34

98 9 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

_Shafin gaba ɗayansa sadaukarwa ne ga duk wani makarancin littafin *LULLUƁIN BIRI*, ina jin daɗin yanda kuke bibiyar littafin nan, alkhairin Allah ya isa gare ku._

*34*
da asuba Turaki na dawowa daga sallan asuba kira na shigowa wayarsa, babu suna ajikin lambar dan haka ya tsaya yana kallonta da son ya fahimceta, ganin ba lambar da ya taɓa sani bace ya ɗaga.
yana karawa a kunnensa Gimbiya Aisha ta kwaɗa sallama cikin dodon kunnensa da irin muryar da kana jinta kasan tasha uban kuka.

banda koyawa ta addininsa da babu abinda zai sa shi amsawa, dan sarai ya shaida muryarta, kuma ko ba komai taji daɗin amsawar saboda muryarsa nan me daɗi, daɗin da take jin yafi na sarewa tsuma zuciya.
daga kan gadon da ta ke tasa tissue ta ƙara goge idonta, with littile courage tace masa,"barka da asuba. ya amarci?".
tsabagen mamaki ma bai san me zai ce mata ba, last kira da tayi masa Bello ne ya karɓi wayar ya keta mata rashin mutuncin da ko kare ba zai shinshina ba, kuma in ace Bello gaban fadawa yay hakan abu ne me kamar wuya idan ba'a fille masa kai ba, dan tsananin shock na irin maganganun da ya dinƙa yaɓa mata matsayinta na ƴar Sarki tsayawa tayi kamar statue, and a zaton Turaki ko ace shi ɗaya ya rage namiji a duniya Gimbiya Aisha ba zata ɗauke shi ba saboda abinda Bello yayi mata, amma shine yau take daɗa kiransa?.

dama bata tsammaci zai amsa mata ba, saboda haka maganarta kawai taci gaba da yi.
"ƙawata Ilham bata faɗa min zancen aurenku ba kwata-kwata, amma na gani a duniya, naga the best couples in the year of 2022, na jima banga perfect match couples irinku ba.
duk da kai babu farin ciki a tare da fuskanka but hakan ba shi ya hana fiddo da ainihin kyawun surar da ubangiji yay maka ba, and wannan rashin bayyanar annuri da fara'a na fuskanka ya shaida min cewa auren dole ne akayi maka, kai baka so but ita tana so dan tata fuskar ta bayyana hakan 100%, but duk da haka fa duniya zata judging rashin walwalanka da a haka kake, amma to me da na riga na san fuskan da bai rabo da murmushi na san sam auren ba so yake ba. Anyway i congratulate you dear, Allah ya baku zaman lafiya. sai dai you have to know one thing, ni Aisha Sanusi M2 ni ce zan zama uwar ƴaƴanka, keep this in your mind".

Turaki dai tun sanda ta fara maganar ya kunna TV yana sauraron karatun alƙur'anin da aka saka a channel ɗin saudi tv, abubuwan da ta faɗa ma ba komai yaji ba banda na ƙarshen.
bai bari ta ƙara cewa komai ba ya datse kiran da ya haddasa masa ciwon kai. ya wurgar da wayar a gefensa yana daɗa jin ransa duk babu daɗi.

yana gama bin azkar ɗin da yake sauraro ya jinginar da kansa da kujera, lokacin tuni gari ya waye har 6:30 ta kusa.
idonsa a lumshe hoton Fillo nata haska masa, lokacin ne Gimbiya Ilham ta fito daga bedroom tana takowa da ƙyar har ta ƙaraso wajensa, abaya ne yello colour jikinta me bala'in kyau, ta ɗora hular chantly akan kwantacciyar sumar kanta, tayi kyau sose da light makeup ɗin da tayi sai zuba ƙamshi take yi, ta ɗauke hannunsa akan kujerar sannan ta zauna a kusa da shi ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, hannun nasa kuma ta ɗora akan cinyarta.

muryarta a sanyaye kuma a shagwaɓe tace,"Hammah fever na son kamani, kaina yana ciwo sosai, jikina ma duk ciwo yake yi".
ta ƙarasa maganar yana jin saukar hawayen nata a kafaɗarsa, yana jin yanda ɗumin hawayen ya tsarga fatar jikinsa, yana kwatanto shi da zafin hawayen Fillo, wacce ya san a duk inda ta ke yanzu kuka take yi.

bai ce da Gimbiya Ilham komai ba har wucewar daƙiƙa ɗaya, lokacin wayar dake kusa da shi tayi ringing, yana kallon new number ne ajiki yaƙi ɗauka.
har sau biyu kiran na katsewa tunaninsa duk Gimbiya Aisha ce, sai kira na uku ya shigo da lambar Inna Falmata, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga yana yin sallama.
daga can ɓangaren Boɗejo ta amsa sallamar tasa tana ɗorawa da faɗin,"ban kiraka da lambata ba saboda nasan ba ɗagawa zaka yi ba, ashe sabuwar lambar ma baka ɗagawa, sai ka ɗaga ta Falmata da yake kasan ta ƙanwar ubanka ce, ko ba komai halin girmama manyanka na burgeni, duk uban miskilancinka ka san manyanka".

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now