16

113 10 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

_avoid any mistake plss🙏._

*16*
*Shongom LGA, Gwandum, Yabayo village.*
rubutun da map location ɗin ya zana kenan ajikin wayar dake riƙe a hannun Khalil. with high speed yake drving motar kamar zai tashi sama. adu'a yake cikin ransa Allah ya kaisu lafiya, idan ba haka ba za'a iya samun gagarumar matsala a wannan tuƙin nasa, saboda kukan mahaifiyarsa dake gigita hankalinsa da tunaninsa, da kuma tunanin halin da ɗan'uwansa, Yayansa mafi soyuwa a gare shi yake ciki.

tunda suka taho kuka kawai takeyi, duk wata magana ta kwantar da hankali ya faɗeta amma taƙi tasiri a gareta, ya rasa me kuma zaiyi, yasan dai ba zata taɓa natsuwa ba har sai sun isa inda take da buri, to amma atleast yana so ta tsayar da wannan kukan nata ko dan ya samu yayi tuƙin nan lafiya.

ya ƙara kallonta a karo na babu adadi yana jin zuciyarsa na tsinkewa, ya cine fuska ya wani daki stearing da mugun ƙarfi, kamar ya fasa ihu haka yake ji. shi amsar ma da yake so ya sani wai me ma ya fitar Hammansu a wannan salasainin daren?, shin ba ya shiga bedroom ɗinsa yayi masa gud night ba, ya tarar kuma lokacin har ya fara bacci.

ya sauke numfashi yana barin kallonsa ga tuƙin da yake, a hankali yace da ita. "Maama dan zatin Allah kiyi shiru ki daina wannan kukan, wallahi yana ɗaga min hankali, stearing nan nema yake fa ya ƙwace a hannuna".

tasa gefen hinabinta ta goge hawayent tana so ta tsayar da kukan. ta ɗago ta kalle shi idanuwanta duk sunyi jawur sun yi girma. cikin sanyin murya kuma a raunane tace da shi,"to ka kira min Baffan naku".

ya rufe idonsa ya buɗe ya sauke agabansa, da zafin nama ya kaucewa bishiryar daya kusa duka. ya furta subhanalla sannan yace,"Maama na faɗa miki insha'Allahu babu wani abu da zai sami Hammah, shima nasan bige mutum ɗin da yay ne yasa ya rikice har yake faɗa miki bai san a inda yake ba...".

ta katse shi da cewar,"ni dai idan ba zaka kira min Baffan ba to ka faɗa min, sai na sauka na nemi masu waya su ara min".
yace,"to me za kice masa?".

ta ɗan kalle shi yana mata abu kamar ba ɗanta ba, sai tayi shiru bata ce masa komai ba. shima shirun yayi, can ta ƙara cewar,"yanzu dai ba zanci arziƙin wayar taka ba Khalill?".

buɗar bakinsa yace mata,"kina so ki rasa mijinki ne?". ta girgiza kai da sauri. "to ki haƙura da wannan kiran dan baida amfani, kin san dai Baffa ya fiki shiga tashin hankalin akan lamarin daya shafi ƴaƴansa, yanzu idan kika faɗa masa ya yanke jiki ya faɗi a inda yake fa?, kin san dai yanda ba kya kusa da shi ɗin nan anything can happen. so kiyi haƙuri har mu ƙarasa ai mun kusa zuwa, na kira mijin Inna Falmata yace ga police nan da ambulance zasu biyo mu a baya, dan Allah Maama kiyi haƙuri kita adu'a kawai kinji uwa ta gari".

ta gyaɗa masa kai kawai tukunna tace,"to amma baka sauri ka ƙara speed". yace,"to Hajiya Maama yanzu kam za kiga mun isa...ai wurin ba wata tafiya me nisa bane".

tana kallonsa tace,"Yabayo fa Khalil". yace,"can ɗin fa, yanzu za kiga munje Maamancy, situation ɗin da kike ciki ne fa yasa ki ganin nisa".
ta kuma gyaɗa kai bata ce komai ba, taci gaba da tasbihin da take yi.

a wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke ya kwantar da kansa jikin kujerar, abinda zai iya faruwa da shi dalilin accident ɗin nan ba shine damuwarsa ba, ran yarinyar kawai yake ji, baya so ta mutu, idan ta mutu bai san wanne hali iyayenta zasu shiga ba.

ya buɗe idanuwansa a hankali ya sauke su akan titin da duhun dare yasa ba'a iya hangen komai. yaji wani abu da bai san menene shi ba ya tsarga masa. ya juya baya yana kallon yarinyar, har yanzu zuciyarsa faɗa masa take da gawa yake tare, ta riga ta mutu, irin jinin da ta zubar ba zai barta ta rayu ba.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now