27

97 9 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

_not edited._

*27*
Fillo ce zaune akan dakalin bayan ɗakinsu, daga yanda ta zabga tagumi kasan tunanin wani abu takeyi wanda ke damun ranta.
ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jajir, idon kuma ya ƙara girma. Maijidda ta ƙaraso wajen tana faɗin,"na tsani wannan tagumin naki wallahi".
Fillo ta ɗago ido tana kallonta, bata iya cewa komai ba saboda zafin da zuciyarta ke yi mata, tun ɗazu take so tayi kuka ko ta sami relief amma kukan yaƙi zuwa.

"kwana nawa kina kuka?, zatonki kuka na maganin damuwa?, to idan baki sani ba kuka baida amfanin komai, damuwarki ya wuci ki kaita gaban Allah, akwai me yaye miki sama da shi ne?, amma sai kiyi ta faman kuka kuma ayi tambayar duniya kiƙi magana, da me kike so Kaka taji?, bafa isassan lafiya ke gareta ba. kuma ke har me kika nema kika rasa a duniyar nan da zaki ɗau damuwa kisawa ranki kina ƴar ƙaramarki, salon dai jawa kai matsala".

Maijidda tayi shiru a sanda taji Fillo ta riƙe hannunta gam, tasan ba komai bane illa kukan da take so tayi, ta janyo Fillon jikinta ta kwanta a kafaɗarta, tuni kukan da Fillo ke jira tun ɗazu yazo mata, saida tayi me isarta tukunna ta yakice daga jikin Maijidda tana goge hawayenta.

cikin muryar kukan da bai gama sakinta ba tace,"Maijidda ke kike ganin ban rasa komai ba tunda Kaka ta tsaya min, amma a zahirance ni nayi babban rashi tunda har na rasa uba, ba wai don ya mutu ba, yana raye amma na zama kamar banda uba a raye, tunda uwata ta haife ni ban sami soyayyar uba ba irin wacce ko wanne ɗan halak ke samu, ban sami gata ba irin wanda kowanne ɗan halak ke samu daga wurin mahaifi, ban samu tarbiya ba daga wajen ubana, ban sami ilimi ba daga garesa, ban sami kulawarsa ba, ban sami farin ciki daga wurinsa ba balle naji daɗi daga garesa, ya kirani da suna shegiya, ya kirani da ƴar zina alhalin akan shimfiɗar sunnah ya samar da ni...".
muryarta ta harɗe tana kifa kanta akan cinyar Maijidda tana ƙara fashewa da sabon kuka.

"Maijidda banyi dacen uba ba, ni kaɗai ce nayi rashin sa'ar uba, ta dalilin baƙin cikinsa har yau ban san inda Ummina take ba, bamu san ina ta tafi ba, ki tayani adu'ar duk inda take Allah yasa tana cikin kariyar ubangiji, jikina na bani Ummina bata rasu ba tana raye, amma Kaka wai sai tayi ta ce min Ummi ta mutu".
kukanta ya ƙaru sosai, kuma daga ita har Maijiddan kukan suke yi. "Maijidda i wish ace ana sauyawa tuwo suna dana sauya Hayyo a matsayin ubana, i wish Hayyo is not my father, I wish I could take revenge for what Hayyo did to me and my mother. but i can't, i can't do that Maijidda, duk da lalacewarsa i still feel his love in my heart".

da ƙyar kukan Fillo ya tsaya bayan da ta ɗau tsayin mintuna tana bawa zuciyarta haƙuri da kalar tata ƙaddarar.
tana riƙe da hannun Maijidda tace,"ina key ɗin motar Turaki da na baki ajiya?".
Maijidda tace,"yana ƙasan kayanmu. amma Fillo ba kya tsoron garin mayarwa a ganki".

tana kallon wani side na daban tace,"idan ma an ganni there is no problem, and ba ma komawa ɗakinsa zanyi na ijje ba, Maama zan kaiwa".
Maijidda tayi ajiyar zuciya tace,"gaskiya Hajiya Madina ta dabance, ni tunda kika ban labari na rasa ma abinda zance, nayi matuƙar girgiza da lamarin".
Fillo tace,"ni kaina farko ban yarda ba sai da kunnuwana suka jiye min...kiji fa wai a tsinke burkin motar, wai sai ta kira shi tace yaje ya ɗaukota a anguwa motarta ta lalace, wai in ya taho sai me tirela ɗin yasha gabansa kawai yabi takansa".

Fillo ta rumtse ido gam tana jin kanta kamar zai buga. "Maijidda wannan masifa har ina?, ace ka dinga harin jinin ɗan'uwanka?, me ya yi musu?, Allah da ƙyar ƙafafuna suka iya ɗaukata suka kai ɗakinsa, ke yanda na tafi a rikice ko a hannunsa naga key ɗin motar sai nayi kokawa da shi na ƙwace, ko kuma na faɗa masa komai kowa ya huta, saboda Hajiya Madina yasa kawai ban faɗa masa ba amma wallahi nayi niyya, to kawai dai ina tausayin halin da Maama zata shiga ne. kuma nayi rashin dabarar na faɗa mata ma tun a daren, dan da wuya in babu spare key da zai ce zai yi amfani da shi".

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now