*LULLUƁIN BIRI*
'''DAGA MARUBUCIYAR'''
1-Sirrin Ɓoye
2-Al'amari
3-Hidaya Noor
4-Alhussain
5-Sanadin Talauci
6-Ƙaddarar So
7-Prince Khaleed
Da sauran su.....*32*
ganin Hajiya Madina yasa drivern tafiya wurinta da sauri ya karɓi ledan kayan dake hannunta, a gaban mota ya aje manyan ledan kayan kusan guda 5, da gani kasan ba siyayya bace ta jarirai kamar yanda ta faɗa, siyayya ce ta musamman tayita don yin kyauta ga Fillo.
drivern ya buɗe mata back seat ta shiga, sai dai tun kamin ya zagayo ɓangarensa har Hajiya Madina ta kula da rashin Fillo cikin motar. hakan yasa ta buɗe motar ta leƙo kanta tana faɗin,"Ɗan Usaini ina ƴata?, ina Halimatu taje?".Ɗan Usaini ya dakata da buɗe motar yace,"Hajiya ai taje kai miki waya ni kuma naje ɗan yin uzuri".
Hajiya Madina tace,"ban gane nufinka ba".
yace,"ruwa naje kamawa, to ban san ba gaskiya ko ta dawo na dai barta ta shiga ciki kai miki waya".lokaci ɗaya Hajiya Madina ta fito a motar gaba ɗaya,"ka daina cewa ta kai min waya. kai wayar tun yaushe ne?, kusan fa minti biyar kenan, tana bani ta fito".
Ɗan Usaini na waige yace,"to ko ta zo ta tarar bana ciki sai ta koma, bari na duba cikin store ɗin".ya faɗa yana barin wajen, Hajiya Madina tabi bayansa. lokacin hankalinta duk bai tashi ba amma dai ta tsorata, ina Fillon zata je?, idan cikin store ɗin ta koma ai tana shigowa zasu yi clashing tunda tana daga bakin ƙofa tana biyan kuɗi.
daga cikin store dai har wajensa babu Fillo, a wannan lokacin hankalin Hajiya Madina ya fara tashi, haka suka dinƙa zagayen arean wajen suna kiran sunanta suna dubawa amma ba ko alamarta.Ɗan Usaini na tare da me gadin store ɗin yace da Hajiya Madina,"ƙilan ko da ta shiga kai miki wayar makuwar hanyar fitowa tayi".
Hajiya Madina dai tana tsaye ta kasa cewa komai, saboda yacca take jin numfashinta na neman yankewa, iska ce a wajen ke ta kaɗawa amma ita zata iya rantsewa hucin zafi take ji ajikinta, zata iya rantsewa kamar ji da ganinta ya ɗauke.ƴar mutane ta ɓta ata sanadinta?, me zata ce da Kakar yarinya?, me zata ce da wanda ke shirin aurenta?. lokaci ɗaya kanta yay wani mugun sarawa kawai sai ta fashe da kuka, staffs dake cikin store ɗin suka fito dai anata ƙara lalube, tsawon kusan minti 30 inuwar Fillo ma ba'a gani ba.
da ƙyar Hajiya Madina ta iya picking call ɗin Baffa, ta faɗa masa halin da take ciki, sai dai kamin yace komai Hajiya Madina ta yanke jiki ta faɗi a lokacin, dalilin abinda taji Ɗan Usaini na faɗawa me gadin wajen."to ni dai bana ce hakan ba ne, zargi kawai nake da hasashe. kaga bakin bishiyar can anan naga motar tayi parking, kuma wallahi tun lokacin da zan tafi fitsarin naji hankalina bai kwanta da motar ba, to kuma sanda nake dawowa sai naga motar na barin wajen, sai na bita da kallo har ta ɓacewa ganina, kasan Allah ba wai don saboda ɓatan yarinyar nan ba, jikina kawai naji bai aminta da motar ba, Ya Rahmanu dai yasa ba ƴan garkuwa bane suka yi gaba da yarinyar nan".
da hanzari akai kan Hajiya Madina, da ƙyar aka iya kamata aka sakata a mota sai asibiti.
Tunda suka isa asibitin aka karɓe ta aka shiga bata taimakon gaggawa saboda yanayin yadda ta ke a sume, su na tsaye cirko-cirko a ƙofar ɗakin aka shiga da ita suna jiran suji me likitan zaice in ya fito, ba'a fi mintina biyu ba ya fito yana ƙarasa zare gloves ɗin hannunsa a lokacin ne kuma Baffa ya iso wajan da hanzarinsa.ganinsa yasa Ɗan Usaini nufarsa, sai dai ko ta kansa Baffa bai bi ba yay wajen likita.
"Likita ya jikin matata?" Baffa ke tambaya yana kallon likitan da yake goge hannunsa da hand sanitizer.ya kalla Baffa yace,"Patient ɗin ku jininta ya hau sosai, akwai abinda ya firgita ta lokaci ɗaya shiyasa BP ɗinta yayi high, wannan dalilin ya saka ta suma, but yanzu an saka mata drip kuma da izinin Allah da ta farka zata dawo dai-dai."