*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_not edited._
*26*
Ilham ta shigo parlon Yarima Abbas bakinta ɗauke da sallama da wani irin emotions a tare da ita. tun shigowarta kanta ke sunkuye a ƙasa kamar ta shiga fadar Me Martaba.
ta ƙarasa gaban table ɗin dake tsakiyar su Yarima Abbas ta ajiye ƙaramin tray dake hannunta, bayan ta ajiye ta ɗago ido ta kalli ɓangaren da tasan anan ne zata yi tozali da Turaki, tunda from there hancinta ke jiyo mata ƙamshinsa, wannan ƙamshin turaren da ita ta basa kyautarsa har ya zama choice ɗinsa.idonsa da nata suka haɗu wuri ɗaya, kuma ba tare da ƙwayar idonsu ta fita ata junansu ba suka saki wani sanyayyan murmushi wa juna. wanda hakan ya wanzar da jin kunya a tare da ita, Turaki kuma da har sannan murmushin bai ɗauke masa ba yace,"zo nan".
Yarima Abbas dake cike da jin girma na izza yace,"kafi kowa sanin bana son yara suke zuwar min sashina ko, amma duk sanda kazo sai ka dinƙa wani kiransu suna shigo min da dattin ƙafafu".
ba tare da Turaki ya dube shi ba yace,"da wa kake?". rai ɓace Yarima Abbas yace,"yaushe wannan rainin hankalin zai bar jininka Turaki?".
Turaki ya ɗauke idonsa akansa yay masa banza bai tanka masa ba.Ilham ta zauna akan hannun kujerar da Turaki yake, ya kamo hannunta ya riƙe yana cewa,"wai ni wannan Kunyar tawa da kike yi tun sanda kika dawo ta mene?". kanta na ƙasa tace,"kunya kuma Hammah?". yace,"ehh mana, kuma ni ban haihu ba, balle nace ɗana kike kamu".
ta ke fuskanta yay turning zuwa na shagwaɓaɓɓu tana ɗan dukan ƙafa a ƙasa tace,"yanzu Hammah ka rasa da wa zaka haɗani sai ɗanka".murmushi kawai yayi yana shafa beard ɗinsa. idonsa akan tray ɗin da ta aje yace,"mene wannan?". tace,"your favorite, since morning na dafa idan zan tafi na kai maka...". sai ya katseta da cewan,"have you forgotten?". sai ta ɗan ɓata fuska tace,"ban manta ba, but ai naga ada ne". ya gyara zamansa yana faɗin,"ba da bane har yanzu Ilham. girkin Maama da Zaytun kawai".
wani irin rashin jin daɗin ya ziyarci Ilham, fuskarta ta nuna hakan, Turaki ya kalleta yace,"fushi?". ta girgiza kanta da sauri,"a'a". yace,"to saki fuskan". ba tare da tayi hakan ba tace,"to har girkin matarka ma ba zaka ke ci ba Hammah?". yace,"dalilin da yasa zanyi aure na zauna a kusa da Maama kenan". tace,"amma Hammah akwai...". ya tari numfashinta da faɗin,"akwai mutuwa ko?, na san da hakan. ki tayani adu'ar na riga Maama mutuwa ba naga tata ba". Ilham tace,"to Allah ya ƙara mata lafiya ya kuma bata tsawancin kwana me albarka". ya amsa da,"amin lelen Boɗejo". ya sauke numfashi sannan yace,"ina gyalenki?".
tace,"na barosa kan bed ɗin Mami saboda kace na hanzarta".
hannunsa akan fuskarta yace,"je ki ɗauko ki dawo, ki faɗawa Mami zaki min rakiya".fuskarta ta washe da murmushi tana tambayarsa,"ina zamu je?". ya shafo wuyansa sannan ya bata amsa,"perfume zamu sayo".
idonta ya ƙanƙance a sa'ilin da take kallonsa. "ƙarewa yayi?, in ɗauko maka nawa?".
yace,"a'a wani zan sauya". idonta na ƙara ƙanƙancewa tace,"canjawa kuma?, perfume naka ɗin? your best choice ɗin?".
ya ɗaga gira ɗaya,"yes, bana son ƙamshinsa yanzu". tayi knodding kanta sannan ta miƙe ta fita.Yarima Abbas ya rakata da harara, yayinda Turaki ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta har sanda ta fice, bai san dalilin da yasa yake tausayin yarinyar ba, ko dan ta kasance ita ɗaya a wurin mahaifiyarta ne?, ba hakan bane, hakan kuma ba zai zama dalili ba. yana son Ilham kamar yanda yake son Nihal, Samha da kuma Zaytun. yana ƙara sonta da burin faranta mata saboda yanda itama take sonsa tun yarintarta, ta ke masa kallon jininta fiye da yanda take kallon su Yarima Abbas.
ya sauke numfashi yana jinginar da kansa jikin kujera tare da rufe idanuwansa, baya manta alkhairi a rayuwarsa ko da ace daga baya zaka saka masa da sharri, wannan alkhairin naka garesa zai mantar da shi girman sharrin da kayi masa. sai dai har yanzu ya kasa mantawa da sharrin da Mami tayi masa, tsawon shekaru da yawa har yau neman dalili yake na ƙala masa sharrin sata da Fulani Azima tayi.