*LULLUƁIN BIRI*
*29*
motar Turaki bata tsaya a ko'ina ba sai a compound na cikin company nasu, ƙarfe biyar na yamma a lokacin, and at that time an ma yi closing, bai san exact abin da ya shigo da shi ba, kawai ɓacin ransa ya kaisa.yay parking yana daɗa tabbatar da duka glasses na motar a rufe suke, ya kunna karatun qur'ani sannan ya buɗe lock. ya kalli Fillo da har lokacin kanta ke kife a gefen kafaɗarsa, tun san da ta ke roƙon yay driving nasu a hankali taga baida hankalin dainawa shikenan sai tayi shiru, kuma tsoron da takeji shi ya hanata ɗagowa a kafaɗar tasa.
wucewar 20seconds yana kallonta, yana jin yanda numfashinta ke sauka a hankali, a tunaninsa duk bacci ne take yi, nan kuwa tsabagen zuciya ce tasa tai luff kamar wadda baccinta yay mugun nisa, wani irin zafi take ji a zuciyarta kamar ana rura wuta, in ace ta ɗago a ɗazu da tabbas babu abin da zai hana hannuwanta shaƙe Turaki, in yaso suyi accident ɗin da gasken gasken.
kafaɗarsa ya janye nan take kanta ya ƙwalu da kujeran, ta buɗe ido a hankali tana kallon inda suke, bata ko motsa ba har ya fice daga motar, tana kallo ya saka lock ya wuce ya barta, ita kuma ta rakasa da ido.
tana ganin yacca ƴan tsirarrun staffs da basu wuce ba kowa na gaida shi, shi kuma yana ɗaga musu hannu.duk ƙoƙarin da tayi don ganin lock ɗin motar ya fita ta kasa, kenan rufeta yayi a motar ya tafi ya barta?, koma me zai faru da ita ya faru da ita?, to me yake nufi da ɗaukota ɗin?, ga shi ya kashe Ac balle ta samu sauƙin zafin gari da na zuciyarta da take ji.
wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya, sai ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka, kuka take sosai har tana jin kamar zata shiɗe, ga kanta na uban sara mata, ga zufa duk ta wanke mata jiki, sai da tayi me isarta tukunna ta ɗago tana goge hawayen, tana jan majinar hancinta ta ƙara trying buɗe motar amma taƙi buɗuwa.sai kawai ta jinginar da kanta jikin kujerar ƙirjinta sai bugawa yake, ta cikin glass ɗin ta fahimci magriba ta gabato saboda yanayin yacca garin ya lulluɓe, zuwa lokacin duk staffs sun ɗaɗe sai me gadi kawai da take iya hangowa ta cikin mirror. ta rufe idonta tana bin suratul Yusuf dake tashi cikin ƙira'ar Yousuf Kalo.
Turaki kuwa tunda ya shiga office ɗinsa zama yay kawai ya rufe idonsa, yayi hakan ne kawai saboda temper ɗinsa yay cool, dan in yaci gaba da kasancewa tare da ita a yanda yake mugun jin haushin abin da tayi ba abin da zai hana sa illata ta. sai da ya ɗauki tsawon awa guda bai motsa a yanda yake ba, yana kallon kira daga different numbers na shigowa wayarsa amma babu ɗaya da yay picking.Fillo dai har sannan tana zaune sai wurga idanu kawai take yi, Allah ɗaya yasan yanda take ji a cikin ranta, taja Allah ya isa tafi kai ashirin, in ace da wani abu da zata iya fasa glass ɗin tuni ta fasa ta fita ta windown.
tana cikin tunani a ranta sai taga Turaki ya fito daga wani building daban da inda ya shiga ɗazu, cikin sauri yake tafiya yana sauke hannun rigarsa da ye tattare, da alamu alwala yay zai wuce masallaci tunda ga ruwa nan a fusakarsa.bata ɗauke idonta akansa ba har sai da ta daina ganinsa, bayan minti goma sai taji lock ɗin motar ya fita, kuma kamin ta kai ga buɗe murfin idonta taji ƙofar side ɗin da take ta buɗe.
"out". taji muryarsa ta shiga kunnenta san da take buɗe idonta duka.kamar tayi banza da shi sai kuma taji tana tsoron yin hakan, Allah shahidi bata tsoron uban kowa a duniyar nan amma tana mugun shakkar Turaki.
ta tattaro mayafinta tana ƙudundune jikinta sannan ta fito a cikin motar ta tsaya a gefensa, tana fitowa ya rufe yay gaba yana cewa da ita,"follow me".tabi bayansa tana ɗan kalle-kalle, sai yaba kyan company ɗin take yi, daga waje ma kenan ina kuma ga an shiga ciki.
suka shiga cikin office ɗinsa sannan suka wuce cikin wani ƙaton parlo, inda anan ne yake Turaki ke hutawa."kiyi sallah". abinda yace mata kenan ya wuceta ya zauna kan ƙaton farar cushion.
Fullo ta kalla haɗuwar parlon ta ƙara kallo tana me jinjina uban yawan dukiyar da aka kashe wajen ginin company ɗin da kuma abinda aka zuba acikin office ɗin, wato kuɗi dai suna inda suke, talaka da baida su ne yake ganin kamar babu su kwata-kwata.