3

147 18 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya

*3*
*Dare, 20:45pm.*

Ƙafafun Hajiya Madina suka shigo cikin ƙaton parlon, wanda ƙamshinsa ya haɗe da sanyin acn da ke hurawa ya haɗu ya bada wani sanyin ƙamshi me motsa zuciya.
Jikinta sanye da ash abaya wadda taji adon stones ajiki, ƙyallin stones ɗin sai wurgawa suke ta cikin hasken fitilun parlon. Ganin Ƴaƴanta ya saka ta sakin murmushin da bata shirya masa ba, tana ƙaunar yaran fiye da yanda take son kanta, kowa yasan da hakan, abu ne ma da kamar tayi tambarinsa a goshinta.

Tana tsaye daga bayansu tana ƙare musu kallo cike da so da ƙauna, su kuma hankalinsu ya tattara kan tab ɗin da ke kan cinyar Sameer su na kallon pixx ɗin da su kai ɗazu na birthday ɗin Turaki. Gyaran muryar da tayi ne ya ankarar da su zuwanta, suka ɗago a tare su na kallonta fuskokinsu na washewa da murmushi.

Ta zauna a kujerar da ke fuskantarsu tana faɗin,"shi ne aka kasa jira nazo, wannan cin amanar har ina?". Tayi maganar da sigar wasa kamar wadda ke tare da ƙawayenta.

Samha ta ɗauko tab ɗin ta nufo wurinta tana faɗin,"Maama kinga wanda aka maku ke da Hammah duk yafi kyau wallahi".
ta zauna kusa da ita tana nuna mata hoton da aka ɗauka a sanda Turaki ke saka mata cake a baki.

Allah ɗaya yasan me taji cikin zuciyarta a wannan lokacin, dan shi kansa murmushin da ya suɓuce a leɓenta bata san da zuwansa ba. Ta kai hannu ta shafa hoton, ƙwayar idanuwanta na haskawa da ƙyallin wata ƙauna da ke tsakanin Uwa da Ɗa wanda Ubangiji kaɗai ya san girmanta.

"gaskiya munyi kyau, kamar ban haifi Hammah ba, kalle ni wata ƴar suwet a kusa da shi. Wannan idan sirikata ta gani ai sai tayi jealous idan bata san wacece ni ba".
Ta faɗi hakan cike da raha, haƙoran makkan da ke bakinta guda biyu su na bayyana duka a waje.

Taci gaba da scrolling har tazo kan wanda su kai gaba ɗayansu,"kai amma wannan ma yay kyau. 1 Family na Baffa kenan". San da tazo kan wanda Turaki yake shi kaɗai ta ƙara cewa,"wannan kam shima enlargement ɗinsa zan bada a ƙara min, Hammah yayi kyau sosai kamar wani magidanci".

Sameer yace,"Maama wai duk sai kin cika bangon ɗakinki da parlonki da hoton Hammah ne?".

"ƙila hakan ce zata kasance, dan sai dai idan bai yi sabon hoto shi ɗaya ba".
Sai da suka zo ƙarshe a kallon hotunan sannan ta ƙara cewa,"gaskiya Hammah ya dawo ya fito min da matar aure, dan na ƙagu naga sirikata".

nan dukansu suka haɗa baki wurin faɗin,"aiko dai Maama ya kamata ace Hammah yayi aure, sai tsofewa yake yi".
Kallon da tayi musu ne yasa babu shiri suka gimtse bakinsu, saboda kalmar tsufa da suka jinginata da Turaki.

"Hajjah nyamdu mae henyi". (Hajiya abinci ya kammala). Mai aikin da ta ƙaraso wurin a yanzu ta faɗa sanda take tsugunawa a gefen hannun kujerar da Hajiya Madina ke zaune.

Ba tare da ta juyo ta dubeta tace,"usema be habdugo". (sunnu da ƙoƙari)

"aha Hajiya Miyetti". (yauwa Hajiya na gode)
Daga haka ta miƙe ta bar wajen cikin azama dan barin musu wajen. Hajiya Madina ta ɗauke tab ɗin daga kan cinyarta tana ajeta kusa da ita, sannan ta kalla ƴaƴan nata tace da su,"my bloved ones dinner is ready".

Tare suka miƙa kaf ɗinsu suka nufa dining area, warm coolers na abinci ne zafafa masu kuɗin gaske, an jere akan dining table ɗin wajen kala shidda, kowanne cooler da kalan abinci da ke ɗauke acikinta, ta yanda kowa idan zai ci abincin zai ci favorite nasa ne.

Zaytuna ta buɗe flask ɗin da ke ɗauke da Mandi rice ta zuba a plate ta miƙa shi gaban Hajiya Madina, sannan kowa ya shiga zuba nasa abincin. Tunda suka fara ci babu wanda yay magana sai ƙarar cokula da kake ji har su ka kammala, wanda Hajiya Madina ce ta fara gamawa, ta yagi tissue ta goge bakinta.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now