*LULLUƁIN BIRI*
*58*
dawowar Fillo gida ta tarar ana ta kai komo wajen shiga da kayayyaki ɓangaren Ilham, tun jiya ake wannan zaryar, ƴan'uwan mahaifiyarta ne kusan duk ɗin su, sai Boɗejo da Inna Falmata.
sai dai bata san ba ko yau har da su tunda dai bikin ba ɗaya ba ne, duk da dai taga Boɗejo na nuna kamar bata da hurumi da auren su Zaytuna da Khaleel da Samha, kamar su ma ba jikokinta ba ne.ɗauke kai tayi daga barin kallon part ɗin Ilham ɗin, tayi wucewarta part ɗinta bayan ta tambayi Baba me gadi ko an kawo masa abinci, da shigarta kuma ta rufe su Sakina da faɗa akan rashin kaiwa Baba abinci da suke yi da wuri.
ta kalli Maijidda da ke zaune a parlon ta haɗe rai, ta ce da ita,"yi haƙuri don Allah, sammako nayi gidan Yaya Yusuf, za su je taraba ne na bayar da saƙo akaiwa Ummi".
Maijidda tace,"ba dai bikin Raudha ba".
"shi ne ya taho wallah, next week in Allah ya kaimu".
"kin ga da an kammala na su Adda Zaytun sai ki bi su ku tafi tare kawai".
Fillo tayi murmushi me ciwo ta ce,"ni ma haka nace. ki hau sama ki jira ni bari na ajiye waɗannan kayan".
ta faɗa tana wucewa kitchen, friedge ta buɗe ta zuba fruites ɗin da ta siyo, kusan kwana uku da ƙarewar na su amma Turaki bai kawo wani ba.
fitowarta daga kitchen ɗin ta tarar da baƙi a parlon, fuskar farko da ta kalla ta shaida ƴan'uwan Ilham ne, don su na kama sosai da Fulani Azima.
ta ƙarasa wajen su ta durƙusa har ƙasa, cikin ladabi ta shiga gaishe su, kuma ba tare da ta miƙe ta koma kan kujerar ba tayi zamanta akan carpet ɗin don bata tunanin zata iya zama kan kujera alhalin su na kai, hakan kamar da rashin ɗa'a.su uku ne manyan matan, kowacce sai da ta gama yi mata kallo a yatsine sannan suka haɗa baki wajen amsa gaisuwartata.
Antyn Kano ta dubi Fillo da kyau kafin ta mayar da dubanta ga Mama Asabe ta ce,"wannan ce kishiyar Ilham ɗin?".Mama Asabe tace,"ina jin ita ce ko?".
sai kuma kusan a tare suka jefawa Fillo tambayar,"kece matar nan ɓangaren ko kuma ƴar aiki ce?".kafin Fillo tayi magana Hajiya Zaliha ta amshe da cewa,"ita ce mana".
"yanzu wannan ita ce wacce aka liƙawa Turakin da ma?, ai ce nake yi waccan da aka ce an ba shi a bushe take ko".
Mama Asabe tayi maganar.Hajiya Zaliha ta taɓe baki ta ce,"yo ai dama saboda su taimakawa ƴar'su ta zama mutum kuma su ci arziƙi, shiyasa suka bi ta ƙarƙashin ƙasa suka kori Ilham aka liƙa masa ita, amma banda haka Turaki ai yafi ƙarfin tsummar ƴar aiki, ko da yake banga laifin iyayenta ba dan sun yi ƙoƙarin haɗa iri da mai dukiya kamar Turaki ba. hausawa suka ce bangon sukari a jingina da kai a lasa, yanzu ba gashi sun mayar da ƴar'su ta zama mutum ba, dama ai ƙwaɗayin dukiyar tasa ake ba wai saboda Allah suka nuna su na sonsa ba, yo ke daga jin labarin ɗauke asiri ai kin san ƙarya ne ma".
Mama Asabe ta ce,"to ai ni a wata ruwayar ma ji nayi ance bata da asali, ance uwar na haifarta ta jefar da ita ta gudu, an ce ma bata san uban nata ba sai da zai mutu yazo neman gafarar uwar. to duk dai kin san harkar ta a haɗu a rufawa kai asiri ne shiyasa aka ɓoye gaskiyar zancen, amma dai tabbas an ce shegiya ce".
Antyn Kano ta gyara zama tana duban Fillo, ta kama haɓa ta riƙe cikin izgili ta ce,"shegiya kuma?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ashe abun har haka yayi muni, yanzu tsakani da Allah ina gamin haɗi tsakanin tsarkakke da gurɓatacce, shege ai sai ɗan uwansa shege, gaskiya wallahi an zalunci yaron nan, ko da yake aikin asiri babu abin da ba yayi.
to ni su Mai Martaba ma mene na haɗa Ilham kishi da ƴar gaba da fatiha?. kai talaka dai akwai zubarwa da kai mutunci, da zarar an ce an rasa cin na yau da na gobe shikenan sai kiga an faɗa harkar karuwanci kuma. Allah dai ya kyauta yasa kar a haifi iri".