*LULLUƁIN BIRI*
*39*
*08:30am.*
acikin bedroom ɗin na Baffa, Hajiya Ramla ce tsaye gaban mirror ita da shi, sanye take da shadda golden colour tasha azababben aiki ajiki, anyi mata ɗinki bubun sai ƙyallin stones take yi, tayi masifar kyau kamar balarabiyar usuli, ita da Baffan iri ɗaya sak.
daren jiya tailor ya kawo musu ɗinkin su uku iri ɗaya, ita take taimakawa Baffa wajen shirin da yake yi, tana shirya shi ɗin suna hira cikin annashuwa da jin daɗi tare da alfaharin ƙara kasancewa da junansu.turare ta ɗauka ta fesshe shi da shi tuni kuwa ɗakin ya ɗauka da wani daddaɗan ƙamshi, Baffa ya rungumeta jikinsa yana faɗa mata irin son da yake mata da kuma kewarta da yay a sanda bata tare da su, albarka kawai yake zunduma mata kamar yawun bakinsa zai ƙare.
wayarsa tayi ƙara ta zame daga jikinsa tai saurin isa kan gado ta ɗauko wayar, sai da tayi picking tukunna ta kara masa a kunne.
daga can ɓangaren Boɗejo tayi sallama suka gaisa da Baffa, tana kuka ta-ke shaida masa halin da Fulani Azima ke ciki, shi kansa Baffa da ya dawo a jiya jikinsa yayi matuƙar sanyi ya kuma tsorata ainun da yanda ya sami Fulani Azima, ya ƙara jin tsoron Allah da kuma tsoron sharrin duniya, saboda yanda ta dawo kamar ƙwarangwal halittarta dai babu kyan gani a yanzu, har ƙwalla sai da yay musamman da ya fahimci tana so tayi magana da shi, to amma shi har ga Allah ba zai iya bata wannan damar ba saboda ba zai iya zaman kusa da ita ba dalilin mugun ɗoyin da take yi, mijinta kansa sai ta window yake ganinta balle kuma shi, yana ji ma ana batun dawo da ita gida saboda su kansu asibitin sunce ba zasu iya da ita ba.cikin sigar kwantar da hankali Baffa yace da Boɗejo,"kiyi haƙuri, adu'a zamu cigaba da mata Allah ya bata lafiya".
ta ƙara sautin kukanta tana faɗin,"Dikko ni ƴarta nake tausayi, a jiya yarinyar nan Ilham tayi suma yafi biyar, ko abinci bata iya ci Dikko, aljanun da bamu santa da su ba sai tashi suke, yau baka ga yanda suka farfasa mata jiki ba". ta faɗa tana kuka sosai.Hajiya Ramla dake jiyo komai ta sauke numfashi tana jinjina al'amarin sakayya, ita dama tun can bata da niyyar tonawa Fulani Azima asiri akan abinda tayi mata, abunda zuciyarta ta yanke mata kawai shine zata barta da Allah sai kuma sun haɗu acan lahira, amma anan dai ba zata taɓa faɗar cewa ga wacca tai silar barinta gida ba, duk da cewar tunda ta dawo ta bada labari kowa ke cewa aikin asiri ne, to amma ko kusa bata yarda ta bar hakan a zuciyar mutane ba, duk da Hajiya Madina taso ta ɓaro komai ɗin dan har sunan Fulani Azima sai da ta ambata tana cewa wallahi sai taci ubanta zata kawo ƙarshen makircin matar, to da ƙyar dai ta tausheta ta bar maganar.
Boɗejo na kukan sosai tace,"Dikko ka bawa Ramla wayar ina so nayi magana da ita".
"tom shikenan, amma ki daina kukan hakan dan Allah".
tace,"Dikko ina ni ina daina kuka kuwa yanzu, ai ni da barin hawaye har sai Azima ta mutu, amma indai zanke ganinta a wannan halin hankalina ba zai kwanta ba kamar yanda hawayena ba zasu tsaya ba, wallahi ma ni daka ganni na yafe mata duk wani kalar rashin kyautawa da tayi min".Baffa ya miƙawa Hajiya Ramla wayar, suka gaisa da Boɗejo, tai ƙasa da murya tana cewa.
"kiyi haƙuri Ramla ƙarar ɗanki na kawo miki, wallahi yaron nan azzalumi ne baya tsoron Allah kwata-kwata, kinga dai ko maƙiyin Azima yana zuwa ya dubata amma shi tunda ya kawo matar tasa ya yasar anan bai ƙara waigowa ba, tace min ko kiranta a waya ma baya yi, idan ita kuma ta kira shi suna gaisawa ɗan banzan yaron nan zai kashe wayar baya ko tambayar lafiyarta balle ta uwar dake cikin wani hali, to dan Allah ki faɗa min wannan mijin aure ne, kuma wallahi ƙarya yake yi yace baya son Ilham, dan dai kin ɓata ne lokacin yarintarsa amma da ko ke sai kin aura masa Ilham, to ni dai yanzu abinda nake so daga gareki tunda kin isa da shi kisa yazo wajen matarsa ko da ba zai zo duba Azima ba dan wataƙila sharrin da tayi masa ne bai manta da shi ba, ba haka ake ba sam wallahi, ya kamata yazo ya kasance da ita ya kwantar mata da hankali da irin salon ma'aurata, to da yake dai shi ɗin baida addini shisa, kuma rashin hankali da tunani ke damunsa, duk da nasan Madina ce take zuga shi wallahi, kuma zan dawo ne zata gamu da fushina da bata taɓa gani ba".