*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*_🤔zato dai zunubi ko da ya kasance gaskiya, ku daina ɗaukar hakki babu kyau ni gaskiya nake faɗa muku, ahh tou🤣, yo kowa ya tashi sai ya wani kama cewa Hajiya Madina kaza-kaza, banda ma dai neman magana yaushe kuka taɓa ganin ta cutar da wani daban balle Turaki da ya gama nannaɗe zuciyarta😒...to a daina gaskiya ban so, duk wanda naji ya ƙara taɓata zan hau bori😭😭..._
*18*
After long minutes sai ga Zaytuna itama ta shigo room ɗin, har lokacin Khalil yana nan bai tafi ba, yana zaune akan kujerar da Kaka ta ajiye masa.
yana kallon Zaytuna da mamaki yace,"from where?". bayan duk ta gaida su Kaka tare da tambayarsu ya me jiki tace da shi,"bamu jima da shigowa garin ba, so muna sauka a airpot mu kai waya da Hamma yake ce min yana nan".Khalil ya ƙara tambayarta,"ya Granny ɗin?".
tace,"tana lafiya, duk tana gaishe ku...da ta saka rigimarma sai mun zo tare tana so taga Hammah".
yace,"Allah sarki Granny, insha'Allahu zan matsa masa akan muje, sai mu dawo a ranar tunda dai am sure ba zai kwana ba".
Zaytuna ta cirewa Fillo drip nata da ya ƙare yanzu, itama tana tambayarta yanda take jin jikin tana faɗa mata komai da sauƙi ƙafarce dai har yanzu.
after five minutes Zaytuna ta yiwa su Kaka sallama saboda kiran da Baffa yake yi mata, tare suka fita da Khalil wanda yake ta mamakin yacca akai har yanzu Turaki bai shigo ba.bayan fitarsu Maijidda ta dafa shoulders ɗin Fillo tace,"mene damuwar?".
tace,"me kika gani?".
Maijidda tace,"na san dai ba ki da lafiya amma yanayin fuskarki ya nuna akwai damuwa a ƙasan ranki".
Fillo ta haɗiye yawu tukunna ta ɗago ta kalla Maijidda sannan tace,"me yake damun Amir?".
Maijidda ta tashi daga kujerar da take zaune ta dawo gefen gadon kusa da ita ta zauna, ta kamo hannunta ta riƙe acikin nata tace,"me kika gani?".
Fillo ta dake ta hana kuka ƙoƙarin fitowa tace,"sannu fa kawai yace min, ina amsawa yasa kai ya fice".
"kinyi masa wani laifi ne?".
ta girgiza kanta,"a'a ni banyi masa komai ba. kuma ko da ace ma nayi masa ba zai min haka ba tunma da ya ganni banda lafiya".
Maijidda tace,"to kwantar da hankali ba abin da kika masa, kawai yana cikin damuwa ne akan lamarinki. yace ya kasa fahimtar me ke faruwa, yana ganin kamar mutanen ɓoye naso su shafeki ne tun a wancan ciwon da kika yi, amma wannan karon sai yaga kamar ma sun riga sun shigeki...baki gani ba wallahi yanda yake ta sadaƙa yana sauke miki alƙur'ani, anan fa yake kwana kullum ba ya tafiya, abinci sai Innarsa tayi da gaske".
Fillo tai ɗan jim kafin tace,"to ai ni banda wasu aljanu, hasashensa ne dai kawai".
Maijidda tace,"to aikuwa abin da kowa ke faɗa kenan".
Fillo ta kalli su Kaka da suke can gefe su na maganarsu, hankalinsu ba ya kansu gaba ɗaya. murya can ƙasa tace,"Maijidda ina asirin da nace miki zan ɗauke a ɗakin Turaki?".
idanun Maijidda a waje take kallon Fillo da al'ajabi, ai dama tunda hakan ta faru ta fara tunanin da wuya idan ba karambaninta ne ya bata damar ɗauke asirin da ta gaya mata zata ɗauke ba. ita kam ta fara tsorata da lamarin ƙawarta, ta bakin Amir aljanu sun shigeta domin mutum dai ba zai yi abin da takeyi ba.
Fillo taja hannun Maijidda da taji tayi shiru,"kina da matsala wallahi, shi yasa wani lokacin da faɗa miki abu gwara shiru".
bata bawa Maijidda damar magana ba taci gaba,"na ɗauke asirin harma ya ƙone".