61

263 12 1
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*GAMJI WRITER'S ASSOCIATION*
   _Home of exceptional writers._

*61*
Da gudu ta fito daga cikin ɗakin, isowarta falo suka yi karo da Inna Wuro ta faɗi a ƙasa, ita ma medical glass ɗin idonta ya faɗi, nan da nan ta shiga kokawar ɗauko shi daga ƙasan.
idanun sai ƙiftawa suke yi kamar an tsokane su, sai da ta saka glass ɗin sannan suka daina ƙiftawar, kuma kallo ɗaya zaka yiwa ƙwayar idon nata ta cikin glasses ɗin ka san ba lafiyayyu ba ne.

yanda jikinta ke rawa zaka ce ko bata da lafiya ne, nan kuwa zallar rashin gaskiya ne a tare da ita.
ta kalli Inna Wuro ta gefen ido, dariya ta taho mata tayi saurin sa hannu ta toshe bakinta.
"huhuhu, la'ila ha'ilallahu, waiwaiwai. to ni dai sai dai in ce Allah ya isa kawai".

ta buɗe baki zata yi magana Inna Wuro tayi saurin ɗaga mata hannu tana girgiza kai.

"a'a fa ni ba sai kin ce min komai ba, ai na riga na kaiwa Allah ƙara, zai yi min sakayya da kansa, cuta ce dai kin gama yi min ita".

Aliyu ya shigo a lokacin, Inna Wuro ta ɗaga kai ta dube shi tana aikin rumtse ido, ta yarfar da hannu ta ce,"gwara da Allah ya shigo da kai Aliyu, hanzarta ɗauko mota ka kawo bakin ƙofar ɗakin nan nawa, gidan sarkin ɗori zamu tafi tun ban gama shiga uku ba, ta ɓalla min duk ƙafafun nawa biyu, kai baka ji irin azabar da ke ratsa ni ba. waiwaiwai, huhuhu Allah dai ya saka min".

Aliyu ya kai dubansa ga Maama wacca ke tsaye tana gyara zaman glass ɗin idonta, fuskarta ɗauke da siririn murmushin ƙeta, a yayin da dogwayen lashes ɗin sama da na ƙasa suka haɗe, kafin ta buɗe su kyawawan chocolate eye balls ɗinta masu ɗauke da ruwa su bayyana.

suna haɗa ido da ita tayi ƙasa da kanta tana haɗe pink lips nata, still tana ƙunshe dariyarta.
sim sim ta bar bayan Inna Wuro ta nufi hanyar fita Aliyu ya dakatar da ita, ta tsaya tana rumtse idanu kafin ta juyo ta kalle shi.

cikin siririyar muryarta me bala'in zaƙi tace,"Uncle ba na sane fa".

sai ya kalli Inna Wuro da har yanzu take dirshen a ƙasa, sai matsa ƙafafu take yi a lallai sun karye.
"Inna to kinji bata sane".

"to dama tsoron Allah take yi da zata faɗa maka gaskiya, ni dai tun da ta riga ta cuceni kaje ka ɗauko mota kawai mu tafi gidan sarkin ɗori tun ban koma amfani da sanda ba, dan ƙarshe dai asibiti su yanke ƙafafun, ni kuwa ina zan so naga ana tura ni a keken guragu".

tayi shiru tana girgiza kai alamun takaici ya isheta."sam yarinyar nan bata da mutunci wallahi, ka duba fa Aliyu ka gani an fi ƙarfin awa guda da watsar da ni da tayi a ƙasan tiles ɗin nan, amma kalmar haƙuri ta gagara fitowa daga bakinta. alhalin tun duku dukun safiya aka baro gidan uba aka taho gidan ɗana cin arziƙi, to da yake ma dai ɗan Adam butulu ne, amma babu komai akwai Allah ai".

Maama tace,"kiyi haƙuri Inna Wuro".

"a'a wallahi ba zai yiwu ki cuce ni ba ki bani haƙuri, ke dai je ki kawai da mugun halinki".

Maama ta fice daga ɗakin tana dariya.
Aliyu yazo ya kama Inna Wuro don ɗagata, ta miƙe tana faɗin,"ba abin nace zan bawa Zainabu shawara ba tace zata ƙullace ni, ko kuma ta zage ni, amma da sai in ce ku kai yarinyar nan gidan ruƙiya zance na domin Allah kenan".

Aliyu yay guntun tsoki,"zancenki kenan aljanu".

"to kaji ba, ina kuma ga uwarka na faɗawa. yanzu in ace jikar Falmata ce wallahi kaina tsaye zanje in bata shawarar nan. yanzu kai Aliyu ban da kai ma dai halin uwarka ka yo na rashin son gaskiya tsakani da Allah ai ka san wannan ƴa dai tana da iskokai".

yay mata wani kallo yana nufar kujera ya zauna,"babu wani zancen gaskiya tun da ba gani kika yi ta tayar ba".

"to Aliyu har sai ta tayar za'a san tana da aljanu, ina batun watsota da suke yi a guje fa?, Kullum fa haka zaka ganta fuuuu kamar guguwa, haba a duba lamarin nan dai. ni ko da kaji na faɗi haka ba wai sonta ne bana yi ba wallahi".

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 07, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now