shi,"Hammah yace kaje gida ka same shi".sai a yanzu na fahimci da wanda yake faɗan a wayar, amaryarsa ce suke rigima akan irin ɗan ƙaramin lamarin nan da ba'a rasa shi tsakanin kowanne ango da amaryarsa.
"to ba zan bayar ba, in za ki haƙura ki haƙura".daga cikin wayar ɓangaren Rashida ta ce,"haka kace?, to zaka san kayi da ƴar halak, wallahi sai in ce ma ba za'a kawo ni gidan naka ba".
ita ma tayi maganar a fusace kamar yanda shi ma yayi."hakan zai sa ki burge ni".
ya faɗa yana kashe wayar ya jefa cikin aljihu, ransa a ɓace ya nufi mota ya shiga.daga cikin gidan, idan ka shigo compound, zaka kutsa ne ta cikin tarin jama'ar da ke ta hayaniya su na kaiwa da komowa wajen aikace-aikace, wasu na wucewa da manyan kuloli na abinci, yayin da wasu ke tsaye akan babban kaskon da ake suyar nama a cikinsa.
idan ka lura da part huɗun da ke jere, za ka fahimci a ɓangare na uku daga ɓangaren dama, wanda shi ne ɓangaren Hajiya Ramla, anan ne taron mutanen yafi yawa, don ga takalman jama'a nan birjik daga wajen ƙofar parlon.a yayin da ka shiga cikin parlon, zaka tarar da manyan mata masu ji da kansu, waɗanda suka sha ilimin boko, boko ta ratsa su ta ko'ina, waɗanda mafiya yawan su ma'aikata ne a ƙarƙashin federal government.
wasu na zaune akan kujera yayin da wasu ke zaune a ƙasan carpet ɗin da aka malale duka parlon da shi, kowa na hira da abokin zamansa, hayaniyar dai tayi yawa wacca ta kai ga har ba'a iya jiyo sautin muryar wata dattijuwa da ta shigo ciki tana kiran sunan Hajiya Ramla.a lokacin ne kuma Hajiya Ramla ke sakkowa daga saman bene tare da ɗaya daga cikin amaren da ake aurarwa wato Samha.
magana suke yi yayin sakkowar ta su inda Samha ke ta ƙorafin hayaniyar."na nemi Nihal na rasa, ki lalubo min ita acikin taron jama'ar nan don Allah, ta zo driver ya kaita su karɓo mana ɗinkin mu. kina kallo ma Fillo bata sami saka ankon ɗaurin auren nan ba, haka Babana ya zo ya sakani a gaba yana ta kumbure-kumbure, ni ban san ya akai ku ka kaiwa ɗan shiriritar tela ba".
Samha ta amshe da cewa,"ai wallahi jiya na so da ni aka je da sai nayi masa rashin mutunci. ni yanzu Nihal ma aina zan ganta, da ƙyar ma idan bata ƙwace tayi gidan Hammah ba fa".
a lokacin ne dattijiuwar da ta shigo tana laluben Hajiya Ramla ta ƙaraso wajen.
Hajiya Ramla tace da ita,"sannun ku da aiki Maga"."yauwa Hajiya, wai da ma masu yankan nama ne suka ce Baffa ya kira waya yace a ƙara yanka raƙumi da raguna guda uku, sai akai raƙumin gidan Hakimi".
"sun yanka ne?".
"a'a da ma nace bari na zo na fara shaida miki"."to kinga garzaya ki faɗawa Madina, ki dubata a ɓangarenta ko ɓangaren yaran nan".
"to shikenan, batun funkason can fa ya za'ai da shi?"."ai da kun gama ku kai gidan Babana, ɓangaren Fillo za ku kai, nata ne aka yi mata saboda baƙin da ke can".
"to shikenan".Maga ta juya ta fita a parlon, yayin da Hajiya Ramla ta ƙarasa wurin mutanen da ke zazzaune a parlon, waɗanda mafi yawan su abokan aikinta ne.
"sannunku fa". ta faɗa a sanda take zama akan ɗaya daga cikin kujerun, kusa da wata aminiyarta Hajiya Shamsiyya.
"yo ke uwar amarya haka ake sai ki shige ɗaka ki barmu zazzaune anan".