33

116 5 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

'''DAGA MARUBUCIYAR'''

1-Sirrin Ɓoye
2-Al'amari
3-Hidaya Noor
4-Alhussain
5-Sanadin Talauci
6-Ƙaddarar So
7-Prince Khaleed
Da sauran su.....

*33*
*Switzerland*
sanya take cikin rigar sanyi mai kauri sosai, dogon wando ne fari a jikinta sai p-cap red colour da ta saka, wanda shigar ya amsa farar fatar jikinta sosai. yanayin fuskarta kaɗai zai shaida maka cewar bata cikin walwala da annuri, haka kuma ƙwayar idonta na shaida rashin nutsuwar da take da ita a zuciyarta a kullum a ko da yaushe.
a tsaye take daga jikin window tana leƙan waje, tana kallon yacca ruwan sama ke sauka, sanyin garin na ratsowa har cikin ɗakin yana shiga jikinta.

ta sauke dogon numfashi tare da ɗaga gorar hollandia ɗin dake hannunta ta ƙara kurɓa, ta buɗe lumsassun idanuwanta a sanda take juyowa ta fuskanci kyakykyawan farin bafulatanin dake zaune kan kujera yana danna wayarsa, shima fuskarsa kaɗai ta isa ta shaida maka cewar zuciyarsa a ƙunci take.
Samha ta ɗauki tsawon daƙiƙu biyar tana kallon Sameer kafin ta buɗe baki tayi magana, muryarta ta fito acikin rauni da kuma damuwa.

"tsawon shekaru masu yawa, har kullum, har yanzu na kasa haƙuri da juriya akan yacca nake ganin mahaifiyata ta fifita wani daban akan ni da ta haifa, tafi son sa fiye da ni da ta haifa, tafi basa kulawa fiye da ni da ta haifa, tafi kyautata masa fiye da ni da ta haifa, tafi damuwa da damuwarsa fiye da ni da ta haifa, hankalinta yafi karkata 100% akan ƴaƴan da bana cikinta fiye da wanda ta haifa acikinta. ka faɗa min ta yanda za'ai nayi farin ciki duk da cewar ban taso a tagayyare ba, ban taso a cikin talauci ba, ban taso da rashin gata ba, ban taso na nemi abinda nake so na rasa ba, ban taso na rasa soyayyar mahaifi da ta mahaifiya ba, sai dai wannan soyayyar tasu ce tayi min kaɗan, ba kalar wannan soyayyar nake so daga wurin mahaifiyata ba, kalar waccan soyayyar da take nunawa Turaki da Zaytuna ita nake so, ita nake da buri ita nake da muradi, amma tsawon shekaru masu yawa na rasata, na kasa samunta duk ta yanda na so...shi yasa ya zama dole na kawo ƙarshen wannan bambanci da iyayenmu ke nunawa ko ta halin ƙaƙa, ko da ace asanadin hakan zan rasa raina".

ta ƙarashe maganar muryarta na bayyana wani irin baƙin ɗaci dake tasowa daga ƙasan zuciyarta.
shirun da tayi yasa Sameer ya ɗago da kai yana kallonta, tana tsaye hawaye na bin fuskarta, ba ta da alamar zata hana su zuba balle tasa hannu ta goge su.
ya rufe idonsa for few seconds ya buɗe yana sauke numfashi tare da ajiye wayarsa a gefensa.

"ke kaɗai ce dama kika rasa dukkan abinda kika lissafa?, ko kuma ke ɗaya ke cikin irin wannan ƙuncin?".
kanta na ƙasa tana kallon ƙafarta dake cikin black socks tace,"bani ɗaya bace, ko Hammah Khalil da Nihal na san basa jin daɗin haka, deep down there heart na san suna jin zafi, domin babu ɗan da zai so yaga iyayensa na nuna banbanci tsakaninsa da ƴan'uwansa...so amma abinda nake so ka fahimta Sameer inda ace hankalin mahaifiyamu na kan mutum guda acikinmu da ta haifa, to da atleast zamu sami sassaucin raɗaɗin zuci, ba wai take nunawa kamar ba ita tayi naƙudarmu ba".

cikin zafin nama tai wurgi da hollandia ɗin dake hannunta tasa ƙafa ta murje, tana huci take cewa,"wani sa'in zuciyata na faɗa min Turaki da Zaytuna asiri suka yiwa Maama, ba haka suka barta ba, don babu uwar dake cikin hayyacinta zata ke nuna irin son kai tsakanin ƴaƴanta da na kishiyarta, but what ever lokaci yayi, wallahi a wannan karan babu fashi da tsiya tsiya sai na aika da su lahira, zanbi ta irin waccan hanyar da suka bi, ko duk bokayen duniya zan bi saina sa an kawo min ƙarshen su Turaki".

Sameer ya hura iska a bakinsa sannan yace,"bin boka is not the best solution dear tunda aikin asiri na karyewa, and ba zan bari ma mu aikata shirka ba. abu ɗaya kawai da yake nan waɗan nan mutanen su zamu ƙara bawa kwangilar...".
ai tun bai ƙarasa ba ta duki table ta katse shi da cewar,"kuɗina ba zai ƙara zuwa hannun gantalallun can ba".

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now