*LULLUƁIN BIRI*
*50*
sai ƙarfe goma sha ɗaya Turaki ya farka da ga baccin bayan asuba da ya kwanta, lokacin da ya tashi bai ga Fullo a ɗakin ba, bai yi mamaki ba ya san da ma tsoro ya kawota, ba don haka ba ya san ba zata taɓa zuwa ba.
yana kunna wayarsa ya ci karo da messege ɗin Sectery nasa, da yake tuna masa appointment din da yake da shi da wani company na lemu by 3pm.saukowa yayi akan gadon ya shiga toilet yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin shigar manyan kaya na kufta black colour da tayi masa masifar kyau. yana cikin fesa turare yaji cikinsa yayi ƙugi sosai alamar yunwa, dan daren jiya ma bai ci komai ba, yay gajeran tsaki na ƙorafi da takaici, ga shi da aure amma bai da matar da zata dafa masa abincin da zai ci, shin wai sai yaushe zai san yayi aure ne?, when zai fara jin wannan daɗin da ake cewa akwai shi a gidan aure?, wannan farin cikin sai yaushe?, ga shi ta bakin Bello da gaske rainon Fillo zai yi, rainon da baya jin cewar zai iya, ya ƙara yin tsaki yana dire perfume da ke hannunsa, yanzu ba abin yaje gida ba da sunan zai ci abinci a fara yi masa tambayar ƙwaƙwaf.
jakar laptop ɗinsa ya ɗauka ya fita a room ɗin, daidai bakin ƙofar room ɗin Fillo ya tsaya, ƙofar a buɗe take, ya tsaya yana tunanin ya shiga ko kar ya shiga, a ƙarshe zuciyarsa ta yanke masa yay tafiyarsa kawai, tun da har ta iya barin ɗakin nasa taji sauƙi kenan.
yana saukowa parlo ƴan aiki suka fito da sauri daga kitchen, suka durƙusa suka gaida shi, hannu ya ɗaga musu ba tare da ya amsa da fatar baki ba, har ya kai bakin ƙofa idonsa ya sauka akan dining, flask ne guda biyu a ajiye sai na tea flask, ya kalli Sakina da ba ta koma kitchen ɗin ba ya ce,"ta sakko ne?".kanta a ƙasa ta ce,"a'a ranka ya daɗe bata sakko ba kwatakwata".
yay ɗan jimm sai kuma ya ce,"ita tace kuke yin girki?".
ta ce,"a'a ranka ya daɗe, mun ga dai hakan na cikin aikin mu ne".
ƙaramin tsaki kawai yayi ya zuge glass ya fi ce, Sakina ta bi shi da kallo tana riƙe haɓa da jinjina kai.
Hannatu na ganinta ta ce,"lafiya?, me kika guntso?".
"uhmm ke wannan me gidan bai da sauƙi ko kaɗan, babu ma alamar mutunci a tare da shi, ni da ma tun ranar farko naji bai yi min ba sam, gaskiya matarsa na haƙuri da shi, irin mazan nan masu shegen girman kai da izza, fuska gaba ɗaya babu annuri".
Hannatu ta ce,"wani abu kika gani hala".
tayi maganar da irin suffa ta ƙwanƙwararrun munafukai.
"ke kin ji yacca yake tambayar wa ya saka mu yin girki, kamar fa zai kawo min duka, babu wani irin taushi girmamawa ta ɗan adam acikin muryarsa".
sai kuma ta taɓe baki,"ni da ma na faɗa miki tun ranar da muka zo na san ba zaman lafiya ake a gidan nan ba, ba ki ga ita kanta kamar ba ta da miji ba, sai dai ta sauko tayi kallo taci abinci ita ɗaya ta koma, tabɗijam ni kuwa dai duk kuɗin namiji wallahi ba zan yarda da rashin mutuncinsa ba, ke ni ba zan ma yarda da wani auren dole ba, ba zan iya namiji ya takani ba gaskiya".
"ke ma dai Sakina ai da ma da gani ba auren soyayya akai ba, ni itace ma ta ke bani tausayi tun da naji ance tayi aiki a gidansu, wataƙila ƙarfi aka nuna musu aka aura ma ta shi dan anga ba su da hali, ni tausayi ma take bani kina kallonta kin san bata jin daɗin zaman, ko da yake babu komai zamu ɗaurata a hanya, naga ba ta da girman kai za ta sake da mu, zamu ba ta shawarwarin da zata saita mishi zama".
Sakina ta nufi cooker gas tana faɗin,"ke yanzu dai buɗe firinjin nan ki ɗauko mana kazar nan da naji ta ɗan fara yami, mu gyara muci abarmu in ba haka ba a banza za'a barta ta lalace, naga matar gidan ba wani wayewa tayi da cin kayan daɗi ba, duk gata nan a ƙanjame ai. Allah na tuba ni ina da wannan uban kayan daɗin ma me zai sa in damu da takaicin ɗa namiji, ai ɗaukarka zanyi in bawa banza ajiyarka, kai ita ma dai wallahi anyi lusara, ko da yake wasu sun ɗaukaki soyayyar namiji fiye da jin daɗi, kuma kin san Allah duk yanda akayi ganinta ƙashi da rai yasa yake ma ta wulaƙanci, babu gaba babu baya kyace me cutar S, kai Allah dai mun gode maka, kuma banza da ita ma kawai ta jefa shi a kwandon shawara ta bawa jikinta ingantattun kayan da zasu farfaɗo da ita, ba dai gidan jin daɗi da hutu ta zo ba, wallah wata guda yay ma ta yawa ta murmure".