*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya**4*
*E9611, Ibb Way. Maitama Phase 1 Abuja.*Ɗil 1,2,3,4,5, Adadin seconds ɗin da suka buga kenan ajikin agogon da ke manne a bangon ɗakin, tagogin windon ɗakin a buɗe suke, iska ta busa inda ta shigo ta cikin windon ta ɗaga labulen tagar zuwa sama.
hasken rana ya ratso ta tsakanin labulen ya haska idon Turaki da ke tsaye a gaban madubi yana saka agogo a tsintsiyar hannunsa. Wannan hasken yasa shi kanne ido tare da ɗagowa ya kalla tagogin da iskar ke ta busowa zuwa ciki, na tsawon seconds ɗaya sannan ya maida kansa ƙasa yaci gaba da ɗaura agogon.haka kawai daren jiya da zai kwanta yaji ba ya buƙatar iskar bature, ko ta fanka ko ta Ac, dalilin da ya sa shi buɗe window kenan, kuma ko da ya tashi sai ya manta bai rufe ba har ya kunna Ac, wanda sai a yanzu ya fahimci dalilin da yasa Ac ɗin taƙi yin sanyi yanda ya kamata.
ya gama taje sumar kansa ya miƙa hannu bakin gadon da hularsa ke ajiye zai ɗauka, yana ɗora hannu akai agogon ɗakin ya buga ƙara, sai ya ɗago kansa a kaikaice ya kai kallonsa ga inda agogon yake.Ƙarfe 9 na safe shi ne lokacin da ya buga, Mutumin da yazo cikin kansa a wannan lokacin shi ne Bello Ƙaraye, ko bai faɗa ba yasan yanzu yana can yana mita shi kaɗai na barinsa da yay yana jiransa. Sai kawai ya motsa leɓensa sannan ya ɗauki hular ya saka. Ya zauna a bakin gadon dan saka takalmi wayarsa ta shiga ƙara, ringtone ɗin i love you Maama ya karaɗe duka ɗakin.
Ya miƙa hannu ya ɗauki wayar kuncinsa na murmusawa. bai picking call ɗin ba har sai da ya yanke tukunna yabi bayan kiran, bugu ɗaya aka ɗaga tare da yin sallama. Allah ɗaya yasan me yaji acikin zuciyarsa a wannan lokacin, bai amsa sallamar ba sai da ya lumshe idonsa tukunna.
"Babana".
Sautin muryar Hajiya Madina tayi amo a cikin kunnensa, Sunan da ta kirasa da shi ya fama masa wani ciwo da ke manne a zuciyarsa, ciwon da ba zai taɓa warkewa daga gare shi ba har san da numfashinsa zai tsaya, ya riga ya san da wannan, kuma kowa ma ya san da shi.
Lokaci ɗaya yaji wani dunƙulallan abu ya tsaya a maƙogoronsa ya hana yawu wucewa, bai san lokacin da ya ɗaga wayarsa ya daki goshinsa da ita ba. Irin hucin da yake jerawa ya ankarar da Hajiya Madina situation ɗin da yake ƙoƙarin shiga, dan haka da sauri tayi ƙoƙarin dakatar da hakan ta hanyar kiran sunan da ita kaɗai ke kiransa da shi, kuma shi kaɗai ne sunan da za'a faɗa masa ya faranta ransa.
"Me babban suna, be patient please".
Lokacin da tayi furucin kwanciya yay a jikin gadon yana fuskantar P.O.P, yatsun hannunsa na hagun a saman karan hancinsa yana murzawa da ƙarfi, yayinda idanuwansa ke a kulle har yanzu basu bar raɗaɗi ba.
"Ina kwana Maama".
"Ka tashi lafiya?"."lafiya lau, ina fatan duk kuna lafiya?".
"muna lafiya lau, Ya wurin aikin naka?"."Aiki mun gode Allah, yanzu nake shirin fita".
"Glad to hear that, Allah ya taimaka ya bada sa'a da nasara".Daga kan dining ɗin da Hajiya Madina ke zaune, ta kai glass cup ɗin da ta ɗauka bakinta ta kurɓi lemun ciki na five alive, sannan ta ƙara cewa da Turaki.
"When are you coming back home?".
"Ina kan hanya zuwa wani satin Insha'Allahu, munyi magana da Baffa jiya".
Jin yace mata sunyi magana shi da Baffa ta murmusa kuncinta kamin tace,"To shikenan Allah ya dawo min da kai lafiya".
"amin ya Allah Maama".
"ina fatan Baka da matsalar komai ko?"."Babu Maama".
"to Allah yayi maka albarka...Make sure you eat your breakfast before going to office".Ya kai hannu ya shafo gefen fuskarsa inda gashin sajensa yake kamin ya amsa da,"insha'Allahu Maama".