*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_Ina yi mana barka da sallah tare da fatan alkhairi a rayuwarmu🥰, mugun ji mugun gani Allah ka tsaremu da shi Amin Y Allah🤲...wayidi a miƙo, a miƙo naman sallah kar nai zuciya na hau bari a shop ɗin *BEST SHAWARMA & MORE*😫, idan kuwa na dira a shop ɗinn abin ba zai kyau ba dan ban fitowa sai asusun Yaya Nusaiba ya gane kurensa😂._
*19*
Yusuf na zuwa gida ko horn bai yi ba balle ya tsaya jiran wani abu shi buɗe gate, ya fito daga motar cikin sassarfa. yasan yana da patient, matarsa dake ɗauke da juna biyu mai wuyar laulayi, yau lafiya gobe babu lafiya, shi yasa duk hankalinsa ya tashi tunda yaji irin salatin da Inna Wuro ta zabga, duk wanda yaji wannan salatin ya san ba lafiya ba kamar yanda ta faɗa.jinsa yake kamar ya ɗauki kansa ya dire a parlon Inna Wuro, ƙaramar ƙofar gate ɗin a buɗe take dan haka yana zuwa turawa yayi ya shiga. mai gadi dake daga cikin ɗakinsa a zaune yay masa sannu da zuwa, a sama ya amsa masa ya wuce kamar zai tashi sama gabansa sai faɗuwa yake.
hango Ammi yay zata shiga motarta, ya bita da kallo for some seconds, atleast dai zuciyarsa ta sami natsuwa ko ya ya ne, dan shi abunda yake hasashen ya faru daban ne, to kuma tunda yaga Ammi taci kwalliya kuma bai ga wani alamun tashin hankali tare da ita ba sai ya fara nutsuwa.
but still dai gabansa bai daina faɗuwa ba, ba zai yi la'akari da yanayin Ammi ba akan ba wata matsala bace babba, komai ma zai iya faruwa ba tare data sa ni ba, idan ma ta sani zata iya yin banza taci gaba da sha'aninta, ranar nan ma haka tayi da akazo aka ce mata Nuratu ta faɗi, baki kawai ta taɓe ciki-ciki tace Allah bada lafiya, Ko da aka kwantar da Nuratun bata je asibitin ta dubata ba, zallar ƙi take nunawa aurensa da Nuratu babu ɓoye-ɓoye ga kowa.
yana wannan saurin tafiyar ne dan ƙarasawa side ɗin Inna Wuro sai yaji wayarsa na ringing, yasa hannu a aljihu ya ɗauko. yana ganin sunan Ammi ƙirjinsa yay wani irin bugawa, da ƙyar ya iya ɗaga kiran a lokacin da yake dab da katsewa.
kasa cewa komai yayi daya ɗaga wayar but still bai daina tafiyar ba, sai dai ya rage saurin tafiyar tasa, jin bakinsa yake kamar ba zai iya cewa komai ba.
Ammi tace masa,"shawaran da zuciyar taka ta yanke maka kenan Yusuf?". mamaki ya kama Yusuf, taya akai ta gansa?, a hankali ya juyar da kansa gefe yana kallon inda take sai yaga bata wajen, ba abin yace mata ba shi bane tunda dai ta riga ta gansa ɗin.
ya buɗe baki zai yi magana ta tari numfashinsa,"yau da safe baka shigo inda nake ka duba ni ba sannan ka dawo kana ganina amma kasa kai ka wuce saboda banda mutunci yanzu a idonka. idan Falmata ce ka isa kai mata haka?, ko sallah kaga tana yi a compound ɗin nan ai sai ka jira ta idar tasa maka albarka tukunna zaka wuce. to ni dai Allah ya isa rabani da akai da kai wallahi, ba'a san irin baƙar wuyar dana sha kafin haihuwarka da lokacin haihuwarka ba, ba yafewa zanyi ba. kuma kaje duk wanda zai saka maka albarka wallahi bata kai tawa ba, a banza a wofi, kai da ka san darajar uwa ma da baka fifita kishiyata akaina ba, shashashan banza marar hankali kawai, idan baka sani ba ka sani uwa tafi gaban wasa".
muryar Yusuf a hankali kuma da ladabi yace,"kiyi haƙuri Ammi amma ba yanda kike tunani ba ne, yau da safe ko gidan nan banzo ba Allah".
taja tsaki tace,"aikin banza. to ka juyo ka kaini unguwa in ka dawo kaje duk inda zaka je".yasa hannu ya shafa kansa tare da rufe idonsa bai ce komai ba kuma bai motsa daga inda yake ba. Ammi ta ƙara cewa,"baka ji me nace ba ne?".
yace,"naji Ammi". tace,"ba zaka kainin ba ne?, ko kuma izinin uwar taka zaka fara zuwa ka nema?".ya ƙara sosa kansa yace,"ai Umman bata dawo ba Ammi".
da a kusa da ita yay maganar da babu abinda zai hanata buge masa baki, cikin zafin rai tace,"zan zauna zaman jiranka ne ko ya?".