49

106 8 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*49*
washegari da la'asar Turaki na zaune a falonsa Bello ya shigo, kallo ɗaya Turaki ya yi masa ya mayar kan computer ɗin da yake dannawa, Bello ya ƙaraso gabansa ya ɗaga robar faro ɗin da yake hannunsa ya tuttule masa ruwan ciki akansa.

"Bello what kind of rubbish be this?".

"ɗan iska ma nan ya ganka ya ƙyale MT, yanzu na ƙara sarawa girman rainin hankalinka, kuma ban yafe ba zagin da ka ja min, akan kujera nake amma sai da na miƙe babu shiri tsabagen shigar zagin nan, har yau a jijjige nake da shi, sai kace kayi abu ni da banyi ba ni ke kwana aciki".
Bello ya faɗa yana zama kan kujera, Turaki ya dinƙa kallonsa da wani kallo kafin yay tsaki ya miƙe ya cire rigar jikinsa da ta jiƙe.

"tukunna ma ni ban gane maka ba har yanzu, ni ka rainawa hankali ko kuma su Mum ɗin ka mayar marainan wayonka?, sarai dai da iliminka ka san yarinyar nan ba ta da iddah akanka amma ka barta tana zama acikin gidanka".

Turaki bai tanka masa ba ya ci gaba da aikinsa, sai can Bello ya fara masa ƴar murya,"haba Aminina kar muyi haka da kai mana, faɗa min gaskiya don Allah. gudun ɓacin ran su Maama yasa ka ƙaryata sakin da kace min kayi ko kuma ni ɗin dai ka mayar sauna?".

"munafiki kawai". Turaki ya ce da shi yana hararsa.

Bello yay dariya sosai ya ce,"naji ka kirani da koma menene, ka san Allah idan baka faɗa min gaskiya ba to zanje na faɗawa su Maama gaskiyar abin da na sa ni, dan ni dai kace min ka saketa".
ya faɗa yana miƙewa.

da sauri Turaki ya ce da shi,"kai wai mara hankalin ina ne, yanzu sai kaje ka faɗa musu hakan?".

Bello ya ɗaga kafaɗa,"ofcourse, zan zuba maka ido ka ci gaba da zaman haramun da yarinya saboda kana gudun ɓacin ran iyaye, ai gwara a faɗa musu kawai su san gaskiyar abin da ke faruwa, yarinya ta tafi gidansu ta sami wani mijin tayi aurenta, kai kuma ai maka duk hukuncin da ya dace da kai. ko nufinka ka mayar da ita ne baka faɗa min ba?".

Turaki na daɗa ɓata rai ya ce,"ni dama ban saketa ba, ko da nace maka na saketa to wallahi tallahi ban saketa ba".

dariya ta zo wa Bello ya ce,"yau har da su rantse min?".

"saboda ka ƙyale ni na huta, kamar yanda ka barni na huta da takurarka na 7days".

Bello ya jijjiga kai,"amma kai dai anyi mugun ɗan rainin hankali, da ma saboda na ƙyaleka na 2days yasa kace min haka saboda ka san zanyi fushi?".

Turaki yay masa banza, sai kuma Bello ya ƙara cewa,"to kuma na ga har yanzu baka bar nan part ɗin ba?, ko kewar ta nan ɗin kake yi tunda ita ka ɗanɗana ka ji?, ko kuma ita ma baka saketa ba hankalin mutane ka raina?".

Turaki ya dire abin da yake ya dafe kansa, wucewar wasu sakanni tukunna ya buɗe ido ya zuba akan Bello ya ce,"in kana ƙaunar Allah da Annabi ka ƙyale ni, saboda fa wannan shegen sa idon naka yasa na barka a yanda itama waccan yarinyar ta ɗauka".

Bello ya gimtse dariyarsa ya ce,"tun da kace Allah da Annabi an wuce wurin. mu koma kan aiki, ɗa zu mun yi waya da financial sectary na IBTC company, ina wancan document ɗin da ka haɗa?,".

"shi na ke haɗawa yanzu?".

"what! ba jiya ka ce ka yi completing nasa ba?, yau fa ya kamata ace mun yi printing an kaiwa Baffa".

"to ya zan yi, after na gama wayar ta lalace, kano ma na kai gyaran a jiya, na so na tsaya na taho da ita Khalil ya damen da kira akan in taho gida ya ga kamar ba lafiya, but mun yi da shi me gyaran za'a kawo yau, ni kuma ganin ba su kawo tun safe ba naga gwara in haɗa wani kawai".

"wai wayar da ka siya last week ne ta lalace ko wanne?".

"ita ce".
"kaii! da ma ba original ba ce cutarmu suka yi, but tawa fa normal take, me ya sami taka ɗin da ma?"

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now